💔WACECE NI???💔 part2 page Thirty-one by CUTYFANTASIA

59 8 0
                                    

     2YEARS LEAP
Ihman kwance cikin kujerar jirgi tana bacci peacefully bayan dokin da ya cika ta na zuwa Nigeria for the first time bayan tayi aure. YESS! Sai da tayi shekaru uku cirr a Egypt bata je ko'ina ba a dalilin tsaurin karatun da take yi, a duk lokacin da ta dan samu hutu kokari take ta saita gidanta da rayuwarta a can, karatun ba na wasan yara bane, ya wuce yanda tayi tsammani don haka kullum a tsaye take tana iya kokarinta domin ganin ta cimma burin da tayi wa kanta alkawarin cimmawa.
Mafarki take yi mai dadi lokacin da taji maganar Faris yana tashin ta ta daura belt sun iso Nigeria. Tuni ta wartsake tana wani irin murmushi wadda ke fallasa matsanancin farin cikin da take ciki.
Don murna a wajen ta bar jakarta ta wuce Faris tana dariya, girgiza kai yayi ya koma ya dauko mata jakar ya biyo ta.
Tun daga nesa Inna take kallon wannan zankadediyar matashiyar tana mamaki, she has changed, she has really changed!!!
A cikin shekaru ukun Inna ce kawai basu hadu ba domin kowa yaje Egypt ya kai mata ziyara musamman lokutan da take throwing tantrum din lallai sai tazo gida ko lokacin karatu ne, sai Faris ya kira Hamma ya dinga magiya a zo daga Nigeria a ganta ko hankalinta zai kwanta. Toh a take Hamma zai shirya tafiyar da duk wanda zai samu dama a tafi Egypt don kwantar da hankalin Ihman, Uncle din ta yaje sau biyu, Hinaya tana zuwa yi mata hutu duk karshen shekara don haka babu kishiryawar wanda take yi kamar Inna. Ita ma kuma Innan tana kin zuwa ne saboda fultancinta amma deep down babu abinda take so irin ganin Ihman! Ko zuwa airport din ma Ihman ce ta rantse idan ta sauka a jirgi bata ganta ba sai ta juya da ba zata zo ba.
Cikin matsancin farin ciki take kallon Ihman wadda ta chanja daga waccan santaleliyar bafulatanar zuwa nutsatstsiyar matashiyar balarabiya. Tayi fari akan wanda take da shi ta qara tsayi kamar an ja ta, bata yi qiba ba saboda wahalar karatu amma tayi gogewar da idan ka tsaya kallonta zaka bace cikin mamaki.
Tana sanye ne cikin baqar Sakakkiyar abaya mai golden din zare ta nannade fuskarta da mayafin looking kamar wata fure a cikin furanni mafi haskawa.
A guje ta karaso ta rungume Inna tana fashewa da kuka, Hamma ya girgiza kai yana murmushin farin cikin da ya mamaye mi shi zuciya. Cikin sanyin murya yace
"Ihman kin makance ni baki ganni ba ko?"

Ta dago da sauri tana murmushin da yake bayyana madaukakin farin cikin da take ciki ta kama kunnuwanta tana roko

"Hamma ko na makance ai ba zan kasa gane ka ba! Innan ce tayi missing dina da yawa..."

Inna ta ture ta tana cewa

"Inji wa ya gaya miki?"

Suka fara yi wa Inna dariya.

Cikin barkwanci da farin ciki suka shishshiga mota suka dau hanyar gida. Faris yaso ya kama masauki ya sauka amma Abba yace sam bai yarda ba shima ai ya zama family yanzu, tuni an gyara mi shi guest room an saka turaren wuta. Su Aunty ana kitchen ana hada hadar abincin baki kai sai ka rantse yayanta ne zasu sauka. Wato babu abinda yafi zaman lafiya dadi domin rayuwar gidan completely ta chanja salo, idan kaji bakin Aunty cikin maganar yara sai dai tace "toh" mai bada umarnin da shawara Inna ce don haka ta samu gurbin zama sosai a zukatan iyalan kuma nan da nan suka manta da waccan Auntyn da suka sani a baya suka bata sabon matsayi.
Satin su Ihman biyu a Kano suna hutawa tare da jin dumin yan'uwa duk da shi Faris din kwanakin shi hudu ya tafi Abuja akan wani uzuri wanda bai fada ba amma maganar gaskiya zancen filinsa ne ya kai shi, shekaru goma sha biyu kenan da siyan filin da suka hada su uku, kuma shi ne kawai kadarar da bai sayar ba a ciwon Inna a dalilin ba mallakin shi ne shi kadai ba. Bayan sun yi aure da Ihman daya daga cikin su yace yana da bukatar siyar da wajen zai kara aure, sai Faris ya biya shi kudin ya zama kaso biyu cikin uku ne na shi. Kwatsam yanzu wani dan siyasa ne yake son wajen zai yi amfani da shi, aka taya 200m sai yace ya ninka kusu kudin, Imran abokin Faris yace maza su sallama su karbi kudinsu, toh shine dalilin da ya sanya Faris tafiya Abuja. Aka kammala ciniki aka ba shi kudin shi ya dawo Kano cikin farin cikin samun damar cimma kudurin da yayi ba tare da ya gayawa kowa ba.

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now