WACECE NI??? Part2 Chapter Fourteen BY CURYFANTASIA

209 17 8
                                    

Inna ce ta shigo dakin Hinaya wadda ta futo daga wanka tana shirin tafiya office, ta nemi bakin gado ta zauna tana fuskantar Inna cikin nutsuwa.

"Ihman magana zamu yi"

Ta sake maida hankalinta ga Innan tace

"Inna me ya faru?"

Cikin damuwa Inna ta soma magana

"Ihman kina ganin tafiyar nan da zaki yi a karo na biyu shi ne daidai? Haka zaki sake barin gida shekaru wajen hudu?"

Ihman ta kalli Inna a tsanake cikin ladabi tace

"Inna idan ban yi karatu yanzu da nake da opportunity da support da lokaci ba sai yaushe? Kina kallon yanda rayuwar tawa take tafiya babu babu wanda zai ji labarina bai juya mun baya ba! Ba wai nace ba zan yi aure bane amma Inna lokacin ne bai yi ba, idan yazo Allah yafi mu sanin yanda zai shirya komai! Nayi addu'a mai yawa Inna kuma na san cewa Allah ba zai tozarta ni ba! Amma jiran lokaci ba nawa bane, wannnan damar ita kadai nake da ita watarana karatun ne kawai gatana"

Jikin Inna yayi matukar sanyi, duk makaman da ta shigo da su dakin sai  ta zubar da su, a maimakon hana Ihman tafiya sai ta tsinci kanta tana bata kwarin guiwa da addu'ar nasara da fatan alkhairi sannan ta mike ta futa! Ihman ta maida kofar ta kulle kawai ta fada gado ta soma kuka, sai da tayi me isar ta sannan ta daga hannu sama ta dinga kwarorowa Allah kirari tana neman daukin sa da agajinsa na gaggawa!
Ta koma toilet ta wanke fuskarta tayo alwala ta dawo daki tayi sallar la'asar sannan tayi shafa ta saka kwalli don ta boye kodewar da idanunta suka yi, ta saka liner har da mascara sannan ta shirya cikin embellished holland wax mai ash da silver(light ash) wadda aka tsarawa eight pieces skirt and fitted blouse aka kuma bi design din da "Swarovski" stones qanana kamar tare suka zo da atamfar! Tayi daurin gaban goshi bayan ta tattare gashinta a keya ta nade a band! Da siraran fashion tayi amfani a kunne da wuyanta, tsintsiyar hannunta kuwa ruwan sarkar agogon "Cartier" ne da round ring a yatsan hannun! Ta kawo gyale fari ta dora a kafada bayan ta fesshi jikinta da sassanyan turaren "Davidoff cool water" ta dauko handbag dinta ta da zuba duk abubuwan amfaninta a ciki, sannan ta ta zura Armani slippers ta futo looking like a bag of diamond saboda kyau da class!
Bayan tayi sallama da Inna ta shiga motar ta zuwa Mall tana bin karatun alqur'ani daga bakin "Abba Zaria" cikin suratul Furqan a hankali tana jin saukin damuwar da take ciki.

Karfe hudu ne da rabi na yamma, motoci ta samu dankare cikin harabar mall din ta lumshe idanu tana godewa Allah bisa daukakar da yayi wa wannan waje, tunda aka bude shi mutane suke tururuwa, sam ba sa hadani da mugun tsadar kayan kunsan garin Kano ko da me kazo an fika, gashi cikin GRA, ga buiding din da finishing one of a kind! Everything is just breathtaking and mindblowing! Sai hamdala!
Bayan tayi parking ta dauko jakarta ta futo tana takawa a hankali, ko kadan bata bari mallakar wannan wajen ya saka ta jin ita wata tsiya bace balle ta daga kai! Tana shiga hankalin ma'aikatan ya dawo kanta suka soma kai gaisuwa, tana amsawa cikin far'a da saukin kai kamar dai itama siyayyar ta shigo yi, duk customer din da ta gani sai ta musu sannu kafin ta wuce office din ta ta shige ciki.

Ac ta kunna da burner din turare, ta dauko kwalbar sandal asl ta bude ta zuba akan burner din, wani tattausan qamshi da sanyin kwandisha suka gauraye office din, ta sake dauko room freshner din "Aqua" ta fesa sannan ta zagaya ta zauna akan kujerarta tana maida numfashi! Daga bisani ta kunna laptop ta soma aikin da take yi, mintina arba'in da zamanta daya daga cikin staff din ta kwankwasa mata kofa, ta amsa tare da bada izinin shigowa. Rose ta risina tace

"Madam you have a visitor (Madam kina da bako)"

Ba tare da ta dago ba tace

"Male or female?(mace ko namiji?)"

Tace

"Namiji ne"

"Waye shi?"

"Yace kawai nace miki kina da bako"

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now