WACECE NI??? Part2 By Cutyfantasia chapter three

172 21 3
                                    

A take yanayin Hamma ya sauya gabadaya, damuwa ta lullube fuskar shi! Cikin karfin hali yace

"Sadik bashi da lafiya! Ya shiga wata damuwa ne akan wani abu, Aunty kuma tace ta tsine masa idan har aka bashi abunda yace yana so, so wannan damuwar ce guda biyu ta jefa shi cikin wani hali, har ya soma shan magungunan da zasu saka shi bacci, daga nan kuma abubuwan suke son yin nisa domin ya riga ya zama addict, kuma ba kananan abubuwa kawai yake sha ba......."

Tuni hawaye sun jiqa mata fuska! Wani irin tashin hankali take ji da tausayin Sadik! Wani mutum wanda ba zata taba mantawa da shi ba cikin rayuwarta ba, Sadik na jerin mutanen da suka nuna mata soyayya da kulawa a lokacin da Inna take tsakiyar kuntata mata! Sadik na daya daga cikin wanda suka tsaya tsayin daka akan dawowar walwala da farin cikin ta, Sadik ya taka rawa a rayuwar ta kuma ya nuna mata soyayya da kauna da karamci duk da cewa basu hada alakar jini ba! Toh ya za'ai ba zata shiga tashin hankali akan halin da ya tsinci kansa a ciki ba?

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Hamma me yake so? Me yake so ba'a bashi ba? Me yasa Aunty tayi masa haka?"

"Maganar abinda yake so ta wuce tunda mahaifiyarsa ta riga tayi masa baki! Sai dai hanyar da za mu bi mu ceto shi"

"Hamma wacce hanya ce? I'm willing to help no matter what it takes! Ya Sadik mutum ne Hamma, bai taba juya mun baya ba! I would really like to help don Allah"

Shiru yayi yana jin wani irin daci da bacin rai da kuma muguwar tsanar Aunty a zuciyar shi! Ba don abubuwan da tayi ba, da tuni shi ne zai jagoranci kulla auren Sadik da Ihman with so much pride and love! Ko ba komai ya san Ihman tana safe hands, Sadik ba zai taba wulakantar da ita ba, domin ya yarda da irin soyayyar da yake mata, sannan shi kuma Sadik din to save him don ya tabbatar soyyyar Ihman jarrraba ce ga Sadik, idan har bai same ta babu abinda ba zai iya faruwa da shi ba, even worst than this! Toh Allah ya hada shi da shu'umar uwa mara tunani da mutunci, da kanta ta rusa masa rayuwa kawai saboda wani dalili mara hankali.

"Hamma kace wani abu"

Ya sauke ajiyar zuciya yace

"Ahm! Ihman right now, Sadik bai bukatar kowa, he needs to be alone, muna komawa gida zan dauke shi zuwa Germany for proper medical check up and treatment ! Insha Allahu rayuwar Sadik ba zata tagayyara ba, da izinin Allah ba zai durkushe rayuwar shi ta nakasta ba! Nayi wannan alkawarin!"

Ta sake share hawaye tace

"Zan iya magana da shi don Allah?"

"No Ihman you can't! Kuma anan zaki mun alkawari da bakin ki ba zaki taba kiran Sadik a waya ko ki nemi wani ya hada ki da shi ba."

Cikin mamaki take kallon Hamma

"Yes! Na san dalilin da yasa nace haka kuma ina fatan ba zaki tambayeni ba, i know you trust me akan duk abinda zan hana ki akwai babban reason behind it! So for now, don Allah kibi maganata kuma bana son bayan ni ki sake tambayar wani akan maganar Sadik! Promise?"

Idanun ta na fidda hawaye ta girgiza kai! Wannan al'amari ya dake ta ba dan kadan ba! Hankalin ta ya tashi kwarai. Amma tayi alkawarin za ta saka shi cikin dukkan addu'ar ta safe rana dare, da albarkar Manzon Allah saw sai ya samu nutsuwa da lafiya.
Sun dade a zaune suna tattaunawa da Hamma, anan take gaya mi shi burin ta naci gaba da zama a Ghana

"But why Ihman? Kaura zaki mana?"

Cikin sanyi tace

"Hamma bana son Nigeria! Daga Gombe har Kano are not safe for me a wannan halin, Hamma ko zan dawo sai bayan wani lokaci kadan, by then hankalina ya kwanta na samu nutsuwa!"

Kwarai shima na shi tunanin kenan, Ihman ta zauna hankalinta ya kara kwanciya, hakika tana bukatar chanjin environment kamar yanda ya shirya musu tafiya Rusia a baya, toh nan tana gida ne ma, gaban mahaifinta, wanda shi ma yake bukatarta kusa da shi! Bayan ta haiwu an san abinda za'a yi sai ta koma gida! Amma daman bai yi niyyar furtawa ba saboda ko da wasa kada wani yayi tunanin suna son nisa da ita ne saboda halin da take ciki.

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now