WACECE NI??? Part2 chapter Ten BY CUTYFANTASIA

161 11 0
                                    

Tana kwance cikin kujerar jirgin, a rukuni mafi daraja wato first class, kunnenta sanye da earpiece wanda suratul ambiya'i take futowa cikin qira'ar Sheikh Abdullah Juhany tana sanyaya mata zuciyarta da ke cikin wani yanayi! Bikin Farida ne yazo mata daidai lokacin exams, ranar da suka kammala za'a daura auren, kuma a ranar ta taho, don haka babu abinda zata samu na shagalin bikin sai welcome dinner da iyayen mijin suka shirya ranar saturday idan an kai musu amarya Abuja! Don haka idan ran Ihman yayi dubu ya baci, tana ji tana gani sai dai a turo mata pictures din biki, duk wata rawar da zata taka Adda Asma'u ta amshe ta maye gurbin ta sai kawai ta kashe wayar gabadaya kowa ya huta sai da zata taso ta kunna ta sanar da su!

Sun sauka a Abuja cikin dare don haka a airport ta karasa kwanan da safe Abdurraheem yazo ya dauke ta zuwa gidansa! Ba zaiyu ta koma Gombe a ranar su juyo da amarya ba don haka kawai tayi zamanta! Sai ga wani mugun suprise da ya shammace ta bayan ta tashi daga bacci, su Amna da Aunt Halima tare da Hinaya wadda take gudunta ko'ina tana yan maganganun da ba'a rasa ba! Yarinyar ta rage kama da ita amma ta kara haske da qiba kamar wadda ake hurawa, anyi mata kwalliya mai ban sha'awa da gyaran gashi kamar ka sace ta ka gudu! Duk zumudin ganin Hinayan tayi ne a cikin zuciyarta bata bayyana fili ba, domin ta riga da ta damqa ragamarta gabadaya ga Aunt Halima!
Itama Aunt Haliman tsayawa tayi baki sake tana kallon yanda Ihman ta koma kamar balarabiya, ta qara tsayi da qiba kadan wadda ta mayar da ita wata irin classy lady! Ga wani aji da nutsuwa da suka saukar mata hade da wani gayu na musamman kamar ba itace wannan zulumbuwar Ihman din mara son wanka ba a wasu lokuta da suka shude wanda ba zata taba mantawa ba!
Gidan Abdurraheem make up artist din da tayi booking tazo ta same ta, already duka dinkunan ta matar Abdurraheem din ce ta kai kuma ta karbo mata tun ma kafin ta san ba zata ta samu zuwa bikin gabadaya ba!
Karfe hudu suka kammala shirin, ta futo cikin azabbaben HKG lace kalar burnt orange dinkin fitted gown daga "Hudayya House" dankwalin kayan ta daura sannan tayi parring da gold custume! Yanda kalar ta karbi fatarta kawai abun kallo ne! Wani abun armashi kuma bata bar kwalliyar haka terere ba ta kawo wadataccen mayafi light orange mai duhun texture ta yafa don haka ba zaka gane yanda kayan suka kamata ba sam! To say she is beautiful is an understatement duk inda ta wuce sai an kalleta an qara! Da su Aunt Haliman suka tafi wajen bukin inda suka samu Amarya radam cikin shigar amare sai kyalli take yi, Adda Wasila, Aunt Zainab da Adda Asma'u na ta shiga da futa da irin kayan jikin Ihman wanda suka dinka musamman saboda wannan ranar abun gwanin sha'awa!
Tana ganin yan'uwanta ta ruga wajensu suka rungume juna, shekara daya da wata uku ba wasa bane, tayi missing gida fiye da misali don ma babu Inna wadda tafi qishirwar gani fiye da kowa! Anyi biki an gama lafiya an mika amarya gidanta da ke sabuwar unguwa Global estate kafin su tattara su koma Turkey da mijinta sannan suka juya garin da suka fi wayo ranar monday!

Tun daga gate ta saki jaka ta ruga da gudu ta rungume Inna ta baya wadda ke tsaye a kitchen tana hidimar abincin saukar bakin, cikin murmushi da farin cikin ganin Ihman din ta juyo tana dariya!

"Wai ke yaushe zaki girma da wannan abun ne?"

"Inna nayi missing din ki"

Ta fada cikin sanyi.

"To ai gani, ba guduwa zan yi ba"

Adda Asma'u ta shigo tana cewa

"Inna inaga Zainab kawai ta hakura ta barwa Ihman matsayin auta mu huta"

Suka dinga dariya suna tsokanar Ihman din, gabadaya gidan nasu ya sauya ya koma me azabar dadi! Asma'u ta zama kamar dama can cikinsu ta taso, baka iya rarrabe ta cikin su Adda Wasila balle ka gane cewa ita ba yar Innan bace! Ashe daman Aunty ce matsalar gidan, tun da tayi nisa da su komai ya dawo normal! Abba yana shigowa ya dinga far'a da murnar zuwan Ihman, taje ta gaishe shi tare da tsarabar da ta kawo mi shi

And the rest of the days went by cikin armashi da farin ciki kamar kada su wuce! Da tayi niyyar zuwa Ghana, amma yanayin da take ciki cikin iyalin ya hanata darawa ko'ina har ta cinye hutun ta gabadaya! Kullum Inna cikin yi mata nasiha da bata shawara take, ta kula da kanta, ta kula da addininta, ta kare mutuncinta, sannan burin ta na karshe a kanta ta samu miji nagari tayi aure! Don haka duk inda Ihman ta shiga a rayuwa wannan hudubar ta Inna bata daina ringing cikin kwanyar ta! Tana kuma matukar kokarin ganin cewa tabi duk wadannan shawarwarin iya gwargwadon ikon ta.

A cikin shekararta ta biyu ne Allah ya hadata da Mudassir! Watarana kawai ta tashi tana sha'awar zuwa shopping, abinda bata cika yi ba, duk abubuwan da take bukata online take order a kawo mata. And she is the simple type, ba wasu tarkacen kayayyaki take bukata ba! Ta shirya cikin Armani jeans baki, da top nude colour wadda ta kawo mata har guiwa sannan ta nannade fuskarta da bakin gyale da ka ganta ka ga musulma cikakkiya sai dai ba lallai ka gane cewa ita din daga Nigeria ta futo ba. Ta sanya snickers din ta bakake ta kawo doguwar jacket nude colour ta dora a sabili da sanyin da ake tsugawa a garin! Har gida ta kira mota wadda ta dauke ta zuwa
"WESTFIELD FORUM DES HALLES"
Shopping tayi akan abinda ya danganci kayan sawa musamman saboda chanzawar yanayi, sai kayan shafa da tarkacen kayan gida wanda suka bata sha'awa! Ta kammala komai ta taho hannayenta duka biyu riki riki da kaya, kamar daga sama taji ance
"Akwai dako Hajiya?"
Ta juya cikin sauri saboda kalaman da taji irin na gida musamman a tashar dukku! Tozali tayi da Mudassir, dogon mutum wanda ke cikin middle shekarunsa, daga kallonsa ta gane bafulatani ne dan'uwanta kuma me kamala da far'a!
Murmushi tayi tace
"Ana bukatar dako a garin nan?"

"Gashi kuwa ni na futo nema"

Ya karasa maganar yana kokarin karbar kayan sai kawai ta sakar masa.

"Muje na raka ki wannan kayan ai sun miki nauyi!"

"Ba nauyi Allah"

"Gashi nan kina takawa dakyar kuwa"

Murmushi kawai tayi alamar rashin sabon magana da mutane musamman wadanda ba jinsin ta ba.
Sai da suka zo wajen mota ya zuba maka kayan gabadaya sannan suka tsaya suna kallon juna.

"Ladan dakona?"

"Nawa ne?"

Ta fada cikin murmushi domin ita dariya yake bata sosai

"Zaki biyani kin yi alkawari?"

Ba tare da wani tunani ba tace

"Ya za'ai na danne maka haqqinka?"

"Toh number ki zaki bani a matsayin ladan"

Ta bata fuska tana cewa

"A'a...."

"Kin yi alkawari"
Ya katse ta

"Toh ai kudi nayi tunanin zaka ce, amma number wayata ai tayi arha akan wannan dan aikin"

Yayi murmushi

"Duk wannan dakon na kare a kudi? Haba Hajiya! Ki cika alkawari kawai"

Ba'a son ranta ba ta karanto mi shi ya adana cikin wayar shi yana cewa

"Toh sunan fa?"

"Haba! Bayan arhar har da alakoro kuma? Abun ai sai yayi yawa"

Yayi dariya yana ja da baya

"I will earn that too! Take care"

Suka ja mota suka tafi tana mamakin wannan bawan Allah ta kuma yabawa sense of humor dinsa.
Toh wannan ne silar haduwarta da Mudassir wanda suka yi wani irin sabo cikin kwanaki sittin da bakwai din da suka biyo baya domin Mudassir ya iya sace zuciya cikin hikima da barkwanci. Ya gaya mata shi dan asalin Katagun ne ta jihar Bauchi kuma ma'aikacin tashar BBC a kasar Jamus kuma trainning ya kawo shi Paris na tsayin watanni hudu zai sannan ya koma Germany! Yana da mata guda daya da yara biyu, kuma yana ganinta zuciyar shi ta kissima mi shi lallai aure na biyu ya kamashi, because this kind of feeling cannot end just like that!
Ihman ta yaba da hankalin shi duk da cewa akwai wani ciwo da take kokarin dannewa kullum kwanan duniya, domin ita har zai ci gaba da ruruwa a zuciyarta, toh tabbas wani mutum ba zai samu gurbi a cikin zuciyarta ba!
Bata yi kasa a guiwa ba wajen sanar da Inna abinda yake faruwa, domin a halin yanzu bata da aminiyar da ta kai ta! Ta zubar da kowa ta kama Innan domin tana ganin this is the part of life she has missed, wato bond tsakanin ta da mahaifiyarta, yanzun da ta samu bata jin dadin kowacce alaka bayan ita. She does not need a friend at all, don haka ne ma duk shiahshigewar da su Hilwa suke mata bata iya basu fuska ba har suka gaji suka kyaleta da Genevieve din ta wadda ta dauka a matsayin mataimakiya wadda ta san ba za tayi wani tasiri a rayuwarta outside school and Paris ba.

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now