💔WACECE NI???💔part2 page Thirty by CUTYFANTASIA

60 9 1
                                    

Watanni hudu cif har da kwanaki uku bayan bikin Ihman aka kammala mata gyaran gidan da zasu zauna a kasar Egypt, kafin lokacin ta kammala duk wani shiri da zata yi, ta danka mall dinta a hannun trusted mutanen da ta tabbatar zasu kula mata da shi sannan ta mayar da Mami matar Sadik kujerarta tunda ita ba aiki take yi ba.
A satin da zata tafi Egypt taje Ghana tayi kwanaki biyu wanda suka bata damar sallama da Kowa musamman Hinaya domin zata yi mata nisan da bata san lokacin da zasu sake haduwa ba. Duk da haka she has never regretted her decision na baiwa Aunt Halima rikonta, tana samun soyayya da kulawar da tayi ihmanin ba zata samu a wajenta ba don haka kullum take kara godewa Allah take kuma godewa Aunt Halima. Tare da Uncle Sa'id suka taho Nigeria saboda shirin na shi auren da yake tayi wanda saura sati biyu, taso ta zauna sai anyi bikin Abba yace ko kwana daya ba zata kara mi shi gida ba idan an gama mata aikinta zata tafi Hamma ma ya goya mi shi baya da cewa
"Ihman ki dinga tunawa fa Uncle din nan don yana wasa da ke ba shi ne zai sa matsayin shi ya chanja a wajenki ba. Shi din ba yayan ki bane ko abokinki don haka bai zama dole sai dake za'ai bikin auren shi ba ko don ma ya samu sakewa yanda yake so! Get ready and leave don Allah"

"Hamma kaima korata kake yi?"

"Eh nima na gaji da ganin ki. Ki bar mana gida ki tafi naki"

Hangame baki tayi cikin mamaki yayinda Hamman ya mike yana saba hannun babbar riga

"Hamma ni din?"

"Ke din fa Ihman!"

Ya fuce abunsa yana murmushin karfin hali yayin da su Inna suka shiga yi mata dariya wadda ta tunzura Ihman ta shige daki tana kunkuni.

Rabar talata Jirginsu Ihman zai tashi, tun shadayan safe Aunty ta saka ta a gaba ta shirya cikin tattausan lace black me touch din lilac! Ta kawo sabuwar laffaya lace fara sol ta taimaka mata ta nannada sannan kuma Ihman ta soma hawaye, Aunty ta kama hannunta zuwa falon Abba yayi mata nasiha, amma kalaman shi na qarshe sai da suka ta fashewa da magigicin kuka.

"Na cika burina Ihman nayi miki aure zaki bar gidan nan cikin gata da mutunci zuwa hannun da muke da yakinin zai rike ki amana! Na godewa Allah da wannan alkhairi! Kiyi hakuri da zaman aure Ihman, kiyi hakuri amma idan kika ga hakurin zai cutar da ke kiyi maza ki sanar da ni halin da kike ciki, nayi miki alkawarin sai inda karfina ya kare, aure nayi miki ba siyar da ke nayi ba saboda haka duk lokacin da abubuwa suka cagule miki ki taho da gudu wajena zan baki kyakykyawar tarba da duk taimakon da kike bukata! Na yaba na gamsu da halayyarki kuma ina fatan ba zaki bani kunya a zaman auren ki ba! Ina yi miki fatan dukkan alkhairin da yake cikin rayuwar da zaki shiga ina nemar miki tsari daga sharrin dukkan abun ki"

Dakyar Aunty ta kamo ta suka wuce dakin Inna, cikin rauni Ihman ta durkusa a gaban gadon da Inna take zaune ta kwantar da kanta a kan cinyoyinta. Inna ta dafa kan Ihman ta soma yi mata addu'a da sa albarka wadanda suka motsa ran su Aunty kowa ya dinga share kwalla.
Ga wanda ya san rayuwar da suka yi a baya ya kuma gan su a yau, dole ya zub da hawaye! After series of crying, farewell and all aka saka Ihman cikin motar Hamma suka tafi airport, duk yan rakiya Abba ya tsaida su a gida yace ba amfanin tafiya Airport ana wani koke koke da rungume rungume kowa yayi sallama da ita daga gida.
Aunty,Aunty Aisha matar Kawu Bala da Adda Wasila ne zasu yi mata rakiya har kasar Egypt cikin jagorancin Sadik! Hamma ne ya kai su airport ya tsaya aka kammala komai, sai da zasu shiga ciki ne kuma shima yaji zuciyar shi ta karye

"Toh Ihman Allah ya bada sa'a! Ina yi miki fatan alkhairi, please always be yourself kada ki chanja daga yanda na san ki! Take very good of yourself kuma kada ki manta I'm always a call away a duk lokacin da kike bukatar wani abu ko menene shi! Allah yayi miki albarka"

Ya juya da sauri yana share hawayen da suka kufce masa cikin jarumtaka. Sai yau din nan ya tabbatar da cewa abinda yake ji game da Ihman is beyond explanation. Ya dade da fahimtar cewa yana sonta soyayya mai tsananin da shi bai taba sanin akwai irin ta ba, kuma ya fara jin hakan ne a sannu a hankali ba wai lokaci daya ba! Yayi kokarin boyewa yayi jarumtar dannewa kuma yayi nasarar cinye wannan jarrabawa akan Ihman!
Ya san cewa yafi kowa sonta amma da dai baya son ya nuna hakan saboda wasu dalilai
Na farko dai yana son ta sake da shi ta mayar da shi wani mutum da za ta dosa da kowacce  irin matsala karama ko babba idan ya nuna mata soyayya ba zai samu wannan ba.
Na biyu yana son tabbatarwa duniya cewa ba sai kana son mutum da aure bane kake tsayawa ka inganta rayuwarsa ka taimake shi ka ba shi duk wata kulawa da soyayya ba
Na uku baya son ya karya mata zuciya ta gane cewa shi din ba yayanta bane na jini kamar yanda take tsammani a lokacin ma bata kai ga sanin komai ba.
Bayan ta gane komai kuma yaji ba zai iya auren wadda Sadik ya haukace akai aka hana mishi ba
Na hudu yana son wannan alakar tasu da ya gina ta dore har karshen rayuwarsu as brother and sister as protector and guidance for her
Na karshe yana son ta auri wanda take so ta amincewa ya amince da ita yanda take ba wai wanda zai aure ta don rufa mata asiri akan abinda ya faru da ita ko wani dalili mai alaka da haka ba.

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now