WACECE NI??? Chapter EIGHT BY CUTYFANTASIA

143 11 0
                                    

Kwanakinta goma da dawowa matar Hamma ta haiwu, baby girl me kama da shi sak qatuwar gaske! Murna da suka yi ba zata misaltu ba, iyayen Zainab sun so tafiya da ita gida tayi wanka Inna ta kekasa kasa tace babu inda zata, ita zata kula da ita da yar jikallenta. Wannan baby ta ragewa Ihman missing din Hinaya, ita ta zage tana raino, ta goya ta sauke ta hada madara ta bata ta jijjigata tayi bacci, kwanciyar bacci kawai take mayar da ita gidansu wanda yake mata wani masifar dadi a dalilin rashin Aunty da kuma sabon relationship dinsu da Inna.

A wannan yanayi ta fara tunanin cancelling tafiyarta makaranta, domin ita a ganinta ba wata rayuwa da ta fiye mata wadda take yi yanzu, gata ga Inna cikin yanayin da bata taba tsammani ba, ga Abba a gefenta bai chanja mata ba, sai ma wani karin kulawa da yake mata, ga uwa uba Hamma abokin shawara da sirrinta, ga sisters din da babu kamar su Farida da Adda Wasila, toh me zata je yi wata kasar? Bayan ga university nan a cikin jihar Gombe, idan bata so ga wasu nan cikin Nigeria na gwamnati da na kudi wanda zata yi hankali kwance ba tare da tayi mugun nisa da ahalinta ba?

A lokacin da take korowa Inna wadannan jawaban murmushi Innan tayi mai sauti sannan ta kalmashe murya cikin kulawa ta soma yi mata bayani kamar haka

"Ihman kenan! Har yanzu ke yarinya ce kuma duk tunanin ki na kuruciya ne. Ki daina yankewa rayuwar ki hukunci base on halin da kike ciki a wani lokaci domin it will either build your future or destroy it! Ihman irin qaddarar da ta same mu da wuya bawa yake daina kuka a kanta har abada, wani miki ne wanda kake rayuwa da shi tare da tsammanin kowanne lokaci zaka iya fama shi ya koma sabon ciwo! Sai kayi kamar kayi healing, ka warke ka manta, sai wani al'amari ya shigo wanda zai tono komai a sake maimaita labarin kamar lokacin ya faru, hakan kuma ba zai hana ka kuma jin zafin da kaji ba, bambamcin kawai shi ne kayi nasara a karshe ka samu sakayya kuma ka samu rayuwa mai kyau, amma wannan zogi da radadin sai kaji fresh a cikin zuciyarka!
Ina so ki samu abinda ni ban samu ba a wancan zamanin, wato support da fahimtar iyaye da kuma samun damar yin nesa da environment din da kike ki nutsa cikin duniyar ilmi ki kutsa cikin mutane daban daban ki fahimci rayuwa from different perspectives and angles! Ki samu damar tsayawa da kafar ki ki kai wani mataki wanda ko babu support din kowa you will be able to support yourself ! Kisan menene values da dignity din ki na ya mace ki san kuma duniya da halin mutanen cikinta. Ki samu wata dama wadda zaki iya zama tauraruwa ko fitila mai hasken da zata kawo haske cikin duhun da al'umma take ciki har ma ki kawo chanji.
Hakan ba zai taba faruwa ba sai kin yi ilmi mai zurfi kin shiga cikin mutane daban daban kinyi mu'amala kin kara shekaru da hankali da nutsuwa sannan za ki fahimci duk abubuwan da nake gaya miki.

"Nasihar da zan yi miki guda biyu ne Ihman! Na farko a duk inda kike, a kowanne waje, a kowanne hali, a kowanne lokaci, a kowanne yanayi, kada ki manta da addininki, mutuncin ki, darajar ki ta mace, kuma al'adarki ta hausa fulani! Na tabbatar idan kika rike wannan babu inda ba zaki shiga baki futo lafiya ba, domin shi addini yake guiding mutum, al'ada me kyau tayi shaping din shi, sanin daraja da mutunci kuma su nesanta shi da aikin danasani tare da siyo mi shi respect a duk inda ya shiga!
Na biyu Ihman, kada ki saka a ranki cewa duk maza mugaye ne, ko aure rashin yanci ne, ko kuma abinda ya faru da ke ya saka ki kudurin daura gaba da maza! Ko kadan hakan ba daidai bane! Kowanne mutum a rayuwa da qaddarar shi. Kuma a jinsin mace da namiji dole a samu mai kirki da mara kirki, duk wuya duk rintsi mutuncin ki shine aure  musamman a matsayin ki na ya mace! Ba wai ina nufin kiyi aure yanzu ba ko ki bawa ko dama ba, ina nufin ki budewa wanda ya dace kofa idan yazo, kiyi tunani ki tantance sannan kiyi addu'a Allah yayi miki zabi mafi alkhairi! Ko kadan kada kice zaki dauki fansa akan maza, wata damuwar zaki sake janyowa kan ki, abinda ya faru da ke qaddara ce daga Allah, ki hakura ki fawwala masa komai, kiyi kokarin gina rayuwar ki ta nan gaba domin ta zama misali ga wadanda suka fada irin wannan jarrabawar ta mu! Riko da kullaci ba shi da kowanne irin amfani Ihman, ina gaya miki ne saboda ya faru dani, ban taba jin dadin rayuwata ba, ban taba dariya genuinely kamar kowa ba, ban taba fatan wa kaina wani cigaba ko alkhairi ba! Gani nake komai ya riga ya qare rayuwata ta riga ta yanke ta baci! But look at me! Na cinye rayuwar tawa cikin damuwa da tsangwamar abinda na haifa, hakan bai amfana komai a gare ni ba kuma bai bani farin cikin ba, hakurin da nayi na yafe komai daga baya sai gashi komai ya warware na tsinci kaina cikin sabuwar rayuwa wadda ni ce na hana kaina samu tuntuni.......
Ina fatan ba zaki yi irin kuskuren da na yi ba"

Tun Ihman tana hawaye har ta goge su ta soma murmushi domin Inna bata yi shiru ba sai da ta haskowa Ihman wata irin kyakykyawar future da take hango mata harda iyalai da yaya da jikoki! Tasa hannu ta rufe fuskar ta tana dariya.

"Kai Inna!"

"Ba wata Inna da yardar Allah ko bana raye zaki tuna wannan maganar kice nayi miki! Yanda waccan addu'ar tayi tasiri akan ki  wannan ma haka zata yi"

Cikin wani yanayi tace

"Inna kina nan ma da yardar Allah! Allah zai raya mu tare muyi sharing farin cikinmu kamar yanda muka yi sharing bakin ciki"

Daga nan tunanin Ihman ya chanja zuwa wani irin hope da alkawarin cimma wannan buri na ta da na mahaifiyarta tare da fatan komai yazo mata cikin sauki da yardar Allah!

Anyi sunan Zainab inda baby taci sunan Inna kamar yanda kowa yayi hasashe, and again dai, Ihman tayi uwa tayi makarbiya tace sunan Baby Hinaya ita alkawarinta ba zai tashi ba. Da akace waccan Hinayan fa? Sai tace ai ba tata bace yar Ghana ce ta bar musu! Hamma ya goya mata baya baby ta koma Hinaya kamar yanda Ihman take so! Anyi shagalin suna an rabarbashe taro ya tashi lafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali, idan aka dauke Aunty wadda duniya tayi wa atishawar hatsi domin duk wani asiri da tsubbace tsubbacen da take taqama da shi tayi amma babu wani chanji ko cigaba, tunda Abba ya dauki Sadik ya tafi da shi da sunan neman magani har rana mai kamar ta yau bata sake jin labarin shi ba, idan ta tambaya sai yace mata ya siyar da shi yayi cefane da kudin!

Wata daya da ya shige aka yi case din Asma'u wanda ya sake mayar da Aunty kamar mahaukacciya, Haidar din da suke buri take ganin kamar babu wani abinda zai hana shi auren Asma'u ko don zumuncin da yake tsakaninta da uwarsa wadda suke uwa daya uba daya, sai gashi karon farko ya tabbatar musu da cewa shi ba irin Asma'u yake so ba rawar kanta yayi yawa, da ta nemi shawarar Zeenatun su kai sunan sa wajen Bokan su sai tace mata sam ita ba mahaukacciya bace ba zata taba yi wa danta asiri ba kuma tana gargadin Aunty ko da wasa kada ta sake ta saka mata da a bakin Malamai da bokaye.
Karamar hatsaniya sai ta zama babba, tun suna yi tsakanin su har magana ta futo fili,
Tafi tafi magana taje har kunnen maza, takanas Abba ya dau Asma'u suka tafi Abuja a dalilin dan yaron cikin da ya bayyana a jikinta, juyin duniyar nan kuma tace Haidar ne! Shi kuma Haidar ya kekasa kasa yace sam bai san zance ba, iyayensa suka goya masa baya domin Aunt Zinatu cewa tayi daman don bata gayawa Aunty bane, halin Asma'u ya chanja tana kawaye barkatai da kuma samari, kafin Aunt zinatu ya rufe baki Aunt ta dauke ta da mari, itama ta mike ta rama, dakyar aka shiga tsakanin su suna kokarin tonawa juna asiri.

A karshe dai Abba ya taho shi kadai ya bar su, dole suka biyo mota suka taho Gombe guiwa a matukar sanyaye, zuciyarsu cike da tunanin abinda zai biyo baya! Toh tun da suka koma har wannan lokacin Abba bai waiwaye su ba, Hamma da yayi mi shi maganar yayi saurin dakatar da shi ta hanyar cewa Idan ya sake yi masa magana akan Aunty bai yafe ba. Daga nan kowa ya shafawa kansa ruwa aka zuba musu ido, kowa ya san yanda mai hakuri yake yi idan aka kai shi bango don haka ba wanda ya sake takurawa Abba akan zancen Aunty har wannan lokaci, ita kuma tana makale cikin gidan kanta a kulle domin duk wata mafita da take tunani ta toshe, yan'uwanta duk bayan Zinatu suka koma saboda tafi ta abun duniya kuma tafi ta kulawa da su, gidansu ba wani karfi gare su ba don haka bata fatan sake komawa rayuwa cikinsa, babu wani maga isa da take da shi wanda zata kaiwa kukanta ba tare da ta tonawa kanta asiri ba don haka taja waje daya tayi shiru tana girbar abinda ta shuka!
Ko da babu sanin Abba, Hamma bai taba bari sun yi kukan wani abu a gidan ba, komai ya ajiye musu wadatacce, sannan bayan sati ya kan leqa ya gan su, ya kuma baiwa Aunty kudi ta kai Asma'u asibiti babu kunya tasa hannu ta karba tana godiya jikinta a mugun sanyaye!

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now