💜💙💜
*LAIFIN SHI NE*
💜💙💜
_Na Maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
7️⃣
Bayan ya zo ak'ofar gidansu yayi tsaye yana waige-waige can sai yaga yaro k'arami zai wuce,daga ganinsa sai ya kirashi yace ina zaka je?.Sai yace masa aikinsa akayi sai yace kai yaron nan zo ka kiramin Mariya,bayan yaron ya shiga ya kirata bada jimawa ba sai gata ta fito ta masa sallama, ya amsa mata Mariya cikeda kunya da ladabi tace masa" ina wuni".Malam Kabiru yace"lafiya lau Mariya nasan ba kiyi tsammanin ganina ba ko".Cikin murmushinta mai sanyi tace"gaskiya kam..".
Sai yace mata"daman ba komai yasa na biyoki ba, agaskiya tun lokacin da na ganki soyayyarki ta shiga raina,shiyasa nace ba zanyi k'asa agwauwa ba,nace bari na zo ko Allah zai sa ki amshe tayina".Mariya ta rufe fuskarta da hannunta cikeda matsananciyar kunya ta kasa cewa uffan,ganin tayi shiru yasa Malam Kabiru yace" Mariya ki gayamin gaskiya tsakaninki da Allah idan na miki ki gayamin idan banyi miki ba ki gayamin..".Ya cigaba da bayaninsa"dan ni ba wani lokaci nake son aja ba da yake ban magabatar miki da kaina ba, ni sunana Kabiru kamar yadda kika ji wasu nacemin Kabiru Mai kayan miya inada mata d'aya da yarinya guda, idan na miki ki fito fili ki gayamin".Akunyace Mariya ta iya bud'ar baki tace"Eh na aminta..".
Bayan sunyi sallama ta shiga gida,sai ya wuce gida tun daga lokacin da soyayya ta shiga atsakanin Kabiru da Mariya,iyayenta suka shigo lamarin, ba da jimawa ba a kasa lokacin auren,lokacin da Innah Jummai taji labarin Kabiru ya fara neman aure ba k'aramin tashin hankali akayi shi da ita ba .Daga k'arshe dai da taga wankin wula zai kaita dare sai ta saduda,amma tasha alwashin kul ba jima kul ba dad'e sai ta ga bayan aurensu!Bayan wasu lokutta akasha bikin Kabiru da Mariya ta tare gidan Kabiru mai kayan miya, tasha k'auna da tsantsar soyayya awurin mijinta amma bata yi wata ba ta fara fuskantar tsana da tsangwama awurin Innah Jummai, domin ta girmeta nesa ba kusa ba,da yake ita Mariya marainiya ce D daman wajen k'anin mahaifinta take da zama har zuwa lokacin da suka aurar da ita,kuma daman ko agidan ba wani jin
dad'in zamanshi take yi ba,don dai ta kasance mace mai hak'uri ce da juriya,shiyasa duk cin kashin da ake mata take shanyewa, saboda bata da kowa sai shi k'anen mahaifin nata.Haka dai rayuwarta ta cigaba da tafiya bata jin dad'in zaman gidan Malam Kabiru, jin dad'inta guda saboda mijinta na sonta shekaranta guda agidan ta haifi 'ya mace aka sama d'iyar HAFSATU.
Bayan shekara biyar da haihuwar HAFSATU har yau ko b'arin wata bata sakeyi ba,ashe Innah Jummai ce ta bata wani magani awani lokaci da tace mata bata da lafiya, ashe wanda ke lalata mahaifa ne, to tun daga lokacin bata sake haihu wa ba daya ke abin ya zo da k'addarar ubangiji.
HAFSATU nada shekara shida Allah yayiwa Mariya rasuwa sanadin wani ciwon ciki da ta kwanta,aka wayi gari babu ita rashin da saida Malam Kabiru ya girgiza saboda yana matuk'ar son Mariya bana wasa ba,bayan wasu lokuta sai ya d'auki son duniya ya d'orashi akan HAFSATU, to tun daga lokacin da Innah Jummai ta ga haka ta bazama zuwa wajen bokaye,tasa aka sama k'iyayyar HAFSATU aranshi,tun daga lokacin komai ya lalace komi Innah Jummai keyi baya iya cewa komai ko tayi daidai ko ba daidai ba ne,juyashi agidan take yi yadda taga dama duk abinda tace shi za'ayi ko yayi masa dad'i ko bai yi masa ba,ko yana so ko baya so saboda Innah Jummai tafi k'arfinsa, wannan shine sanadiyar tab'arb'arewar farin cikin gidan Malam Kabiru mai kayan miya......
_Wannan shi ne tak'aitaccen tarihin HAFSATU._
_Ku biyo ni a page na gaba domin ku ji ko wa cece Hajiya Khadija..._
_Comments&Shares._
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.