WACECE NI??? Part2 Chapter Thirteen

150 16 4
                                    

Tun Ihman na tunanin zata iya nemo Hinaya ita kadai har abun ya shallake tunaninta, ta futo daga cikin harami ita kadai tana rangaji hawaye wani na bin wani akan fuskarta. Kallo daya zaka yi mata ka gane tana cikin madaukakin tashin hankali! Har ta futo daga masallacin wata zuciyar tace mata

"Ke kuwa ki baro harami ki tafi gida neman agaji?ki koma kiyi addu'a"

Sai kawai ta juya tana daukar wayarta da take ta kuwwa a karo na ba adadi! Tayi swiping ta saka a kunne

"Inna Hinaya ta bata! Na shiga uku"

Abinda ta fada kenan ta sake fashewa da kuka cikin wani irin rauni! Ji take yi kamar ba zata sake ganin yarinyar ba har abada, ji take kamar rabon su rabu ne ya saka ta tahowa da ita, ji take yi kamar zuwan nasu tare aikin qaddara ne irin wanda take yi a lokacin da taso datse wata alaka ko kauna.

"Ki kwantar da hankalin ki Ihman! Hinaya gata nan an kawo ta! Ki taho masauki yanzu"

"Inna cewa kika yi an ganta?"

"Ehmana gata nan"

"Inna wasa kike mun don na dawo ko?! Ya za'ai ta kawo kanta hotel daga masallaci! Inna ki gayamun gaskiya don Allah"

Sai kawai Inna ta sakawa Hinaya wayar a kunne, Ihman bata yi aune ba taji zazzaqar muryar yarinyar tana cewa

"Aunty ki dawo, Uncle ne ya kawo ni gida ya siya mun ice cream da....."

Inna ta karbi wayar tace

"Toh kinji dai ko? Ki dawo yanzu"

Wani irin numfashi ta sauke mai dauke da duk wani tension da stress da tashin hankalin da ta shiga a wadannan hours din! Ta daga hannu ta godewa Allah sannan ta share hawayenta ta futo daga masallaci tana jin kunyar hada idanu da Inna yanda ta bayyana mata tsananin damuwar da tayi da Hinaya.(daga baya kenan)
Sannu a hankali take takawa zuwa cikin hotel din tana ayyana irin tashin hankalin da zasu tsinci kansu a ciki idan akace Hinaya ta bata a wannan garin cikin wannan zahamar! Tana cikin tunani taci karo da mutum, tayi maza ta koma baya jikinta yana rawa, dagowar da zata yi idanunta suka yi kyakykyawan ganin da ya gigita kwakwalwarta ya daki zuciyarta ta tsaya cak na wasu dakiku!
Sai da tayi kwakwkwaran minti daya ko blinking bata yi ba tana kallon abinda yake gabanta me kama da mafarki, a cire kama ma, wannan mafarkin da tasha yi ne a baya, har zuwa yanzun ma bata daina ba, sai dai tana iyakacin bakin kokarinta wajen binne wadannan mafarkan a cikin zuciyarta ba tare da ta bari sun ci gaba da tasiri cikin kwanyar ta ba.
Idan har ba idanunta ne suka hasko mata karya ba, kwakwalwar ta tayi kuskuren gaya mata hoton wanene akan kwayar idaunta ba, toh tabbas wanda yake tsaye a gabanta FARIS ne duk da dimbin sauyin halitta da kama da ya samu ba zata taba mance wannan mutum cikin rayuwarta ba.

Shi din ne dai, amma wannan na gabanta isn't that joyful and playful Faris! Wannan wani cikakken mutum ne mai tsananin kwarjini da kamala, baki ne har yanzu, amma fatar shi ta bayyana cewa an sauya mata yanayin wurin zama daga zafin Nigeria zuwa wani waje mai ni'ima, sannan akwai wayewa, exposure, ilmi, hankali da bunkasar rayuwa a tare da shi ninkin ba ninkin din na baya. Abinda kawai ta nema ta rasa akan fuskar shi ta da shine walwala da murmushin da baka raba shi da shi ko ba magana yake ba, wannan fuskar shi a hade take tamau kamar bakin hadari, ya rame fiye da baya amma kwarjininsa yana nan! Yana sanye cikin italian fabric din "Silver Dust Wool" ruwan gwaiduwar kwai an mi shi dinkin da ya zauna a jikinsa kamar zane! Ya dora hula ruwan zuma sak kalar agogon zallar fatar da yake tsintsiyar hannunsa dan gidan "polo Ralph Lauren" tare da slippers din kamfanin!

Gabadaya loosing balance tayi zuciyarta ta kasa daukar wannan gagarumin al'amari don haka ta sulale kasa sumammiya a dai dai lokacin da Hamma ya iso wajen cikin sassarfa!

"Faris ya akai ka bari ta gan ka?"

"Mu fara bata taimakon da take bukata Hamma!"

———————————————————————————
                            Two hours leap
Bude ido tayi ta ganta akan gadon dakin hotel din su a kwance, ta sake mayar da su ta lumshe tana so ta tuna abubuwan da suka faru amma tsananin ciwon da kanta yake mata ya hanata wannan damar!
Sai tayi shiru kawai tana kiran sunan Allah a cikin zuciyarta har wani baccin ya sake dawowa ya lullube ta wanda bata sake tashi ba sai da akayi sallar magrib! Wannan karon da ta bude idanu babu kowa a dakin, ta tashi zaune tana ciza lebe tare da karanto kalmar shahada, babu laifi nauyin kan ya ragu sai kadan sai kuma jikinta da yayi mugun sanyi! Cikin kasala ta mike ta rangaji ta shiga toilet ta wanke bakinta ta dauro alwala! Tana futowa ta samu Inna tana jiranta a bakin kofar!

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now