💔WACECE NI???💔 part2 page Twenty-eight BY CUTYFANTASIA

73 8 1
                                    

Lokacin da Sadik yayi breaking news din ga su Adda Wasila kowacce rasa tunaninta tayi for some seconds, wani shock ne ya ziyarce su, biyo bayansa kuma wani matsanancin mamaki da farin cikin da ba zasu iya misaltawa ba. Nan da nan murna ta kacame a cikin gidan aka soma celebration kamar ranar ne bikin. Dakyar Ihman ta samu kanta ta shige daki ta kulle, kawai sai ta tafi sujudush shukur tana fashewa da kukan da zata iya cewa it's the first time tayi genuine kukan farin ciki a rayuwarta.
Bata taba tunanin cewa abubuwa zasu iya juyawa su koma haka ba, bata taba zaton watarana zasu iya kasancewa tare da Faris ba. She has always prayed for him to be in her life! Tun tana yi da hope har guiwarta ta karye, har ta saddakar cewa they were not meant to be watakila shi din ba alkhairi bane a cikin rayuwarta. Duk yanda zata yi, duk kokarin da zata yi tayi akan ta mance Faris amma kullum kamar sabunta mata shi ake yi a cikin zuciyarta, kamar kara ruruta mata soyayyar shi ake yi. Ta kan gaza gane me hakan yake nufi domin kullum addu'a take yi akan idan alkhairi ne Faris a gare ta Allah ya mallaka mata shi, idan kuma ba alkhairi bane Allah ya cire mata shi daga cikin zuciyarta ta manta da shi da soyayyar shi. Tayi yakini tayi ihmani Allah yana jin ta kuma ya amsa mata domin a wannan lokacin suluthainin daren da take tashi ta fuskance Shi, Yayi alkwari babu bawan da zai yi roko a wannan lokacin bai amsa mi shi ba. Shiyasa take zama confused wani lokacin, take jin kamar zata yi hauka ashe lokacin da Allah ya dibarwa abun ne bai cika ba domin shi alkawarinsa ba ya tashi. Yana ji yana gani yana sane kuma ba zai taba tozartar da bawan da ya dogara da shi ba. "THIS IS THE POWER AND MIRACLE OF PRAYER AND TRUSTING THE LORD OF THE HEAVEN AND EARTH"

Wanka tayi tare da alwala ta futo ta shirya sannan ta hau nafilar godiya ga Allah, tsayin mintina talatin din da ta dauka tana sallah wayarta ruri take yi don ma ringtone din ba mai karfi bane da ya hana ta ibadar. Sai da ta idar ta shafa ta ninke kayan sallar sannan ta dauko wayar cikin jakar da ta futa da ita ta duba, The newest ango in town ne Salmanun Faris!
Tana kallo wayar tana ringing amma sam sai taji ta kasa samun kwarin guiwar dauka, toh tace masa me? She feels soo awkward and anxious, she feels so new and changed! Sai kawai tabi lafiyar gadonta ta lulluba da tattausan duvet ta kulle idanunta.....
Cikin ikon Allah kuwa sai bacci yayi gaba da ita.

Washegari ta farka ne ta ji ta cikin sabuwar duniya, sabuwar rayuwa, sabuwar rana mai cike da dimbin tarihi a gare ta. Duk da cewa tayi matukar kokarin kamewa don kada aga zaqewarta da yawa, tana futowa breakfast yan'uwanta suka soma yi mata ihu da guda, sai ta ruga da gudu ta koma daki.
Sai dakin Adda Wasila ta biyo ta da shi tana rarrashi playing the big sister role cikin farin ciki.
Ihman ta amsa waya daga yan'uwa a ranar har ta gaji, musamman mutanen Ghana, musamman Uncle da Aunt Halima. Shi Faris din duk kokarinsa bai samu yin magana da Ihman ba sai bayan sallar isha'i. Tana daki Adda Wasila ta shigo ta saka mata wayar a kunne ta juya ta futa, ba tare da sanin wanene ba tayi sallama, sai taji maganar shi cikin karsashi ba zato yana cewa

"Are we still fighting Ihman?"

Tayi shiru tana murmushi

"Ihman!"

"Na'am!"

"Ko gaisuwa ma babu?"

Ta gaishe sa a sanyaye sannan ya soma tambayar ta mutanen gida da harkokin kasuwancinta, daga nan har ta warware suka shiga hirar da yake so suyi.

"Soo kinga yanda abubuwa suka chanja ko? Kinga tasirin addu'a Ihman? Gaskiya zan iya bugar kirji nace duk duniya a yanzu da bani da iyaye babu wanda ya kai darajar Hashim a idona domin iyaye ne kawai suke rufe idanu su yi irin wannan sadaukarwar ta abinda suka fi so ga yayansu. Ya bani kyautar da wani mahaluki bai taba bani irinta ba kuma ya saka ni cikin farin cikin da ban taba tsintar kaina a ciki ba.
Zan ci gaba yi mi shi addu'a har qarshen rayuwata akan Allah yayi ta aiko mi shi da farin ciki da jindadi da kwanciyar hankali irin wanda ya sanya ni ciki."

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now