💜💙💜
*LAIFIN SHI NE*
💜💙💜
_Na Maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
Da sunan Allah mai rahama mai jink'ai
Zan fara wannan novel ba domin cin zarafin kowa ba,idan kin ga yayi kamanceceniya da ke ko da kai to arashin sani ne nayi ba don cin zarafi nayi ba.
Gajeren labari ne
1️⃣
Awani gari wanda ake kira rafin k'irya acikin jahar kebbi,
wata yarinya ce 'yar kimanin shekara goma tafe da tallar zogalah akanta zata je cikin birnin garin nasu wajen sayar zogalenta.Tana tafe tana rera wak'arta mai dad'in d'and'ano a hanya,daya ke daga garin nasu da cikin birni naira hamsi ne yake kaisu cikin birnin, shiyasa mafi yawansu suke zuwa a k'afa cikin garin,yarinar tana tafe bata tsaya ko'ina ba sai inda k'awayenta suke tsayawa don tafiya birni, tana kai wajensu sai tace"wato yau A'ishe da Nafisah da Larai ko ku biyomin gida mu wuce tare,shine ku kazo wajen da muke tsayawa kafin mu shiga birni ku ka tsaya ko". Larai ce daman daga cikinsu wadda bata shakkar Hafsat sosai,sab'anin sauran k'awayen nata dake tsoronta,Larai itace tayi k'arfin halin cewa"to gaskiya baza muje gidanku ba masifaffiyar matar ubanki ta had'a damu ta zane,domin kin san ta gargad'emu kar ta sake ganinmu tare da ke,shiyasa kika ga yau bamu biyo miki ba". Hafsat tace" ke dai yau ai nayi arzik'i da bata dokeni ba,da yake yau ban makara ba wurin hasa wuta ba ,naje rafi na d'ibo ruwa na dafa zogale har nayi shara da wanke-wanke,koda ta tashi
na gama komai na gida har na d'ora d'umame,
shiyasa yau bata doke ni ba shiyasa yau harda wak'a nake yi bisa hanya, saboda yau bata dokeni ba ".Nafisat da ta fahimci cewar Hafsat ba zata yi shiru ba tayi tsagal tace"ku dai mu tafi wurin tallah kar muje bamu saida da wuri ba adokemu".Sai suka kama hanya suna tafiya suna firarsu har suka isa cikin gari, suka shiga kasuwa kowa ya fara sayar da tashi,wasu kuma suka shiga cikin gari gidajen mutane suna saidawa har dai marece yayi , sannan suka koma had'uwa suka yi bankwana da juna,kowace tayi gidansu cikin murna sab'anin Hafsat dake cikin fargaba da zullumin mi zata je ta tarar domin ta san sai tace ta dad'e bata dawo ba ta d'ora sanwar dare ba.Tafiya take yi cike da rashin kuzari k'irjinta sai luguden fargaba yake mata har ta isa gida, shigarta keda wuya cikin gidan ta ga an jawota an rafka mata mari kaji fauuu!Wani irin rikitaccen zafi da zogi ya ziyarci kunci da k'wak'walwarta,d'ago fararen idanuwanta tayi domin ta ga ko wa ye ya kafta mata mari,charabb idanuwanta suka sark'e cikin nata ba kowa bane ya mareta face matar ubanta mai suna Innah Jummai,cikin azarb'abin masifa tana huci tace "wato kin raina ni ko saboda tsabar wulak'anci tun da safe ki fita sai marece zaki dawo gida ko,to ki sani ko yau haka zaki kwana ba zan baki komai ki ci agidan nan ba mara mutunci wadda ta biyo halin matattar uwarta,mi k'omin kud'ina na k'irga na gani ko biyar ta b'ata na lahira sai yafi ki jin d'adi..!"Innah Jummai ta mik'a mata hannu alamun ta bata kud'ad'enta,ita dai Hafsat kuka kad'ai take yi domin babu abinda ta tsana irin azagar mata mahaifiya, ta mik'a mata kud'inta ta k'irga taga sun cika,ajiyar zuciya Innah Jummai ta safke cike da tsanar Hafsat tace "kin yi arzik'i da yau sai na halaka ki akan kud'ina,shashasha tashi ki je ki d'oramin tuwon dare don in yau kika kai Isha'i ba ki gama ba ranki sai ya b'aci".Hafsat taja k'afafuwanta da k'yar tana kuka mai ban tausayi tana hasa wuta,can ta d'ora tukunya sauk'inta guda ana ba Sule ya kai nik'a shiyasa data san ta banu in taje ba ta samu ba,dakasheta ne kawai Innah ja Jummai baza tayi ba .
Hafsat tana aikinta tana sharar hawaye har ta k'are tuwo, sauk'inta guda Innah Jummai ke kwashewa ita iyakacinta d'orawa da talge ,shiyasa wani aikin ke mata sauk'i don miya ta fara kad'awa sannan tayi tuwo,Innah Jummai ta zo nan ta kwashe sai ta wuce zuwa yin sallah,da yake ba wani ilimi ke gareta ba don makarantar da take zuwa ba kodayaushe ba ne ,sai idab basu samo zogale ba ne take samun ta wuce makarantar allon suyi ta karatu sab'anin d'iyan Innah Jummai guda biyu da basa zuwa makaranta,don Meri kam bata zuwa makaranta acewarta ita bata zuwa saboda b'ata lokacinta zata yi kuma Innah Jummai ta biye mata, kullum sai dai ta ci kwalliya ta fita yawo sai kusan magariba take dawowa ,da yake ta girmewa Hafsat da shekara uku shiyasa take abinda ta gadama domin wani lokaci har ita ke dukan Hafsat,kuma babanta wanda ake kira da Kabiru mai saida kayan miya ko ajikinshi saboda shi mutum ne mai yarda da abin da aka fad'a masa,baya bari yayi bincike sai ya yanke hukunci......................
_Comments&Shares._
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.