💔WACECE NI???💔 part2 page thirty-two by CUTYFANTASIA

55 6 0
                                    

Ihman dai kuka kawai take yi yana shashsheka kamar ranta zai futa yayinda hankalin Faris yayi azabar tashi.

"Ihman abinda nake tsoro nake gudu kenan shiyasa tun farko ban yi miki maganar Falmata ba. Ni ban taba cewa ina sonta ba, ban kuma yi wani abu wanda zai nuna mata hakan ba, ita kadai take kidanta take rawarta. Bazan iya wulakanta Falmata ba saboda darajar mahaifinta a idona amma shi da kansa ya tuntubeni akan maganar ta nace masa babu komai a tsakanin mu sai yan'uwantaka. Kuma wallahi na rufe idona na gaya mi shi hakane saboda kwanciyar hankalin ki. A dalilin hakan baki ga yanda ransa ya baci dani ba har ma ya daina daukar wayata, dakyar na shawo kansa muke gaisawa.
Right now wani ne yazo yana sonta ake lallabata ta yarda ta aure shi, ita jan lokacin da take yi tana tunanin zan iya chanja ra'ayina ne ko kuma idan naga aurenmu ya kwana biyu na amince kuma na gaya mata gaskiyar cewa bazan yaudareta ba sannan ita mace ce lokacinta a qayyade yake kada tayi wasa da damarta. Dakyar dai muka shawo kanta ta amince aka kawo kudin auren aka sa rana, Ihman ba son Falmata nake ba kuma bazan iya son wata yanda nake sonki ba, ban yi miki alkawarin bazan taba yin aure ba saboda bansan qaddarataba amma nayi miki alkawari ba zan daina son ki ba komai juyin zamani.
Believe me Ihman, ni din masoyinki ne ma gaskiya kuma mai fatan ganin farin cikinki a koda yaushe.
Falmata yar'uwata ce, kuma mahaifinta ya taimakeni ba zan iya wulakantata ba, bazan iya yanke alakarmu saboda ke ba, kiyi hakuri don Allah!! Kiyi hakuri da boye miki komai da nayi, banyi hakan da niyyar munafuntarki ba sai don gudun bacin ran ki...."

Bai gushe yana magiya da ban baki ba sai da Ihman ta sauko har tayi danasanin abinda tayi masa duk da cewa tayi hakurin tayi mi shi kawaicin kawai ya kureta ne kuma kishi ya turnike ta.

"I'm sorry too! Nima bazan sake ba insha Allah"

Cikin murmushi yace

"Promise me maganar haihuwa ta wannan sigar ba zata sake hadamu ba domin bana so Ihman"

"I promise"

"Are we friends again?"

"Yes! Friends forever"

"I love you Ihman........
More than I could ever explain, and i will live to prove that"

Wai sai lokacin Ihman ta tuna a gaban su waye suke ta dago da sauri tana kallon kujerar Uncle, sai taga wayam, daga shi har Aunty Haliman sun zargawa karen su igiya. Toh me zasu zauna suyi bayan suna ganin masoyan sun manta da wanzuwarsu a falon? Girgiza kai Uncle yayi ya mike ya fuce yana murmushi yayinda Aunt Halima ta shige dakinta cikin sha'awar soyayyar su tare da yi musu fatan zaman lafiya mai dorewa da zuri'a mai albarka.
Ganin sun tafka abun kunya ya sanya suka silala suka bar gidan zuwa gidansu suna yi wa kansu dariya, Ihman har da kwaikwayon yanda Faris yayi yana magiya kamar wasu shashashai suka dinga tuntsira dariya daga nan suka manta da abinda ya faru.
Washegari suka yi sallama da kowa cikin kewa suka dau hanyar Airport, Ihman sai kunyar Uncle take ji shikuwa yayi kamar bai ma san abinda ya faru ba, daga nan ta saki jikinta suka ci gaba da hira har jirginsu ya iso.

"Uncle i will miss you! Kuma don Allah ana yin haihuwa nice zan fara ji, kuma idan yar mace ce sunana za'a saka don Allah"

Tana fadar haka ta juya da gudu gudu ta wuce ciki tana dariya. Uncle cikin murmushin jin kunya ya kalli Faris yace

"Matarka ta mayar dani kakanta Faris"

Shina murmushi yayi yana sosa keya.

Daga nan sukai sallama suka rabu.

Dawowarsu Kano da kwanaki uku Dr.Amani ta haihu, yaranta yan maza guda biyu masu kama da Uncle! Wai zo kaga kurma cikin wannan estate! Maigoro family sun gigice a wannan rana, sunyi murna sun yi tsalle sun yi farin ciki da godiya ga Allah! Ihman batai kasa a guiwa ba ta sake saka daru sai da ta juya Ghana. Sai dai daga can zasu wuce Egypt da Faris ba zasu dawo Nigeria ba, Abba yayi mata alkawarin su Inna zasu zo taron suna da yardar Allah.
Da yake CS akai mata har suka isa suna asibiti, ko zama basu yi ba suna ajiye kayan su suka shiga motar Uncle Aminu suka wuce asibitin cikin zumudi. Lokacin da ta isa dakin maijegon tsayawa kawai tayi tana kallon ikon Allah, ga Dr Amani zaune tana shan tea har ta wartsake, ga hajiyar Ghana dauke da Hassan, Aunt Halima dauke da Husani Uncle yana gefe yana amsa waya. Sai wasu daga cikin Aunties din ta da ke estate din. Cikin taruwar hawaye ta isa gaban Uncle ta rungume shi tana cewa

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now