💔WACECE NI???💔 part2 page Twenty nine by CUTYFANTASIA

55 6 0
                                    

A WEEK LATER
A cikin wannan satin da ya biyo bayan daurin auren Ihman da Faris babu abinda yake wakana sai matsanciyar hidima da murna da shiri na ban mamaki. Da Amarya da Ango sun kammala yanke decision din su don haka babu wanda yayi musu shishshigi! Duka kayan dakin Ihman sai aka loda su cikin warehouse din Hamma da ke Sharada.
This time, Uncle da kan shi yayi tattaki daga Ghana ya taho Kano for the first time ya taka gidan Inna cikin karsashi da kwarin guiwa da kuma madaukakin farin ciki. To explain yanayin da Ihman ta tsinci kanta a ciki is a whole book, kawai dai duk sanda ta nisa tana godiya ga Allah da ya bata ikon cinye jarrabawar da yayi mata.
Uncle Sa'id yayi amfani da wannan dama ya ziyarci masoyiyar shi Dr.Amani wadda ta rasa inda zata sa bakon nata saboda murna. Kuma sun yi amfani da wannan opportunity din sun je AKTH an musu running duka tests din da suke bukata duk da cewa kowa ya san status din sa. Babbar maganar da kullum Sa'id yake jaddada mata tana kawarwa ita ya sake dawo mata da ita cewa fa an taba ce mi shi ba zai sake haihuwa ba lokacin da yayi accident a wani a asibiti a Ghana. Ta dube shi a nutse tace

"Bayan wannan lokacin ka sake zuwa asibiti anyi maka bincike an yi diagnosising din ka da Infertility? An tabbatar maka cewa ba zaka iya haihuwa ba?"

Ya girgiza kai cikin rauni.

"Then you can't conclude"

Daga haka suka wuce wajen abokiyarta Dr Siama wadda ta hada su da kwararren urology consultant a washegarin zuwansu wajenta. A yinin ranar Uncle Sa'idu yana tsakanin laboratories ana aune aune da gwaje gwaje ba shi ya koma masaukinsa ba sai yamma liqis!
Cikin ikon Allah da qarfin qaddara sai ga result mai sanyaya zuciya ya futo, don matsala akwai ta amma ba permanent bace kuma da taimakon Allah da wasu magunguna da allurai zai warke tas kamar abun bai faru ba. Wannan labari ne mai matukar muhimmanci da alkhairi da farin ciki ga duk Maigoro family da ma wanda yake kaunar su.
A tsarin ango Faris da amarya Ihman basa son bidi'a kuma basa bukatar dinner din da za'a hadu maza da mata a dinga abubuwan da basu kamata ba don haka suka hada kai suka ce su lallai sun yafe duk wani shagalin da za'ayi maza da mata Hamma ya goya musu baya, yace ayi wa kowa abinda yake so a bikin shi. So da wannan ne aka yanke events din zuwa guda hudu, kamun amare ranar laraba, Maigoro zasu yi nasu event din da amare ranar alhamis, daurin auren Asma'u ranar juma'a da daddare dinner din Asma'u kamar yanda take so sai ranar asabar kai amarya Asma'u zuwa garin Abuja yayinda Ihman zata qarasa jiran visarta sannan ta su wuce Egypt da Faris. A cikin satin kuma Alhajin Ghana ya tura neman auren Dr Amani aka kai kudin zance da sa rana watanni hudu masu zuwa kamar yanda ta bukata saboda harhada abubuwan da suke gabanta musamman asibitin ta.

Ranar talata duk wani wanda yake da ruwa da tsaki cikin wannan auren ya sauka a garin Kano, yan Ghana suna can Sultan Road cikin hamshakin gidansu, mutanen Niger yan'uwan Aunty suna gidan Hamma da ke Rijiyar zaki, sauran yan'uwa da daidaikun yan'uwan Abba suna cikin gidan nasu ana hidima kamar ba'a taba taron wani biki ba sai akan wannan. Faris yayi kokarin shirya lefensa, Uncle Mustafa ya nuna masa bacin rai sosai akan hakan ya kuma umarce shi da kar ya sake kokarin yin wata hidima da kan shi. Ba'a son ran Faris ba Uncle Mustafa ya bayar da kudi matar shi ta hado lefe na alfarma aka kai gidansu Ihman! Gefe guda yana ta addu'a da takatsan-tsan ayi bikin nan a gama Falmata bata ballo masa ruwa ba, kusan abinda ya rage masa armashi a bikin kenan, Falmata da tantrums dinta. Shi bai taba bude baki yace yana son ta ba, bai kuma nuna mata wata alama da zata saka tayi tunanin hakan ba amma tabi ta kanainaye duk wasu al'amuransa ta hana shi sakat! Yana fatan kada Allah yasa maganar ta kai ga mahaifinta domin ba zai iya ce masa a'a ba, he has done soo much for him a rayuwa don haka fatansa a gama biki ya lallaba ya gudu Egypt da amaryasa kowa ya huta.

Ranar laraba aka yi kamu a Grand marque na "Afficent" da ke Kano, tsayawa bayyana tsaruwar bikin zai bata lokaci mai yawa domin tun daga kan decor din zaka fahimci bikin ba ordinary bane.
Dukan yayan gidan Manager(Abba) da surukansa shiga iri daya suka yi ta embroidery wax navy blue wadda ta haska farar fatar su kamar taurari. Amaren iri daya suka yi sai dai kowacce da kalarta. Anyi taro cikin walwala da farin ciki da matsananciyar murna an kammala komai cikin tsari lami lafiya.

Washegari alhamis kuwa taron na Ihman ne domin Maigoros ne suka shirya nasu event din a Amani event center, tun ranar kamun Ihman taji ta gaji, don ita har zuciyarta bata son yanda ake raye rayen nan ana zuba kudi kamar ba'a san darajarsu ba bayan akwai dubban bayin Allah da suke cikin wani hali. She's a very simple person, da son zuciyarta za'a bi toh da daurin aure kawai za'ai a zarce da walimar mata a cikin gida shikenan ya wadatar.
Tana wannan mitar a ranta mai kwalliyar da Asma'u ta dauko tun daga Abuja tana kalailaye mata fuska bayan ta sha warning a wajen Ihman kan idan har ta chanja kama toh wlh sai an goge. Fahimtar halin amaryar da artist din tayi ya sanya ta nutsu tayi mata soft make up wanda yayi enhancing kyawunta kawai ya sake fiddo mata kamanninta.
Wani azababben excelsior lace tayi amfani da shi kalar navy blue wanda ya ciza sosai da touch din pitch. Skirt and blouse daga fashion house din "Hudayya" wadda suka zauna mata cif kamar an zana.
Zaka so kallon yanda wannan clrs suka fiddo da annurin hasken fatarta musannan head din da aka yi mata turban da shi pitch da kuma makeken veil din da akai pinning akan daurin shima pitch. Duka custume din ta gold ne qirar bahrain. Kana kallonta kaga yar gatan amaryar da ta jiku da gyara ta tattali da kauna da soyayyar yan'uwa da iyaye.
Wannan event din har yafi na kamun dadi saboda bai kai cikar kamun ba, Maigoro hada Ihman suka yi da Asma'u suka mayar nasu a wajen bikin aka sha shagalin da biro ba zai iya fayyacewa ba aka tashi.

The next day aka daura auren Asma'u aka kuma yi mata dinner din ta da daddare a Meena event center wadda Faris ya hana kan shi da Ihman zuwa ta kuma yi biyayya tayi zamanta ba tare da sauraren ciwon bakin da dangi suke mata ba. Daman ita bata da ra'ayi kuma tunda ta gane angon Asma'u tantagaryar dan gatan Saurayin Abuja ne ta tabbatar wannan dinner din sai abinda hali yayi, ai kuwa an dawo ana salallami da gigizuwa da bidirin da suka yi wajen rawa da liqi da uwa uba shigar da suka yi mazansu da matan abun gwanin ban mamaki.
Asma'u da taji haushin Ihman amma daga baya suka rewaye suka shiga sabgoginsu. Ranar asabar aka yaye zuwa garin Abuja, inda aka sake tarar da wata kasaitacciyar dinner din ta karbar amarya kamar basu san ciwon kudi ba, sai lokacin aka sake tabbatarwa family din mijin Asma'u masu kudi ne, tun daga kan lefe, kudin aure da duk abinda ake yi na hidimar aure na Asma'u yafi ma Ihman, amma ko kadan Ihman din bata kalli abun balle ta saka shi cikin ranta ba. Ita fa wannan Faris din ko a dan dako yazo tayi ihmanin zata amince ta zauna da shi.
She's not a luxury person kuma kyale kyalen rayuwa basu dame ta ba, tana karbar komai a yanda yazo mata, bata da zuzzurfan buri akan komai bayan ilmi don haka take rayuwarta cikin lumana da kwanciyar hankali. Asma'u ce yar qarya kuma Allah ya amsa mata ta samu abinda take so don haka take jin kamar tayi tsalle ta tabo gajimare. Sun taho sun barta cikin tsararren gidanta wanda Hamma ya armasa mata shi da kayan alatu.

Aka ce for every beginning there must be an end, duk abinda yayi farko toh zai yi qarshe sai dai idan ba'ayi hakuri ba. Cikin hukuncin ubangijin al'arshi anyi auren Ihman da Faris an kammala, duka al'amuran da suka faru sun zama tarihi, kuka ya qare farin ciki ya maye gurbin shi sai fuskantar wata sabuwar rayuwar da ke tunkarowa.
A cikin satin da aka kammala biki hutun Faris ya qare ya koma Egypt, a zahiri kenan, a badini kuwa plan din Uncle Sa'idu ne domin ya lashi takobin inganta rayuwar kwallin diyar sa a ko'ina ta tsinci kanta a duniya. Tunda ya tabbatar zaman Egypt ya kamata ya soma neman yanda zai siya mata gida a kasar domin yayi alkwarin Ihman ba zata zauna a gidan da ba nata ba ako ina ne a fadin duniya. Kamar Faris zai yi jayayya Uncle Sa'id ya soma yi mi shi bayanin da ya raunana shi.

"Kada ka tauye mun damar da na samu bayan gushewar wani tsatstsauran lokaci a gare ni. Ban taba samun damar yi wa Ihman hidima a matsayin mahaifi ba tunda tazo duniya har aka yi bikin aurenta. A wancan lokacin tara kudi kawai nake yi zuwa wani wa'adin da na yanke zan sadaukar da su ga marayu da gajiyayyu kafin kasa ta rufe mun ido. Tunda Allah ya dubeni ya dawo mun da Ihman nayi alkawarin amfani da duk abinda nake da iko da shi wajen bata ko da rabin rabin farin cikin da bata taba samu daga gare ni bane a lokacin da tafi bukatar hakan.
Faris nayi ihmani da Allah da mazonsa nayi ihmani Rukayya(ihman) ba zata wulakanta ka ba akan kowanne irin yanayi ta same ka. Abubuwan alatun duniya basu samu waje a cikin zuciyarta ba balle ta rufe ido ta zabe su akan ka. Duk da haka bazan ce komai a game da gidan nata ne ba a yanzu sai bayan lokacin da ya dace amma tabbas ni ne zan nemawa Ihman gidan zama me kyau wanda zaku ji dadin rayuwa a ciki a iya tsahon lokacin da zaku dauka a garin Cairo."

Da wannan yaci galabar Faris suka shirya komai ba da sanin kowa ba. Bayan Faris ya koma Uncle Sa'id ya bi shi suka soma neman gida da taimakon mahaifin abokin Uncle Sa'id ambasada Abdulmumin har Allah yasa aka samu gidan duk da cewa sai anyi remodeling din shi kafin ayi furnishing a shiga. Process din was very very hectic amma da taimakon ambasada aka kammala sai dai lokacin da aikin yayi consuming ya sanya dole Uncle Sa'id yayi wa Abba bayani domin sai da Ihman ta kwashe watanni hudu a Nigeria.

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now