WACECE NI??? Part2 page Twenty-four BY CUTYFANTASIA

111 10 1
                                    

A sanƙame ya bar Ihman tsaye cikin wani irin yanayi na tsantsar nadama da danasani. Shin me yasa tayi haka? Me yasa taƙi sauraron Faris ko da sau ɗaya ne ya kare kansa ko da kuwa ba zata gamsu da abinda ya gaya mata ba? Me yasa ta kasa tambayar shi mahaifiyar shi bayan ta san zafin ciwon da ta shiga ne ya ɗauke shi zuwa ƙasar Egypt da ita wanda daga nan ne bata sake jin ɗuriyar shi ba? Me yasa tayi mi shi haka? Shin wacce irin soyayya ce mahaifiyar Faris da shi basu nuna mata ba? Me yasa ta rufe idanunta ga duk alkhairan shi gare ta take kallon laifin da yayi mata ƙwaya ɗaya? Anya kuwa tayi adalci anan??

Ji tayi Adda Asma'u ta dafa kafaɗarta cikin sanyin jiki tace

"you have hurt him alot Ihman! Gaskiya baki kyauta ba"

Sai taji wasu hawaye masu zafi suna sakko mata, wai sai yaushe za'a gane cewa tsabar soyayyar da take yi wa Faris ce tayi silar wannan mugun fushin da ta ɗauka da shi? ya za'ai ta kwatantawa musu irin ciwo da azabar da rashin sa ya sanya ta a ciki? Ya za'ai ta iya bayyana matsayin da ta bashi da kuma dauriyar da take yi wajen shanye komai kamar ba komai ba? Su suna tunanin it's easy mance abinda zuciya ta saba da shi?............
Cikin rangaji ta wuce gidan Uncle ta shiga ɗaki ta soma kukan da bata san ranar da zata daina irin shi ba. Washegari tana tashi wayar shi ta soma kira, sai da tayi ringing ta katse sau uku bai ɗaga ba, tun tana sa ran zai biyo ta har ta fidda tsammani ta kuma tabbatar cewa yanzu Faris ya soma na shi fushin da ita wanda take jin shi kamar zuban ruwan dalma a cikin zuciyarta. Hakanan suka tattaro suka dawo Nigeria yanayinta ba daɗi, suna dawowa kuma suka shirya suka wuce Dubai domin shopping ɗin aure wanda ya ɗauke su sati uku sannan suka wuce umrah suka yi addu'a kafin su dawo.
Tsayin wannan lokaci babu rana ta Allah da Ihman ba zata kira Faris ba amma ko sau ɗaya bai ɗauka ba. Kullum yana yin post a WhatsApp kuma ita ke fara buɗewa tayi mi shi sallama amma bai taɓa dawo mata da reply ba. Ko buɗewa baya yi, a wannan lokacin ne kuma ta dinga tuna sanda yake aiko mata da messages ashirin a rana sai dai ta goge su tas ba tare da ta karanta ba. Sai taji kamar ta shaƙe kanta ta huta, toh meyasa ta goge? Waya san me ya rubuta? Wataƙila da bata goge ba da yanzu ta samu abinda zata karanta ta dogara da shi wajen rarrashin Faris ya saurareta.
......................................................................................
Lokaci yana tafiya rayuwa tana juyawa shikuma bahaushe yace rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya. Cikin ikon Allah duk wani shirye shirye from all angle ya kammala, biki saura sati uku har an bugo invitation cards. Duk wani mai ruwa da tsaki cikin taron ya zama busy, musamman irinsu Adda Wasila, Mami da Zainab, ita Farida sai ana saura sati ɗaya zata sauka.
Yinin ranar yau Ihman a ɗaki tayi shi cikin zazzaɓi domin muguwar damuwar da ta sanyawa ranta. Tun ana rarrashinta har Inna ta gaji tayi biris da ita tace kowa ya ƙyaleta yaci gaba da harkar gabansa. Tana cikin tattausan duvet taji ringing ɗin wayarta, ta laluba gefenta ta ciro tana kallon screen ɗin. Hamma ne, don haka tayi swiping a hankali ta kara a kunnenta.

"Hamma ina yini?"

"Ihman jikin ne? Me yake damun ki yanzu? Are you sure kawai zazzaɓi ne? Ki gaya mun me yake damunki?"

Sai taji zuciyarta ta karye, har yanzu Hamma ne kawai yake gano damuwarta komai ɓoyewar da zata yi, yafi kowa tausasawa a gareta da tsananta son jin damuwarta da kuma tabbatar da cewa ya kawo mata masalaha akan kowanne irin lamari.

"kinga ki shirya yanzu ki same ni a mota! Minti goma ina jiranki"

Ta amsa da toh sannan ta yaye bargon ta sauko daga gadon ta shiga toilet ta watsa ruwa. Cikin mintina goma ta shirya Into soft laffaya lace wadda ta ɗauru sosai a jikinta ta kwanta a lafiyar farar fatarta wadda take ta shan gyaran amare. Inna ta gayawa cewa zasu futa da Hamma sannan ta wuce ƙofar gida cikin sanyin jiki. Tana shiga motar ya tayar suka bar gidan ba tare da yace mata komai ba bayan gaisuwar da ya amsa mata. Sai da suka yi nisa sosai sannan ya gangara gefen titi yayi parking mai kyau.
A nutse ya soma yi mata magana da tausasawa

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now