BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
Sosai Innayoh ta tura aka gyara daya daga cikin yan matan, sannan ta dawo wurin Fulani Aminatu.
"Na miki abinda ban tab'a b'ata ba, amma qaddarar mutum yana zane ne tun daga ranar da aka haife shi, kiyi hakuri da abinda nayi amma ya zama dole ne nayi haka, na tura mishi daya daga cikin su."
Kallon Innayoh tayi taga ta cika mata Idanu, dan haka tayi kasa da kai tace mata.
"Duk yadda kika yi daya ne." Daga haka ta cigaba da gyara kumbar ta, ta wani dauke kai kamar bata taɓa magana ba, murmushi Innayoh tayi domin bata dauka Fulani Aminatu zata iya bayyana kishin ta kai tsaye haka ba, har zata bar wurin ta ce mata.
"Duk abinda zan yi ba zan taba yi dan jin dadin kaina ba, kuma ba zan yi dan na kuntatta miki ba, zan yi ne domin kare mutuncin ki" daga haka ta bar wurin, bata ji zafin yadda Fulani Aminatu tayi ba dan tasan dole tayi kishin Mijinta, abu na gaba shine addu'a kawai domin abinda tayi ya samo asali ne daga Inna Marwa. Ita din kusan Gwaggo takewa Sarki Bello kuma yau kwana huɗu kenan da zuwan ta. Sun je sun gaida da ita da Fulani Aminatu, kuma Alhamdulillahi Innah Marwa ta yaba da Aminatu sai dai bayan sun bar shashin ta, Ajuji ta ke fadawa Inna Marwa cewa.
"Uwa yarinyar nan bata haihuwa, kuma an bawaai Mai Martaba kwarkwarah yaki amsa"
Juyawa Inna Marwada tayi sannan tace mata.
"A kira min Jakadiyar Gobir"
"Wo!" Ta rike bakin ta, sannan tace mata.
"Baki da labarin Sarki Bello yasa a kashe ta, amma don Allah karki ce a bakina kika ji" shiru Inna Marwa tayi sannan ta ce mata.
"Toh tashi ki ban wuri, kuma a kira wacce take matsayin Jakadiya yanzun"
"Ai Innayoh ce wacce suka shigo tare da Aminatu"
"A kira min ita"
"TOH" kowa da aka kira Innayoh, tazo ta durkusa a gaban Inna Marwa, ta kuma kira Sarki Bello da galadima, suka taru a gaban ta.
Shiru tayi kafin ta d'ago kai, sannan ta ce musu.
"Innayoh kece Jakadiya ko?"
Gyara durkuson tayi, kafin ta ce mata.
"Eh Fulani Inna Marwa" murmushi dattijuwar tayi sannan tace mata.
"A matsayin ki ba iya Jakadiya ya kamata ki dauka ba, hatta fannin uwa ya ka mata ki dauka, shin uwar arziki zata so ganin ana jin ciwon abinda yake faruwa sanadin Yar ta?" Sunkuyar da kai tayi tare da damke zaninta, sannan ta girgiza kai.
"Toh me yasa Fulani bata bawa kwarkwarorin nan damar shiga wurin mai Martaba ba?"
"Laifina ne Fulani Inna Marwa. Nice ban tunatar da ita ba, insha Allah haka ba zai kuma faruwa ba"
"Yana da kai ki kara mata kima ta hanyar nasiha da tunatarwa, idan haka samu haka ba makawa an kashe bakin masu kaiwa da komawa, duk lokacin da Fulani ta shiga kwanakin ta na al'ada a tura mishi wacce zata dauke mishi laluran kwanakin, idan ta dawo kuma a dakatar da kowacce mace shiga turakar shi sai ta sake shiga kwanakin" idanun Innayoh ne ya cika da kwalla ta rasa kuka zata yi ko farin ciki, sannan ta cigabq da cewa.
"Yan mata hudu sun mishi yawa a bar daya me kyakyawar sura da nutsuwa"
"Toh Fulani Inna Marwa an gama" haka ta gama tsara kome, sannan ta sallami Innayoh, juyawa kan Galadima tayi sannan ta ce.
"Wani kokari kayi na matsalar Aminatu da Bello" gyara zama yayi tare da sunkuyar da kai kasa ya ce.
"Inna Marwa, basu da matsalar kome. Jinkiri ne kawai daga Allah, idan da zaa yi hakuri sai abin ya kasance"
"Ban gane ba?" Ta kuma tambayar shi,
"Dukkan su lafiyar su lau" ya fada a hankali, Inna Marwa irin matan nan ne da suka taso cikin iko da bada umarni, abinda ta sani shine mulki ya bi jikin da ta jinin ta, sannan tana cikin manyan matan masarautan Sokoto, domin tun zuwan shehu Usmanu danfodiyo, aka bada auren ta ga Wazirin Sokoto kuma babban Almajiri Shehu Usmanu danfodiyo, sai kuma aka yi dace mijin ta an bashi Sarkin rikon kwarya, har ya rasu, wannan dalilin yasa ta jin gaba da baya mulki ya samar da ita, bata cika zuwa ba daga biyar ko goma, amma idan tazo kowa na fadar nutsuwa yaƙe, (zamu iya kiran da da dowager Mother she is not empress but she has a more powerful than king) Dan haka ko a Sokoton tana da tarin Darajojinta, ga ilimin addini da Allah ya bata, haka ya cire mata kyashi da hassada, sannan kaifi daya ce bata magana biyu, idan tana wuri ba a kawo mata wargi, asalin bagobiyar ce da ta samu damar yin rayuwa kamar kowacce matar sarki, sannan tana Tausayin Fulani Aminatu, domin tana tsakiyar makiya ne, tun kafin ta iso aka gaya mata cewa Bello ya amshi auren bafulatana kuma sai yadda tayi da shi, a tunanin ta zata samu hamshaqiyar mace abin tausayi sai ta ga yarinyar kusan sa'ar jikan ta na goma sha biyar ce, sannan tasan tasirin kiyayyar kowacce masarautar domin ita ɗaya ce bagobiyar a cikin masarautar Sokoto, dan haka ta sha wahala da mijin su da kuma kishiyoyin ta da kwarkwarorin sarki a lokacin, kai tun kafin ya zama sarki ma yana da kwarkwarorin biyar da yazo ya zama sarki sai abin ya ta'azzara har ta kai sai tayi sama da wata biyu bata saka shi a idanun ba, domin ko tace tana son ganin shi basu barinta ta isa gare shi. Idanun ta ne ya cika da kwalla. Domin tuno rayuwar ta, yana yawan saka ta kuka domin bata mori miji ba, sai rabon Yara ne idan ya tsaga toh ko da rana ne sai ya tura Jakadiya ta dauko ta, haka ya faru ne sakamakon mugun son da yake mata, da Kwarkwarah ce ba za'a tab'a damuwa ba sabida sun san ba matar sarki bace, amma matar sarki matukar sarki zai so ta tashiga uku.
"Ka koyawa kanka boye soyayyar ta, domin shine makamin da za a yake ku, ka rungume abinda suka baka." D'ago kai yayi ya kura mata ido. Sannan ya ce mata.
"Inna Marwa idan na ajiye sarautar akwai me tuhumata ne da naso mata ta" rike hannun shi Galadima yayi yana girgiza mishi kai.
Tabbas dan dan uwan ta yayi nisa, itama da haka ta samu yanci a Sokoto da yau bata yi kuka ba.
Sai dai ita mijin yayi kokarin yaki da soyayyar ta ya kuma zauna lafiya, a duk lokacin da yake tare da ita yana yawan gaya mata ya nisan ta kan shi ne domin ta zauna lafiya da sauran matan da Alummomin masarautan,. Kasancewar ta bagobiyar a cikin Masarautan fulani. Dan haka dukkan hanyar da zai nisanta shi da ita yake bi, ba wai dan baya son ta ba. Idan ta kama ya nisanta kan shi da ita har abada toh zai yi kuma zai iya domin ita da yaran ta su zama abin alfahari a cikin Masarautan, kuma izuwa yau itace mahaifiyar Sarkin da yake mulki.
Gyada kai tayi kwalla zuba mata ta ce mishi.
"Kana zaton dan ka ajiye mulki zasu fasa yakar ka ne? Kana zaton ko kayi nisa da gida zasu fasa bibiyar ka ne? Kowani motsinka suna tare da kai ita ce basu kauna a cikin Masarautan. Zuwan ta ua kuma karawa mulkin ka albarka, zuwan ta ya saka kaf nahiyar nan babu na biyun ka, daga shekarun da ka aure ta zuwa yanzu ka duba sauran yankunan da suke kewaye da kai? Ka san ko yaki babu wanda ya tunkare ka da shi? Shin kasan me yasa hil ta nime aba da ita? Domin karfin tsafin su ya kara samun daraja, sannan a kodayaushe ko wani lokaci ta haifawa sarki Arkhan da namiji, kenan Masarautan nan kowa yasan abinda yake faruwa kai ne basu bukatar da cigaba dan haka ruwan ka ka zauna da matan ruwan ka ka rabu da su amma tabbas shirin su akan Aminatu rubutacciyar al'amari ne ko ba yau ba" sannan ta juya ga galadima.
"Sarkin gida ya gaya min abinda ya faru, waye kuke zargi da sakawa a tare Ku?" Shiru tayi tana kallon galadima. Nan ya shiga mata bayani tare da abinda ya sani, sannan ya kara da cewa.
"Ina zargin Yakubu ne, domin na a an zane min shi kwanakin baya, idan ba shi ba toh ban san waye zan kama ba"
"Toh ka tabbatar yayi alaka da Kwarkwarah da aka zab'a mishi sauran a maidawa Chiroma a gaya musu ni Marwa na dawo mishi da tarkacen shi, kwarkwarah daya ta wadatar da shi. Alakar ka da Kwarkwarah ba shi zai saka Aminatu ta wanke kanta ba, sai dai idan yau ta zubda jinin haihu shine kawai zai dakatar da kome, ba naki aminatu bane kiyayyar da ake mata idan baka da lissafi kaima shiga cikin su zaka yi tashi ku bani wuri"Daga haka ta juya kanta, dakyar ya mike tsaye kamar zai fadi, tana halkance da shi, amma ta dauke kai. Yana fita kuwa ya nemi wuri ya zauna, wani irin zafi yake ji.
"Dama abinda ya hanaka tsayawa a tsagina kenan?"
"Abubuwa dayawa sun faru amma yanzu a dakatar da wannan batun mu fuskanci gaba.""Amma kasan ina sonta ko?"
Ya tambayi galadima.
"Na sani" idanun shi ne suka yi wani irin ja...
Wannan shine abinda ya faru, dan haka Inna Marwa tana cikin masarautan kuma ba a daina kawo mata gulmace-gulmace ba, dan ma ta toshe kunnen ta, ta kima fatattaki masu kawo mata gulmar.Koda Innayoh ta tafi dakin bayan tare da taimakon wasu manyan bayi mata suka shiga duba yan matan sai dai cikin ikon Allah zun zabi Bingel duk yadda aka yi sai da ta fi sauran matan dan haka suka tambayi sunan ta.
"Ya sunanki?"
"Yahanasu" janta aka yi zuwa wani sashi na daban, aka shiga mata gyaran jiki, tsawon kwanaki uku ana gyara mata jiki, sannan Innayoh ta sallame sauran yan matan, ita kuma aka kai ta wurin Inna Marwa. Kallon fuskar ta yayi sannan ta ce mata.
"Ki sani ba wai zaki iya zama wata abu me daraja bane ke kamar juji ce, a duk lokacin da ya kwaso sharan shi akan ki zai watsa, bari na gaya miki ko me zaki yi ba zaki tab'a samun damar inda kike ba, ki ajiye a ranki Aminatu bata miki kome ba, idan kuma wani abu ya biyo baya, zamu saka a zartas da hukuncin bisa ga abinda kika aikata"
Shiru tayi, bata tab'a tsannan kanta ba sai yau dan haka bata iya magana ba, domin akan ta isa ga sarki Bello sai da aka gaya mata magana. Dan haka Inna Marwa ta cewa Innayoh.
"Ki sanar da Fulani Aminatu, za'a kai Bingel ga Bello tayi hakuri duk wanda ya zabi tafarkin gaskiya Allah zai bashi ikon cimma inda yake."
Gyada kai Innayoh tayi sannan ta fitar da Bingel, aka mai da ita inda suke, sannan aka ware mata bayi mata biyu, daya babba me suna Lanta da Goshi,. Aka bata su zasu taimaka mata da duk abinda take bukata, sai gefe guda kuma aka bata wata dattijuwa me suna Larai, ita kuma tana saka ido ne akan duk wani motsin ta. Wannan shine abinda ya faru.*
Tunda Innayoh ta gaya mata cewa ai za a tura kwarkwarah sashinsa, ta shiga daki ta rufe kofar, shima da kan shi yazo amma fir taki bude mishi kofa, abin ya bashi haushi dan haka ko da ya fusata dukar kofar yayi sai da kofar ta karye. Nufarta yayi tana zaune. Durkusawa yayi a gaban ta.
"Ko duniya zata juya Miki baya ina tare dake, me yasa zaki tona min asiri domin jin dadin wasu? Me yasa zaki juya min baya domin wasu? Kin san yadda nake jin ki a raina? Kin san yadda na damu dake? Me yasa ba zaki gane ba, don Allah kar ki kuma nisanta kan ki dani, ina iya rasa nawa farin cikin, indai ke zaki rayu cikin salama...
#Mai_Dambu
YOU ARE READING
KALLABI..! A tsakanin Rawuna...
Historical FictionThe gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny...