WACECE NI??? Part2 page Fifteen BY CUTYFANTASIA

142 12 0
                                    

Tunda Faris ya bar office Ihman ta nemi nutsuwa ta rasa! Tayi matukar ƙoƙarin cigaba da danne ramin da ta haƙa cikin zuciyarta ta binne Faris da memory ɗinsa amma ina, liƙin ya riga ya ɓalle ciwon ya dawo fresh kamar wancan zamanin ko ma fiye da haka! Idan har abinda take ji akan Faris shine so, toh tabbas zai iya yin ajalinta domin bata taba jin wani ciwo mai ɗaga hankali da raɗaɗin shi ba. Ko da ta koma gida bata iya saka komai a cikin ta ba, bata iya cewa kowa komai ba ta shiga ɗakinta ta kulle ta faɗa gado tana numfarfashi, daga bisani wani irin kuka mai cin rai ya subuce mata, wasu abubuwa guda biyu take ji a lokaci ɗaya, soyayyar Faris mai matukar tsanani da kuma alwashin ba zata sake bashi damar samunta a karo na biyu ba komai tsanani saboda ta nuna masa cewa shi ɗin ba shi ne autan maza ba.

Har ƙarfe tara bata futo ba, Inna tazo ta kwankwasa mata ƙofar tana kiran sunanta, dakyar ta tashi zaune ta goge fuskarta sannan tayi gyaran murya ta amsa.

"Inna bacci ne ya ɗaukeni, bara na watsa ruwa na futo"

Daga nan ta shiga toilet tayi wanka da alwala ta futo ta shirya ta gabatar da sallar isha'i sannan ta gyara fuskarta don ta ɓoye koɗewar da tayi ta mayar da Hijab ɗinta ta futo parlour. Yau har da Abba a dinning ɗin za'ayi dinner don haka ta sake ƙoƙarin kawar da damuwar da take kan fuskarta ta tsuguna ta gaida shi cikin ladabi

" Abba barka da dare!"

"barka dai Ihman ya aikin?"

"Da godiya Abba"

Sannan taja kujera kusa da Adda Asmee ta zauna tana amsa tambayar da Asma'un take mata na rashin futowarta da wuri.

"kaina ne yake ciwo sai na sha magani na kwanta, daga nan bacci ya ɗaukeni"

"yanzu yayi sauƙi?"

Ta ɗaga kai tana murmushi sannan suka yi serving junan su suka soma cin abincin cikin walwala da farin ciki, the family has never been this peaceful and happy, breakfast, lunch and dinner tare suke yi, wani lokacin har da Abba, anan suka gasgata cewa Aunty ce matsalar gidan, tunda ta tafi Inna ta haɗe kan yaran gabaɗaya suke rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, kai ba yanda za'ayi ka bambamce ƴaƴan Inna da wanda ba nata ba a cikin su. Adda Asmee kuwa kamar tun can daman a hannun Inna ta taso. Sun yi wata irin shakuwa kamar ta ƴa da uwa.
Sun kammala kenan Hamma ya shigo, duk ƙannen na shi suka yi masa sannu da zuwa sannan suka miƙe don ba su waje da iyayen sa. Cikin nutsuwa Hamma yace

"ke Asma'u da Ihman ku dawo zan yi magana da ku"

A take fuskar Asma'u ta washe Ihman kuwa ta shiga cikin ruɗun abinda ya sa Hamma yace su zauna gashi yau gabaɗaya yanayin sa a Hamman ya futo babu wasa ko kaɗan akan fuskarsa. Duk suka dawo suka zauna manne da juna kamar za'a kama su.
Hamma yayi gyaran murya ya soma magana

"Abba mutumin da yake zuwa wajen Asma' u ne yayi mun magana akan yana so ya turo, nayi bincike akansa kuma na gamsu don haka zan tambaye ta a gaban ku ta amince ko kuwa, domin ba zaiyu daga baya tazo da wata magana a saurareta ba in dai ba matsala ce mai girma ba!"

Murmushi Abban yayi, zuwa yanzu yana rayuwa ne peacefully babu tension ko tararrabi, duk wani responsibilities din uba Wannan Ɗan da babu kamarsa ya ɗauke masa, iyakaci kawai ya sanar da shi ko ya nemi izini amma sauran komai shi zai yi. Don haka a yanzu ba sallar da zai yi bai yi wa Allah godiyar kasacewar wannan maɗaukakin bawa a matsayin ɗansa ba.

"kayi komai Quraish! Ai yanzun ni sunan Abba kawai nake amsawa, amma duk wasu responsibilities ɗina ka ɗauke."

Hamma ya gyara zama ya dubi Asma'u yace

"kin amince kina son shi za ki aure shi?"

Adda Asmee ko da bata amsa da baki ba haske da annurin da ya baibaye fuskarta ya bayyana komai! Domin zama da Inna ya horar da ita kunya da kawaicin da bata da shi a da.

WACECE NI??? Part 2Where stories live. Discover now