WACECE NI??? Part2 chapter Five BY CUTYFANTASIA

157 17 1
                                    

Sadik ya tako a hankali ya zauna daga can gefe kansa a sunkuye, shi kan shi tambayar kansa yake yi me yasa yake wadannan abubuwan? Me yasa yake wannan rayuwar? Me yasa ya koma haka?
Aunty tana ganin shigowar shi itama tazo ta nemi kujera ta zauna saboda kada Hamma ya kulla mata wani sharrin ko munafurcin akan danta. Abba ya kalleta yayi kwafa kawai sannan ya maida hankalinsa ga Sadik!
Cikin kulawa da sanyin murya yace

"Sadik"

Bai dago ba amma ya amsa

Ya sake kiran sunan sa.

"Sadik me yake damun ka? Mecece damuwar ka? Kaga yanda ka koma Sadik? Kaga yanayin da kake ciki? Sadik shaye shaye a gidan nan? Baka yi shaye shaye a turai ba sai da ka dawo gida a gabana zaka yi Sadik? Menene kake so wanda baka samu ba? Wanne gata ka rasa? Waye ya baka wannan shawara Sadik? Me yasa......."

Muryar Abba ta soma shaking kamar zai kuka.
Zuciyar Sadik ta sake karyewa yaji inama ya mutu ya huta da wannan halin da yake ciki. Kansa a kasa ya sake jin muryar Hamma yana mi shi magana cikin lallashi

"Sadik this time ba zamu hukunta ka ba, bamu kira ka don mu yi maka fada ba domin mu ma munyi sakaci akan halin da kake ciki, abinda muke so da kai Sadik shi ne ka sanar da mu dalilin da yasa ka zabar wa kan ka wannan rayuwa? Me kake so a duniyar nan da baka samu ba? Me......."

Kafin ya karasa suka ci muryar Sadik cikin raunin da basu taba ji ba

"Hamma Ihman! Ihman ce matsalata! Ka sani Hamma kai na fara gayawa cewa ina son Ihman kuma komai zai iya faruwa dani idan ban same ta ba! Hamma kai kace mun nayi hakuri bazaiyu ba! Kace nayi hakuri saboda idan nace ina sonta zata nemi jin asalinta kuma hakan barazana ne ga lafiyarta!
Hamma ka sani na hakura ne a fili amma wallhi a zuciyata kullum kara son Ihman nake yi! I've tried to be a man and mask up abinda nake ji amma na gaza!
Yau an wayi gari ba Ihman, ya zan yi Hamma? Ya zan yi da rayuwata?"

Sai kawai ya fashe da kuka mai cin rai! Idan akwai wanda zai ce ya taba ganin hawayen Sadik sunan shi maqaryaci! Don haka jikin su yayi masifar sanyi, yayinda wata irin juwa ta shiga hajijiya da Aunty kamar zata fadi daga zaunen! Ta yunkura zata yi magana Abba ya daga mata hannu

"Kina zaune anan ne saboda ke din mahaifiyar sa ce! Amma ikon magana baki da shi sai idan ni ne na baki dama! "

Balbalin bala'in da ta hango cikin idanun Abba ne suka rufe bakinta sai a zuci take ta faman feso kalaman ranta yana tafarfasa

"Sadik Ihman kake so?"

"Eh Abba ka taimaka mun!"

"Toh Sadik idan mutum yana son abu ba addu'a yake yi ba? Halin da ka jefa kan ka ne zai ba ka Ihman din?"

"Abba nayi addu'ar na gaji"

"Wa yake gajiya da addu'a Sadik?"

"Abba ka taimake ni! I'm lost! I'm defeated! Kaina ya kulle! Bansan me zan yi ba."

Hawaye suka cicciko idanun Abba ya maida su dakyar sannan yace

"Kayi mun alkawarin za ka daina shan komai Sadik, kaji tsoron Allah, ka daina abinda kake yi saboda girman zatin Allah ba don kowa ba! Ni kuma nayi maka alkawari zan nemo Ihman duk inda take, idan kuma har ta amince na yi maka alkawarin zan aura......"

Wata irin ashariya Aunty ta kunduma wadda Abba bai taba sanin ta iya ba, watakila da zaman su bai kawo haka ba! Ya daga ido ya kalle ta cikin wani irin yanayi, Hamma yayi sauri ya dafa shi yana cewa

"Abba ka kira sunan Allah, kar ka yanke hukunci cikin fushi don Allah! Don Allah kayi hakuri"

Cikin karaji ta kalli Hamma tace

"Yi mana shiru munafikin banza munafikin hofi! Duk ba tuggun ku bane! Uwarku taje ta dibga mai asiri saboda ta san yarta ba zata auru ba kai kuma kazo zaka mun surutun banza! Toh wallahi tallahi billahi in dai ni na haifi Sadik ba uwar wani ce ta haifar mun ba na tsine mi shi albarka idan ya auri Ihm....."

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now