WACECE NI??? Part2 page twenty-three by Cutyfantasia

128 14 1
                                    

Ihman tayi murmushi tana gyara zaman wayar a kunnenta tace

"Idan aka manta Dr kuma wa za'a tuna? Wallahi it's soo busy here kinsan sha'anin family house"

Dr Amani tace

"Nayi miki uzuri anan! Na fahimta, Ina Uncle?(saboda yawan labarin Uncle da Ihman take baiwa Amani ya sanya ta saba da tambayar shi kuma ko da wasa bata taɓa sanin cewa mahaifin Ihman bane domin yanayin shaƙuwarsu da mu'amalar da take nuna mata a tsakaninsu sannan kuma tana jin tana kiran Abba wadda ta tabbatar shine a matsayin mahaifinta)"

Cikin nishaɗi Ihman tace

"Yau dai zaku gaisa da Uncle i promise! Ke dai ki tabbatar kin sace mun zuciyarsa daga gaisuwa domin wallahi da ke kaɗai na aminta da Uncle ɗina kuma kema shi kaɗai ya dace da ke"

Ta ɓangaren Dr Amani wani dokawa gƙirjinta yayi, wani sashe kuma ya rangaɗa guɗar farin ciki domin tunda Ihman ta soma bata labarin wannan Uncle ɗin ya shiga ranta, balle kuma ranar da ta tura mata hoton sa wanda yayi a office cikin ɗanyar suit ruwan bula kamar wanda yake cikin early 30s ɗinnan.
Don haka yanzu da Ihman ta shigo mata da wannan maganar wani irin farin ciki da annashuwa suka kama ta.
Jin shirun Amani ya tabbatarwa da Ihman zarginta don haka ta faɗaɗa murmushinta ta shige gidan Uncle kai tsaye. Don tsabar zumuɗi ko sallama bata yi ba ta banka cikin falon, sai kawai taci karo da Faris da Hinaya suna zaune kane kane akan carpet suna labari, Uncle na daga kitchen yana dafa shayi da waya a kunnen sa. Sai tayi slow a take ta kuma rausayar da murya tace wa Dr Amani

"Dr Uncle is busy on a call! Idan ya gama zan kira ki"

Suka yi sallama ta dubi Faris a sace sai suka haɗa ido, tayi maza ta ɗauke kanta tana gaishe shi, ya amsa cikin kulawa sannan ya mayar da hankalinsa ga Hinaya wadda take ba shi labarin school ɗinsu.
Cikin ƙarfin hali Ihman ta tattaro duk dauriyar da take da ita ta dube su ta kira Hinaya a tsanake.
Yarinyar ta ɗago tana ansawa cikin murmushinta mai kyau

"Kije wajen Uncle a kitchen kice masa nima zan sha Tea ɗin a dafa dani"

Ta amsa da"toh Aunty"
Sannan ta falfala da gudu hanyar kitchen tana kwallawa Uncle kira, sai da ta ɓace sannan Ihman ta dawo da kallonta ga Faris wanda daman tunda ta kira Hinaya yake kallonta don jin dalilin da ya sanya ta korar masa ita suna hira.
Ta rausayar da kai ta ƙarasa kujerar da take kallon wajen da yake zaune ta zauna a nutse sannan ta soma yi mi shi magana a hankali

"Don Allah idan ba zaka damu ba wata alfarma nake nema kayi mun ba don ni ba don Allah"

Cikin nazari yake kallonta bai ko ƙiftawa, sai da ta kawo aya sannan ya gyara zama yace

"Wacce irin alfarma ce wannan?"

Ba tare da ta ɗago ba taci gaba da magana

"Na san ka san Dr.Amani tunda a wajen ka na fara saninta! Since wannan ranar da muka je asibitin ta Allah ya haɗa jininmu muke communicating muna zumunci. She has even told me everything about her kuma ni gabaɗaya matar ta kwanta mun a raina. Tunda na haɗu da ita nayi wa Uncle sha'awarta kuma nake ta fatan dama Allah zai qaddara aure a tsakanin su domin dukansu sun dace da juna kuma kowanne yana buƙatar auren don haka nake ta addu'a akan Allah ya tabbatar idan da akwai alkhairi a ciki.
Yanayin Dr.Amani da fahimtar da nayi mata a ɗan wannan lokacin nake ganin ba zata yi mun qarya ba amma duk da haka ina son naji daga bakin ka akanta don Allah before I proceed!"

Tunda ta fara maganar yake kallonta yana murmushi a cikin ransa, mai hali bai fasa halinsa, ita dai Ihman kullum burinta ta saka farin cikin wani a gaban nata ko da ita zata cutu. She is the most selfless person he has ever met kuma har yanzu bata chanja ba. Tana da zuciya mai kyau, tana da halaye masu sanyi kuma da kyakykyawan zato akan mutane kuma shine ɗaya daga cikin dalilan da yasa yake ƙaunarta.

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now