💙💜💙💜💙
*LAIFIN SHI NE*
💙💜💙💜💙
_Na Maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
3️⃣9️⃣
Bayan Malam Kabiru ya gayawa Innah Jummai cewar ta shirya ita da k'anenshi su biyu su rakata,don su san inda d'iyarsu zata zauna, bayan ya fita ne suka k'ara tattaunawa da Jalaluldeen har dai suka gama shiri,haka ya shiga ya k'ara yi mata nasiha ya janyo hannunta ya sakata cikin mota,suma sauran suka shiga yana d'aga musu hannu har suka b'ullewa ganinsa, bawan Allah har da kwallah sai da yayi daga nan ya juya gida yana mata fatar samun zaman lafiya arayuwarta,su kuwa su Jalaluldeen sune basu kai ba sai wuraren magariba,domin ba gidansu za'a sauketa ba gidanshi daya gina a chan za'a kaita,da safe kuma suyi walima bayan ya saukesu gidan iyayensa an kawomasu Innah Jummai komai cikin mutuntawa,anyi musu tarba ta mutunci kamar an dad'e da sanin juna aka kaisu masaukinsu,saboda a chan ne zasu zauna har agama hidima bayan sunci sun sha,sukayi sallah suka kishingid'a sai barci dayake dare yayi don har tara ta gota, bayan garin ya waye sukayi shiri da kuma breakfast don da wuri za'a kai ta gidanta,haka kuwa ce ta faru misalin k'arfe goma suka fito da ita Hafsatu don tafiya da ita,harda mahaifinsa Alhaji Abubakar maigishiri ya dawo daga k'asar waje don shima ya gayyato mai walima shida yayan Jalaluldeen Usman,su suka gayyato malamin da zai gabatar musu da walima,don su Zainab ne k'awayen amarya,dayake ita ma anyi nata auren kona cema kusan lokaci guda ne da na Dr.Mansur shiyasa ma bai damu da tarewarta da wuri ba,duk da auren Zainab haka suka shige gaba suka zama k'awaye don ko Meri sai da ta biyosu acewarta 'yar uwarta ce dole aje da ita,haka aka d'auki amarya Hafsatu sai cikin tangamammen gidanta wanda tsabar had'uwarsa ma b'ata lokaci ne wajen gaya muku,haka dai aka shirya amarya don k'arfe biyu za'a fara atashi k'arfe hud'u shiyasa aka jera komai cikin gidan,don gida ne mai fad'in gaske bayan anyi walima lafiya an k'are kowa ya watse, aka bar dangin Hafsatu ko su gobe za'a sa direba ya maidasu gida.
Haka kuwa akayi bayan 'yan uwanta sun gyara ko'ina na cikin gidan, dayake akwai masu sharar tsakar gida daba shuka ruwa shiyasa basu yi na tsakar gida ba,na cikin gida kad'ai sukayi da dare yayi bayan sunyi dinner suka k'ara yi mata nasiha,kowa yaje ya kwanta da gari ya waye sukayi shiri misalin sha biyu akazo aka d'aukesu da shataransu na arzik'i, aka maidasu sai garin rafin k'irya akabar amarya ita kad'ai daga ita sai halinta,bayan wucewarsu Innah Jummai Hafsatu taci kuka har ta gode Allah don ita saida kowa ya watse,taji duk kad'aici yazo mata tana nan zaune tana kuka sai ga Jalaluldeen ya shigo da sallamarsa,ko inda yake Hafsatu bata kallah ba balle ta amsa sallamarsa,don ko maganarsa taji sai gabanta ya fad'i saboda tsananin tsanar da tayi masa arayuwa...........................
_Comments&Shares._
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.