WACECE NI??? Part2 page Twenty-five BY CUTYFANTASIA

118 14 6
                                    

Ihman ta shiga wani irin yanayi na tashin hankali da nadama wadda bata da amfani duk da cewa itama tana da tata hujjar ta ƙin sauraron shi. Akwai wani abu da mutum yake kasa ganewa sai a ƙurarren lokacin da ba zai iya yin komai a kai ba. Sai kuma ya shiga damuwar da ta ninka wadda ya shiga a lokacin da matsalar ma ta faru.
(Ita rayuwa ƴar masalaha ce da haƙuri da juriya, idan har ba zaka yi waɗannan abubuwan ba toh tabbas zaka yi ta shiga cikin yanayin baƙin ciki da damuwa wanda ba mai iya futar da kai sai Allah! A duk lokacin da mutum yayi maka laifi, kuma ya yarda ya amsa laifinsa, ya roƙi ka bashi damar yi maka bayani akan abinda ya faru, kayi ƙoƙari ka bashi wannan damar domin ta haka ne zaku fahimci juna, kaji abubuwan da baka sani ba ka gane abubuwan da kayi wa saɓanin fahimta. Wannan zai baka peace of mind da kwanciyar hankali ko da kuwa ka ɗauki matakin rabuwa da mutum ne ba zaka yi kana kokonto ko tunanin ya akai yayi maka abubuwan da yayi maka ba, ko yanda matsalar ta faru.
Ba lallai ne kaci gaba da mu'amala da wanda ya ɓata maka ba, amma abu ne mai kyau ka saurari uzurinsa ka yafe masa ba wai don ya cancanta ba, sai don ka samu nutsuwa da kwanciyar hankalin cigaba da gudanar da rayuwarka cikin aminci.)

Ganin halin da Ihman ta shiga ya sanya Hamma jin tausayinta sosai sannan ya shiga yi mata nasiha mai ratsa jiki yana bayyanata mata tasirin ƙaddara da yanda Allah yake ikonsa akan bayinsa. Ya bata ƙwarin guiwar cewa tunda abubuwan suka juya suka koma haka toh wataƙila dama can Allah bai ƙaddara akwai aure a tsananin ta Faris ba domin sau da yawa mukan so wani abu amma ba alkhairi ne a gare mu ba, sau da yawa kuma muka ƙi abu amma shine mafi alkhairi a tare da mu. Ya ƙara da cewa

"Ihman shi rabo da kike gani, wani abu ne mai matuƙar ƙarfi! Komai nisan da yake tsakaninka da rabonka sai ya taso yazo har inda kake. Babu wani mahaluƙi da ya isa ya hana rabon mutum ƙarasowa zuwa gare shi sai dai idan tun can daman Allah bai ƙaddara na shi bane. Idan kuma abu ba rabonka bane, ko yazo tsakanin leɓɓenka guda biyu sai ya futa. Don haka Ihman ki kwantar da hankalin ki, ki ɗauka cewa Faris ba mijinki bane kiyi fatan hakan ya kasance alkhairi a gare ki.
Ki daina kiransa a waya, ki rubuta masa text guda ɗaya ki bashi haƙuri kiyi masa fatan alkhairi kice kina yi masa sallama. Daga wannan kiyi blocking ɗinsa gabaɗaya on all platforms, ki bar komai a hannun Allah ki shiga sabgar ki kinji ƙanwata? I promise you Insha Allahu you will be happy!"

This is the most soothing words da Ihman ta saurara for a very long time kuma yayi tasiri sosai a zuciyarta ya saka mata nutsuwa da kwanciyar hankali. Sai gashi ta warware sun shiga wata hirar har ma suka ƙarasa bristol suka ci abinci duk da kashedin Aunty sai da taci dessert masu daɗi ta more. Daga nan ya kai ta gida ya wuce wajen harkokinsa, Ihman tana shiga ɗakinta ta warware lafayan jikinta ta sauya zuwa gown ɗin atamfa tayi alwala tayi sallar magriba sannan ta ɗauki wayanta ta zauna tana cracking brain ɗinta akan kalaman da ya kamata ta shiryawa Faris wanda idan ya karanta ba zasu taɓa barin kwakwalwa da zuciyar shi ba. Sai da aka yi sallar isha'i tana zaune a wajen ta rubuta ta goge, har tayi deciding wanda ta rubuta a ƙarshe kamar haka

"Assalam! Barka da duk lokacin da ka amince ka buɗe wannan wasiƙa ka karanta, dafatan kana lafiya.
Duk yanda zan bayyana damuwar halin da na shiga a dalilin jin rasuwar Inna ba zaka yarda ba amma dai ina daɗa yi maka ta'aziyya Allah yayi mata rahama ya sa bakin wahalarta kenan!
Ban manta da Inna ba Allah yana kallona, Bana son magana da kai ne saboda tsoron da nake ji da kuma tunanin abunda ya faru baya Faris! kaji mun wani mugun rauni a zuciyata wanda nake tsoron idan na sake baka dama zaka fama mun shi wataƙila wannan karon yayi mun ciwon da yafi lokacin ma da naji shi...........
Ba dogon surutu ba, I'm writing to you for the last time insha Allah, a duk lokacin da ka buɗe wannan saƙon nayi nisa da barin rayuwarka na karɓi ƙaddarata da hannu bibiyu da fatan hakan ya zama alkhairi a gare mu bakiɗaya.
Ina baka haƙuri akan duk laifukan da nayi maka kuma ina yi maka fatan alkhairi har ƙarshen rayuwarka!
Ihman!"

Bayan ta tura kuma ta tabbatar yaje, sai tayi blocking number Faris, ba cikin call log ɗinta kaɗai ba, sai da tabi duk wani social media site da suke communicating ta datse shi. Ta ajiye ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya, a wannan lokacin ta tattaro Faris da duk abinda ya shafe shi ta samu wani loko cikin ma'adanar zuciyarta ta jefa shi ciki. Ta amince he is her past and he was never meant to be hers don haka ta haƙura da ɓata hawaye da lokacinta akan abinda ba zata samu ba, ta amince da wannan zaɓin da Allah yayi mata kuma tayi alƙawarin da ba zata sake bari wani ko wata su ga damuwa akan fuskarta ba.
Daga wannan lokacin ta ware aka shiga sha'ani da ita, dalilin da ya sake armasa lamarin sosai. Saura sati biyu biki Farida ta sauka, Adda Wasila satinta ɗaya a Kano tana zirga zirga tare da zainab da Mami, rabon duty ɗin da suka yi baiyu ba kawai haɗe kai suka yi gabaɗaya suna team work. Larabar da ta kasance saura sati biyu dai dai biki Ihman ta samu kira daga Office akan wasu lissafi da suka sarƙe da gajiya da tayi da ƙarar ɗaya daga cikin staff ɗinta Rita wadda take wa cusmtomers rashin mutunci kala  kala. Tana shiryawa tana mitar wahalar da suke bata, wato babu abinda yake da sauƙi a rayuwa, daga aikin har kasuwancin kowanne da nashi ƙalubalen, wani lokacin ma sai kaji kamar ka tattara komai ka ajiye ka koma bin lafiyar gado kana bacci.

Cikin wani maroccon fabric ta shirya coffee colour wanda aka yi wa ƙwararren ɗinkin hannu ɗan zaria, stright skirt da half dress dai dai jikinta. Ta kawo ɗankwalin da aka yi mata turban ta saka sannan tayi amfani da barimar gold a kunnenta wadda ta haske fatarta. Ta kawo gyale milk kalar zaren ɗinkin kenan ta yafa sannan ta fesa turare kaɗan ta tattara ƴan tarkacen buƙatarta cikin chanel handbag ta futo tana ta sauri. A ɗaki ta samu Inna tayi mata sallama ta wuce hanyar exit door ta kitchen tana fatan kada su haɗu da Adda Wasila ta hanata futa, wai ta saka musu doka daga nan har biki ba zasu ga rana ba. Duk wasu shirye shirye su faɗa da baki za'a yi musu. A kitchen suka ci karo da Aunty itama zata futa.

"Kai kai! Ihman zaki gamu da Wasila wallahi, ina kuma zaki je kika ci wannan ado kamar yau ne biki?"

Cikin marairaicewa Ihman take wa Aunty alamar tayi a hankali kada Adda Wasilan ta ji don tana ɗakin Asma'u da mai gyaran jiki suna lissafi.
Cikin raɗa tace

"Don Allah Aunty ki rufa mun asiri kar ta ji, wani case zan je na kashe a office na dawo! Wlh daga nan ba zan biya ko'ina ba"

Aunty tayi murmushi tace

"toh Ita kwalliyar fa? Ina laifin ki saka abaya ko hijab?"

"Aunty it's too late for all this don Allah ki barni na tafi"

"Toh ince kuwa kinci abinda na dafa na ajiye muku a oven?"

Ihman ta girgiza kai cikin ƙaguwa

Aunty tace

"Ashe kuwa ba tafiya, ai na gaya muku babu zama da yunwa, kuma na chanja muku diet plan da kaina, duk abinda zaku ci wanda zai ƙara muku glowing da lafiya ne ba teɓa da ƙaton ciki ba, kuma ban yarda a zauna da yunwa ba"

Tana maganar tana futo da abincin daga oven cikin madaidaitan warmers masu kyau. Da kanta tayi serving Ihman wani faten dankalin turawa da yasha vegetables da kifi kamar kunnenta zai gutsire. Tuni ta manta sauri take yi ta sharɓi kayan arziki ta ƙoshi sannan tasha ruwa tana hamdala

"kuma Aunty kin samu ladana don wlh yunwa nake ji, saurin da nake ne ya hanani neman abincin"

Aunty  ta kwaɗa mata harara tana maida filasanta inda ta ɗauko, Ihman tayi dariya ta wuce tana yi mata sai ta dawo. Wannan Auntyn wata new sweet and caring Aunty ce mai kyautatawa da kulawa ga kowa da duk ƙarfinta. Wannan ya bata damar samun wajen zama a zukatan iyalan gidan har da Abba, domin ance ita zuciya tana son mai kyautata mata kuma tana ƙin mai ƙuntata mata.

Cikin nutsuwa take driving har ta isa shopping mall ɗinta wadda duk lokacin da ta shigo tayi parking ta kalli wajen da cikowar da ake masa sai zauna tayi godiya ga Allah ta musamman kafin ta buɗe motar ta futa. A gaggauce take amsa gaisuwar staff ɗin ta wuce office ɗinta wanda kullum ake sharewa a goge. Ta aje jakarta ta kunna socket ɗin burner ta zuba sandal akan kaskon wani lallausan qamshi ya soma tashi sannan ta wuce ta kunna mini fridge ɗinta kafin ta zauna akan kujerarta mai juyawa tana bismillah.
Tana kiciniyar kunna laptop ɗin da ke kan table  manager ta shigo tana yi mata sannu da zuwa, ta amsa cikin kulawa sannan manager tace

"kina da guest Hajiya!"

Ihman tana ji ta san Sadik ne don tana hanya ya kira ta yace zasu yi magana ta gaya mi shi tana hanyar office yace toh zai biyo. Don haka ta bata izinin cewa ya shigo ta kuma ɗaura da cewa

"ki haɗa staff ɗin gabaɗaya da duka records ɗin kafin na futo, a kulle mall ɗin and call it a day, customers da suka riga suke ciki a barsu su gama sannan a tashi saboda ina son ganin kowa"

Ta amsa da

"yes ma"

Sannan ta futa.

Ba daɗewa aka murɗa ƙofa tare da sallama, ji tayi kanta ya wani sara, domin cira idanun da zata yi Faris ta gani a tsaye jikin ƙofa yana wannan munafikin murmushin na shi mai karya lagon ɗan adam, ƙamshin sa ya karaɗe ko'ina a cikin office ɗin. For the first time taji kamar ta miƙe ta shaƙe shi ya mutu ta huta da wannan Jarabar.

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now