BABI NA TALATIN DA TARA

432 107 18
                                    

BABI NA TALATIN DA TARA
*ABIN DA KA SAMU YAU, NA WASU NE WANDA KAYI HAKURI KA SAMU GOBE SHINE RABON KA DOMIN KAIWA GOBEN SHINE ME WAHALA FATAN ALKHAIRI NAGODE SOSAI 🥰😍*

Kasa tayi da idanun ta, tana kallon hannunta idanun ta sai kara cika yake da ruwa, gyara zama Barkindo yayi yana kallon hannun ta, kafin ya rike tafin hannun yana hura mata iskar bakin shi.
Bayan tafiyar Mahaifiyar ta da rasuwar mahaifin ta yau ce ranar farko da wani ya tausassa mata ya kuma tsaya mata, a hankali take sauke ajiyar zuciya irin me hade da kukan nan irin wanda ba kasan lokacin da zai zo maka ba, Anum fara ce kal kamar uwarta, ga ta da Ubangiji wanda ya ke cunkushe, musamman da babu uwarta sai ya hargitse ya cunkushe kamar ba jikin mutum yake ba.
"Ci kin ji" ya fadi mata yana kallon yadda take kuka.
"Kina son wani abu ne?"
"Ummina" ta fada cikin bagwaren fulatancin da bai zauna a harshen ta ba.
"Kiyi hakuri bata nan amma zata dawo kin ji maza ci sai na mai dake" girgiza mishi kai tayi tana kallon kasa.
"Toh tashi na kai ki gida" wani masifaffen shasheka ta ja, tana kallon shi.
"Kina jin yunwa ko?" Ya fada bayan ta koma wurin dokin da ya kawo su, ya ciro abinci da ya tawo da shi nakiya ce da alkaki, da taji zuma ya mika mata. Duk da tana tsoron shi bai hanata kukan ta ba, sai ma kin amsar da tayi ta rikice mishi da kuka. Zama yayi ya sakata a gaba.
"Toh ya isa mana." Ya fada mata cikin rarrashi, ya jima yana rarrashin ta. Kafin ya ta amsa taci kadan.
Jan ta yayi suka yi ta yawo a cikin gidan gonan, sun yi yawo sosai sannan, sai da dare yayi sannan ya mai da ita gida, abinka da yarinta. Shiga cikin gidan ta yi tana rakube rakube har ta shiga dakin su.

Kwanciya tayi a kasa, dake ta gaji barci yayi gaba da ita a wurin, sashi gari matar Haladu kanin Salihu me suna Tani, ta bude kofar dakin ta watsa mata sauran ruwan kanzon da dabbobi suka sha, da mugun tsoro ta farka ta fara sosai jikin ta, ai kuwa su da sauran matan Yan uwan bingel suka rufe ta da bulala, tasha mugun bugu. Sai dai kamar abin hadin baki suna mata dukar, bata motsa ba har suka fita. Tani tana aikin diban dawan da zata surfa taji kamar abu ya shiga rigar ta, karkade shi ta je yi ya zuba mata ciwo, wani irin ihu ta kwala tana tuma da tsalle, Larai da Iyatu da gudu suka shiga cikin dakin su, nan ma suka hadu da nasu, tun daga ranar ya zama ko me suka yiwa Anum, sai an musu abin da ya sa suka fara ja da baya da ita kenan, aka shiga turata kiwo. Barkindo kuwa mahaifiyar shi da ta nime shi ranar da ya bar gidan koda ya dawo, sakawa tayi aka rufe shi a daki na tsawon kwanaki...

A kowanni rana na duniya sai ta fita da kiwo, tun bata iya ba dan wani lokaci shanun shiga inda zasu cutar da kan su suke, wani lokaci kuma su ja ta,

**
Bayan shekara takwas

A hankali rayuwa yake tafiya kwanaki yana komawa mako, makwanin suna rikidewa zuwa watanin yayinda watanin suka yi shura izuwa shakaru, a hankali Lamido da Gidado suka zama samari karti majiya karfi da kyau, sai da ta kai matasa biyu idan ba kowa ya dauki abinda yake so ba, ba zaka banbance su ba, ga lamido tun wani zuwan shi kasar sudan aikin jahadi ya kuma dauki wata dabi'ar su, shine saka mayafi a rufe fuska. Idan ya lullube fuskar shi zaka dauka irin Bararojin nan ne ko irin larabawan kauye kyawawan nan, a duk lokacin da Fulani ta lallee shi sai ta ga kamar Baffa'm ne a gaban ta, sai dai a lokacin da suke basu wuce matasa yan shekaru ashirin da biyar ba, bangaren Gidado wata mahaukaciyar shakuwa suka yi da Fulani Bintu wanda yasa kowa yake da yakinin son juna suke, ita kanta son shi take kamar tayi Hauka. Haka yasa a cikin gidan Fulani Aminatu tasa aka hana mata bayi zuwa cikin gidan sai dai bayinta masu zama da ita sune kawai zasu shiga su taya Innayoh aiki.

Sai dai a lokacin ne Lamido ya hango wata makarantar irin ta addinin musulunci, duk da lokacin ana maganar auren su ne, amma haka ya roki Alfarman a barshi ya tafi makarantar, kallon shi mai Martaba yayi yana faɗin.
"Lamido ka girma fa, kuma kasan Gidado ba zai yarda yayi aure ba sai kayi, karatun zai dauke ka shekara nawa?"
"Allah ya baka nasara akan abinda ya shafi addini ne, zai dauke ni kamar hudu zuwa biyar"
"Allah ya maka albarka"
"Amin Ya Allah, amma ina son mu tafi da Gidado."
"Sarkin yaki kana jin mataimakin ka zai tafi niman ilmi da girman shi "
"Allah ya baka nasara, sarakuna anan su da niman ilmi babu laifi idan ya tafi, ga karfin damtse ga na ƙwaƙwalwa, ranar da Masarautan gobir ta fada hannun shi tabbas ilmi da adalci zai yi aiki" sarkin yaki ta fadi haka, yana yar dariya domin yasan a duniya idan akwai abinda lamido ya tsana shine ka kira mishi mulki, baya son mulki ya amince ya zama garkuwa ga ahalin shi koda haka zai zama fansa ga rayuwar shi.

Sallama yayi musu ya nufi cikin gidan, anan ya samu Bintu ta saka Ammyn a gaba tana murmushi, ita kuma tana bata labarin yadda Lamido sukayi Kuruciyar su, kamar kazar da ya sha ruwa ya wuce abin shi, tare da nufar dakin shi.
"Ammyn dukkan su biyu ne basu magana ko Hamma Gidado ne kawai?" Murmushi tayi tana bin shi da idanu.
"Shi daya ne, na Lamido kuwa sadaukarwar ce a gaban manyan idan ya zama dole yana yi!"
"Ammyn kuma haka ba zai tab'a"
"A'a ba zai tab'a kome ba shi ba, sai dai yana tauye kan shi da na kusa da shi, iya Gidado yake iya fahimtar shi da Innayoh, ban tab'a fahimtar shi ba, asalima kamar surukar shi yake kallona kunyar shi da yakanar shi tana damuna, ba laifi sadaukarwar amma kuskure ne tauye kai" a cikin maganar Ammyn dai ta fahimci wani abu daya, rashin maganar Gidado yana mata zafi amma shirun da Lamido yake yi yana mata yafi kome munanna mata, domin ta kara da cewa.
"Nasan a farkon ciwon gidado Hussain na manta da Lamido Hassan, amma ko da na dawo gare shi sai ya manta da ni da kome na shi, wanda haka kamar kuskure ne ka manta da wani abin da kake so ko sau daya ne da ina son na zauna da shi mu zanta irin na d'a da Uwa amma na rasa wannan hubb'asan!"
Tab'e baki Bintu tayi dama bai tab'a burge ta ba, Allah ya gani tana Tausayin Ammyn domin jarabawa ne haihuwa irin Lamido ita kan a tarihi bata tab'a ganin mutum irin shi ba, ba a tab'a ganin yana dariya ba, asalima kullum fuskar nan kamar hadari, ina dalili zata dami kanta.
"Uwargijiya ta, na gaya miki halittar shi ce haka, lamido yaci sunan shi ne daga gare ki, abinda da yake ba kome bane sai mulki yake bin jinin shi, a duk lokacin da aka samu haka toh sai addu'a."
Dariya Fulani Bintu ta saka tana kallon Innayoh.
"Innayoh kina tsammanin aka bawa wannan mutumin mulki Masarautar Gobir ai a rabin sa'a zai saka. Fille kawunan mutane kawai Innayoh ki bar tunanin zai zama sarki Insha Allah Gidado Allah zai bashi lafiya shi ya dace da zama sarki."
"A'a idan aka kuma maimaita abinda aka yi yadda aka yi akan Sarki Bello, hmm babu me kai labari baki ɗaya." Idanun ta sun kad'a jajjur. Dafe hannun ta Innayoh tayi tana kallon Fulani Aminatu.
"Kiyi hakuri"
"Innayoh ku daina maganar sarautar nan"
"Fatimah zaki iya tafiya" Innayoh ta fada sakamakon fitowar da Lamido daga dakin shi.
Zama yayi yana me sunkuyar da kaan shi.
Ya jima a zaune a gaban ta, matse hannun shi, tashi Innayoh tayi tana jin wani irin Tausayin su.
"Ammyna!" Kura mishi ido tayi.
Kafin ta ce mishi.
"Lamido nifa Mahaifiyar ka ce, Lamido me yasa." Tashi yayi ya zauna akan gwiwar shi.
"Ki gafarce ni, ki yafe min, don Allah kiyi hakuri. Ban san yadda zan yi bane"
"A'a ka sani me yasa gidado ke iya zama ayi hira da shi? Me yasa shi yafika bani lokacin ka haka zaka auri mace tana maka kallon azzalumin mutum? Ni Mahaifiyar ka ban samu lokacin ka ba balle matar da zaka aura" ajiyar zuciya ya sauke domin yasan bata san tafiyar su Sudan ba, dan haka cikin tausassawa ya shiga bata hakuri, yasan duk abinda yake bata so dan haka ya fada mata shirin sa na zuwa karatu shi da Gidado.
"Innayoh kizo" ta kira sunan Innayoh, koda tazo, zama tayi tana kallon su, shi kan shi a sunkuye ita ranta a B'ace.
Innayoh tasan ko wuka ta saka mishi ba zai kuma maimaita abinda ya fada ba, dan haka ita da kanta ta labarta mata, kallon shi tayi kafin ta ce mata.
"Ai banga aibin zuwa karatun ba, kawai sai dai idan zaki ce baki son su tafi ne!"
"Innayoh yayi tafiyar shi ya bar min d'ana da bai da baki" wata irin sirrintacciyar murmushi ya sauke yana kara sunkuyar da kan shi.
Karon farko da ta ga Murmushin da ta kawata kyakyawar fuskar shi, me cike da haiba da kwarjini.
"Innayoh kin ga ya mai dani mahaukaciya"
"Ki ce dai kin ji dadin yayi murmushi kawai, amma ai abinda yake nufi a fili yake waye zai iya tunkarar Gobir bai da ilimin addini da na iya sarrafa al'umma? Ki bar shi kawai ya tafi Allah ya bashi abinda ya tafi nima."
"A'a yayi tafiyar shi ya bar min Yarona wanda ya damu da kuka na, wanda ya damu da damuwa ta."
"Kayya Aminatu kina kuma kara lalata kome kawai Kiyi hakuri ya tafi da shi, haka ma wani nasara ce ta rayuwa"
Aikuwa Aminatu ta kafe tace ba zai tafu mata da Yaro ba da dinbin mamaki yake kallon yadda ta kafe, dan haka ya kaskantar da kan shi ya fara magana cikin tattausar lafazi ya ce...

""Kayya Aminatu kina kuma kara lalata kome kawai Kiyi hakuri ya tafi da shi, haka ma wani nasara ce ta rayuwa"Aikuwa Aminatu ta kafe tace ba zai tafu mata da Yaro ba da dinbin mamaki yake kallon yadda ta kafe, dan haka ya kaskantar da kan shi ya f...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Jarumin maza.....😍

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now