WACECE NI??? Part2 Chapter 17

146 11 0
                                    

An wayi gari da matsanancin shiri a gidan, ko'ina ya sha gyara na musamman qamshin asalin turaren sandal ya karaɗe dukkan sassan gidan. Ihman dai bakinta kullewa yayi lokacin da ƴan'uwanta suka rakata part ɗin da aka buɗe mai kamar girman na Hamma. Kamfani ne suka zo suka shirya wajen tas da ƙayataccen decor na zamani.
Flat ɗin ɗakuna uku ne da parlour biyu sai dinning da kitchen sannan garden a baya da kuma ɗakin masu aiki. Tsarin jeren babu hayaniya babu tarkace sai manya da ƙananun frames da suka fi komai ɗaukar hankalinta a gidan da kuma standing lamps da aka ajiye a kusurwar kowanne parlour. Ga sassanyan kamshin Diffusers, Masu sanyaya zuciya duk inda ka shiga.
Bayan sun futo kuma suka dawo main cikin gidansu, Daman katon parlor ne guda ɗaya da dinning inda kofar kitchen take wadda ake shigowa cikin falon ta baya. Daga karshen falon kuma wata matakala ce za ka taka wadda zata sadaka da kofofi guda uku, ta tsakiya ita ce zata kai ka wajen Abba, ta gefen dama ita ce wajen Inna yanzu kuma aka buɗe gefen hagun aka gyara, wanda shi ne wajen Aunty.
Daga ni shima aikin Hamma ne domin komai sabo ne, sai dai bai kai can part ɗin kyau da kyale kyale ba.
Ihman ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani ɗaci a cikin ranta, a iya fahimtar ta Aunty bata cancanci sake samun gurbi a wannan gidan ba, domin bata son zaman lafiya, me yasa ba za'a nemar mata wani gidan a wata unguwar ba idan dole sai Abban ya dawo da ita? Idanun Asma'u da ke wajen ya hana ta cewa komai amma kallo ɗaya zaka yi mata ka gane bata yi maraba da wannan tsarin ba.

Da yamma kowa yayi wanka ya shirya, motoci biyu ne suka ɗauko Aunty daga Airport babu mace ko ɗaya a ƴan rakiyar sai Abba da Kawu Bala da kuma Baffanta wanda Babansu Inna ya karɓi aurenta a hannunsa. A cikin gidan kuma A.Aisha matar kawu Bala ce kawai a tare da Inna sai ƴaƴan gidan gabaɗaya sune suka tarbe su a Guest room!
Aunty na lulluɓe cikin sabuwar laffaya ruwan madara, kallo ɗaya zaka yi mata ka girgiza duk da gyaran da ta sha na kome! Ta zaizaiye sosai ta rame tayi baƙi kamar ba wannan kyakykyawar ba'abziniyar ba. Jikinta yayi mugun sanyi domin ko waɗannan kaifafan idanun na ta sun rankwafa sun risina.
Bayan sannu da zuwa da gaishe gaishe Uncle ɗin Aunty ya gabatar da ita ga iyalan a karo na biyu tare da dogon ban haƙuri akan duk abubuwan da suka faru, ya sake tabbatar musu da cewa a wannan karon Aunty za ta zauna da su zaman lafiya da zuciya ɗaya kuma za ta gyara duk kura-kuren da ta aikata a baya.
Kawu Bala ya amsa tare da yi musu nasiha gabaki ɗaya wadda ta sanyayawa kowa jiki sannan Abba yayi gyaran murya ya soma na shi jawabin.

"Na so wannan taron ya kasance a gaban Quraishi da Sadik saboda muhimmancin su cikin wannan al'amari amma kuma Allah bai nufa ba."
Ya dubi Aunty yace

"Na yi miki wannan jawabin amma zan sake karo na biyu a gaban kowa! Iyalina a halin yanzu kansu a haɗe yake, babu bambamci tsakanin ƴaƴan Asiya da na ki, babu wanda zai shigo gidannan ya gane akwai ɗan da ba Asiya ce ta haife shi ba. Ta haɗe kansu gabaɗaya suna rayuwa cikin aminci da ƙaunar juna da girmamawa.
Asiya tana baiwa yarana tarbiyya mai kyau daga mazan har matan kuma sun yi riƙo sosai akan turbar da ta ɗora su hankalinsu a kwance!
Wannan shine tsarin da kika dawo kika samu a cikin wannan gidan na Kano ba irin wancan tsarin na garin Gombe ba. Ina mai tabbatar miki da cewa wannan shine burina kuma fatana har ƙarshen rayuwata, na mutu na bar ahalina cikin koyarwar addini da haɗin kai da ƙaunar juna. Zaki dawo gidan nan ki zauna ne a bisa sharaɗin bin duk wata ƙa'ida da tsarin wannan sabuwar rayuwar, ban amince kuma ban yarda ki karya mun kowanne tsari ba, ba zaki sake shigo da wata bidi'a wadda zata raba mun kan iyali ba, ba zaki sake neman kowa da fitina ba, ba zaki kuma hargitsa mun kan yara ba.
Ga abokiyar zaman ki nan Asiya, ko a wancan zamanin kin ƙullace ta kin zarge ta akan ta raba ni da ke ta kankane komai, ina ganin yanzu za ki fahimci dalilan da yasa ta hau wannan matsayin, ki kalli rayuwar yaran da kika ruguza kika tafi? Ki kalli yaran ki yanzu ki haɗa da wancan lokacin da kike tare da su haka nutsuwar su da kwanciyar hankali take? Shi kansa gidan haka yake? Yanzu kin fahimci dalilin da yasa nake bata girman da nake bata? Kin fahimci dalilin da yasa Sadik ya zabe ta akan ki? Kin fahimci dalilin da yasa kowa yake komawa bayanta?
Ba asiri tayi mana ba kamar yanda kike iƙirari a kullum, rayuwa take da kowa da zuciya ɗaya kuma zuciyar musulunci da ihmani.
Ina jan hankalin ki akan ki bata haɗin kai kuci gaba da gudanar da rayuwa akan wannan turbar, bani da matsala da ita a kan ki don haka bana son naji wata matsalar ta taso daga gare ki. Kin amince?"

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now