WACECE NI???Part2 page Twenty BY CUTYFANTASIA

173 14 3
                                    

Unedited ⛔️

Cikin sauri Kamal yaci burki ya gangara gefen hanya yayi parking hankalinsu a tashe, yana tsayawa Ihman ta ɓalle murfin motar ta futa ta samu bakin hanya ta durƙusa tana ci gaba da kwara amai kamar hanjin cikinta ta zai futa. Adda Wasila na gefenta tana bubbuga mata baya tana mata sannu, daƙyar ta samu aman ya tsaya Faris yayi maza ya koma mota ya ɗauko goran ruwa ya miƙawa Adda Wasila ta bata ta kuskure bakinta suna ta jera mata sannu!
Ta daɗe a tsugune tana mayar da numfashi tare da shaƙar iskar da ke kaɗawa kafin ta samu relief! Adda Wasila ta taimaka mata suka koma mota amma Falmata ko gizau, tunda tayi mata sannu sau ɗaya bata sake kallonta ba ta koma mota ta zauna abunta.

Idanunta a kulle ta sake jin maganar Faris cikin Command yana cewa

"Kamal mu wuce asibiti"

Kamal yace

"Nima tunanin da nake yi kenan Ko Wasila?"

Adda Wasila zata yi magana Ihman ta riga ta magana a wahalce

"Ni bazan je wani asibiti ba naji sauƙi"

Kamal yayi dariya yace

"Ai ba zamu bari ayi miki allura ba kar ki damu"

Duk turjewar Ihman sai da suka kaita asibitin nan don bin umarnin Faris, shi gogan tunda yayi maganar sau ɗaya bai sake ba! Sai waya da kira ya soma wannan maganar ta shi mai kama da karatu

"Hello Dr. Amani"

Ya saurara sannan yaci gaba

"Alhamdulillah!kina gida ko asibiti?"

"Ok i will be on my way"

Wannan ikon Allah da yawa yake, inji zuciyar Ihman! Wai me mutumin nan yake taƙama da shi ne? Wanne nau'in rainin hankali ne wannan? Me yake so ya maida ita?

Iya kunnuwa Ihman ta kunnu kafin su isa asibitin, har wani tsumar zazzaɓi take yi na ɓacin rai amma sanin maganar tata bata da amfani ya sanya tayi shiru ta lumshe idanunta tana kiran sunan Allah.
Wani private clinic ne sabo me azabar kyau, suna shiga reception ya sake kiran Dr.Amani, da kanta ta futo daga office ɗinta tayi musu jagora, daga baya nurse ta taho da file ɗin Faris wanda ya kame a kujerar da take kallon ta likitar yana ƙasaita.

"Sannu Ihman"

Sai lokacin Ihman tayi wa Dr Amani kallon tsanaki, Da wuya ta wuce shekaru talatin da biyar, baƙa ce doguwa, me kyau. Ba kuma kyan ne kawai zai ƙayatar za kai ba sai far'a da sakin fuskarta, tana sanye cikin shuɗiyar super ta ɗora labcoat akai, yayinda ta naɗe fuskarta da blue ɗin gyale wanda ya futo da doguwar fuskarta tayi fes! Ihman ta daɗe bata ga likitar da ta dace da likita irin Dr Amani ba, labcoat ɗin tafi yi mata kyau fiyre kowanne baƙin fatar likita da ta sani.
Ihman ta mayar mata da murmushi

"Me yake damun ki Ihman?"

Cikin nutsuwa tace

"Naci maiƙo ne a wajen dinner, shine yake ta damuna"

"Kina da ulcer ne?"

"Eh amma ba me yawa bace"

"yanzu ya kike ji?"

"I'm fine yanzu! Jikina ne kawai ba kwari sai slight headache"..

Dr Amani tayi rubutu ta kammala sannan ta sake ɗagowa ta kalli Ihman tace

"Bara mu jarraba waɗannan magungunan for 5days mu gani. Akwai allura ta jijiya omeprazole guda ɗaya  wadda za'a yi miki yanzu,sai kuma drugs guda huɗu! Dafatan ba kya tsoron allura"

Ihman ta girgiza kai tana murmushi sannan tace

"nagode"

Ta miƙe a nutse tana shirin ɗaukar file ɗin Faris ya riga ta, Adda Wasila daman tunda ta ga Faris ya kankane komai ta samu waje a reception tayi zamanta suna hira da Kamal. Sarauniya Falmata ƙin shigowa tayi ta zauna a mota tana hura hanci kamar za ta fashe.
Ihman waje ta samu ta zauna a gefen Adda Wasila, Faris ya tafi pharmacy ya siyo magungunan ya dawo, tare da Nurse ɗin da zata yi alluran, a qalla an huda Ihman sau biyar ba'a samu vein ba! Sai sannu suke ake mata idanunta a kulle tana yi wa Faris Allah ya isa. Ganin zata sake huda mata hannu Faris ya runtse idanu ya buɗe ya soma yi mata masifa

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now