BABI NA DAYA

2.4K 266 55
                                    

ƘALLABI...!
      A tsakanin Rawuna..

          *<Babi Na Ɗaya>*
           ~FREE BOOK~
        Na
  Mai_Dambu

  EWF

*Har ila yau SADAUKARWAN taku ce Aminan kwarai a gudu tare a tsira tare*
Zahran Addah Ramlah
       Da
UMNASS din Mai_Dambu

GODIYA TA MUSAMMAN GA SANAH MATAZU

Shimfida.

Kasar gobir na ɗaya daga cikin kasashen hausa
na ainihi, ance ita ɗin tsohuwar daula ce kuma
wata babbar kasa ce da tayi iyaka da Agades
daga arewa, tayi iyaka da Zamfara daga Kudu,
tayi iyaka da Mayali daga Gabas, sannan kuma
daga yamma tayi iyaka da Konni.

Amma magana anan itace, asalinsu ba
hausawa bane tunda wasu nacewa asali waiƴ
daga gabas ta tsakiya suka fito musamman ma
Misira, inda ake da yakinin cewa Sarakuna ukku
daga cikin sarakunan Misira gobirawa ne.

Sarkin Gobir Mai daraja Alhaji Abdulhamid
Balarabe Salihu ya taɓa faɗar asalinsu a wata
fira da jaridar 'Daily Trust' tayi dashi, shine yake
cewa:
Gobirawa sun zone daga misira (egypt). Har
Yace su jikokin Annabi Nuhu A.S ne kuma sun
bar misira saboda wahalar mulki na sarakunan
lokacin. Shine suka sauka a wani wuri mai suna
Gubur. Daga nan ne suka samo sunan Gobir.

Yaci gaba da cewa daga baya sun isa Yemen,
sunyi yaki sosai a kasar saboda su suna da jinin
yaki da jarumta. Daga nan kuma sai suka isa
libya, a haka suna matsawa har suka zo wani
gari mai suna Azbin inda yanzu mutanen Taureg
suka mamaye.

Da suka bar Azbin sai suka shiga sahara, har
suka kafa wani gari mai suna Magali, daga baya
sai suka bar garin izuwa wani mai suna Surukul
(dukkansu yanzubsuna jamhuriyar Niger ne). A
hankali suka riski birnin lalle da gwararramu a
karni na 15 zuwa na 16. A lokacin kuwa, Sarkin
zamfara Abarshi ke mulki wanda yake da zama a
Katanga, kuma an samu har ya auri ɗiyar sarkin
Gobir mai suna Fara, wadda ta haifi Sarkin gobir
Ibrahim Babari..

Kafin Babari ya zamo sarki, ai sai dayayi faɗa
da Sarkin Zamfara na lokacin kuma yaci karfinsa.
Akan haka sarkin Zamfara ya kuduri niyyar
halakashi, amma sai yayarsa ta maido dashi
kasar mahaifiyarsu watau Gobir, a haka kuma har
ya zama sarki (Watau yayi gado ta wajen Uwa).

Babari ya roki Sarkin gobir ya bashi wuri a
yankin Zamfara inda zai zauna, amma sai aka
gargaɗi sarkin Zamfara da cewa kul ya baiwa
Babari gurin zama domin nan gaba zai iya
mamaye zamfara dukkan ta, ai kuwa daga bisani
hakan ne ya faru, da yaki ya ɓarke a wajajen
karni na 16 zuwa na 17, sai da Goburawa suka
cinye har Alkalawa da yaki. (abinda ke nufin inda
suke zaune ayau asali kasar zamfara ce)
Sarkin Gobir Abdulhamid ya kara da cewa " A
lokacin Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo (Karni na
17), ance an ruwaito cewa Ko zakaru basa cara
sabida jarfin tsafinsa, kuma aduk yake-yaken da
sukeyi, gobirawa basu taɓa mika wuya ba. Ance
sunfi gwammacewa a kashe su akan su mika
wuya, shiyasa ake musu kirari da 'Gobir gidan
faɗa'.

Sarkin yace " Bawa jan Gwarzo bai taɓa yaki
da Shehu Usmanu ba A zamanin jihadi, maganar
gaskiya ma itace shehu ya koyar da 'ya'yan
Bawa, ciki harda Yunfa, Atiku, Bello da Mayaki.
Ance ma saida shehu yayi musu nasiha da kada
su bari a samu rarrabuwar kawuna a tsakanin su.
Sarkin yace " Mutanen dake kusa da Bawa
sune suka haɗa kiyayya a tsakanin su, wanda
yayi silar shehu yabar Alkalawa, daga baya kuma
yaci gaba da jihadi a sassan sokoto.
Dan gane da tsagun gobirawa, Sarkin yace asali
basu da tsagu a fuska, amma sabili da yake-yake
ne yasa suka rinka tashi daga nan zuwa can, don
haka suka ɓullo da tsagu domin su rinka shaida
junansu.
(Bari mu daura labarin)
_________________________________

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now