💙💜💙💜💙
*LAIFIN SHI NE*
💙💜💙💜💙
_Na Maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
3️⃣7️⃣
Bayan sun sake gaisawa ne Mama Fatima tayi masa bayanin komai daya faru da wanda ta sani gameda Hafsatu,hajiya Fatima bayan ta k'are masa bayani ne take sanarda Malam Kabiru yau zasu koma gida,"sannan kuma ina son na rok'i alfarma akan zan dawo na d'auketa don na samar mata aiki,saboda ta kammalah karatu aiki kad'ai ne ya rage ta fara".Bayan ta gama yi masa bayani ne Malam Kabiru yaja numfashi yace mata"gaskiya hajiya na aurar da Hafsatu bada jimawa ba don wanda ya b'ata rayuwarta yazo guna ya rok'eni gafara, akan abinda yayi mata kuma na hak'ura to kinga kuwa zancen komawarta babu shi tunda akwai igiyar aure akanta,sai dai ina godiya da taimakon da kika yiwa d'iyata Hafsatu nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi hajiya,ubangiji yasa ki shiga aljanna asanadiyyar halinki na k'warai da tausayi". Hajiya Fatima taji dad'in addu'arsa gareta sai dai zancen auren Hafsatu yazo mata abazata kuma banbarakwai ajiyar zuciya ta safke tace" ameen to shikenan ba damuwa tundashi mutumen ya nemi yafiyarka ba matsalah da naso koni na had'a aurenta da d'ana Mansur, amma ba komai Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba Hafsatu".Ita dai Hafsatu tsabar rud'ani sank'arewa tayi awuri d'aya tunda taji anyi mata aure,auren ma arasa da wa za'a had'ata sai wanda ta tsana..!Har suka k'are maganarsu bata sani ba saboda ta afka cikin kogin tunani,saida hajiya Fatima ta mik'e tsaye ne taja hannunta tace"to ni dai d'iyata zan koma sai watarana idan na sake dawowa ganinki don auren da akayi miki,bazai sa ni jin bana son na cigaba da zumunci dake ba saboda ni tamkar d'iyata na d'aukeki,sai kuma idan kun tashi kaita sai akirani don kina da nombata data yayannki..".Jiki asanyaye Hafsatu ta marairaice fuska tace"'yan Mama tun yanzu zaku wuce..?".Hajiya Fatima ta saki murmushi kad'an tace"to Hafsatu daman kin san bada batun zamu kwana muka zo ba,don haka zamu wuce sai wata rana". Hafsatu tabi bayan hajiya Fatima cikeda rashin kuzari saboda sabo turken wawa ne,har k'ofar gida ta rakasu tana hawaye, saboda Hafsatu har ga Allah ta so tayi wata ta koma don ta fara aiki to gashi kuma taji wata magana banbarakwai, wai anyi mata aure haka dai Hafsatu tayi ta d'aga musu hannu har suka b'acewa ganinta,domin gashi komai basu ci ba haka ta juya ta koma gida zuciyarta cunkushe, ita kuma Innah Jummai firgici ne ya shigeta wai anyiwa Hafsatu aure, kuma da wanda ya b'ata mata rayuwa daman kenan wani ya lalata mata rayuwa,to koma minene dai nice silah don haka zanyi k'ok'arin na gyara kuren da nayi,ta hanyar janta ajiki na nuna mata k'auna ko Allah zai sa Kabiru ya yafemin kurakurren dana tafka asanadiyyar zugar k'awar banza Laure dillaliya......................
_Comments&Shares_
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.