LAIFIN SHI NE

5 0 0
                                    

💙💜💙💜💙

*LAIFIN SHI NE*

💙💜💙💜💙

_Na Maman Afrah Ik_

~Editing by Mugirat Musa.~

3️⃣5️⃣

Basu zarce kowane guri ba sai bakin masallaci Malam Kabiru mai kayan miya yasa akayi sanarwa,bayan mutane sun taru ne aka sheda musu cewar d'aurin aure ne za'ayi kowa kuwa ya bid'i waje ya zauna don an fiddo tabarmi an shimfid'awa jama'a,haka kuwa akayi Jalaluldeen ya d'auki sadaki ya bada dubu talatin aka shaidu suka shaida cewar ya biya sadakin Hafsatu,limamin garin shi yayiwa Jalaluldeen wakilci shida abokansa guda biyu,nan take aka d'aura masa aure da Hafsatu don ya bada dubu d'ari mahaifinta yace ya bada talatin albarka ake so acikin aure  ba tarin abun duniya ba,bayan an gama tdaurin aure ne aka aiki wani ya siyo dabino da guro dayake gefen masallacin akwai mai saidawa aka rabawa mutane,bayan kowa ya watse ne suka koma bakin k'ofar gidan Malam Kabiru suka k'ara tattaunawa akai,sukayi masa sha tara na arzik'i duk da dak'yar ya amsa, haka su Jamil sukayi masa sallama zuk'atansu cikeda farin cikin yadda auren yazo musu da sauk'i batare da wata matsala ba,musamman Jalaluldeen dayake jin zuciyarsa wasai tamkar anyi masa bushara da gidan aljanna,suka tafi kuma saida suka amshi nombar wayar Malam Kabiru domin koda zasu dawo sai su sanardashi, Jalaluldeen kuwa bayan gama d'aurin aure da akayi nashi yaji kamar ya sauke wani nauyi akansa, bayan sun koma gida basu isa da wuri ba sai k'arfe goma na dare, koda suka isa gida hajiya KHADIJA (momy)tuntuni ta shige d'akinta shiyasa basu bi ta zuwa gunta ba sunka yanke shawarar cewa sai da safe sa nemeta su gaya mata wanna abin alfahari da farin ciki,saboda shi Jamil yace masa daga yau gobe zai koma gida sunyi mai wuyar yanzu saura su dage da nemanta. Suna shiga d'aki ne sunka zauna koda suka bid'i waje suka zauna ashe momy ta aje musu abincin da zasu karya don sau tari idan sun jima basu shigo ba a d'aki take kai musu chan suke cinsa,haka kuwa akayi daman sun kwaso yunwa bayan kowanensu ya watsa ruwa ne suka baje suka cika cikinsu daga nan kuwa suka bid'i gado suka kwanta, sai muce Jamil da Jalaluldeen mu tashi lafiya,amma kan shi Jalaluldeen kan duniyar tunani ya lulah Allah yasa su ganta kar dai ace d'iyar mutane na cikin mawuyacin hali ko kuma ta rasa ranta, wannan tunanin yana fad'o masa arai ai kuwa baisan sanda ya mik'e tsaye ba ya fad'a toilet ya d'auro alwalah ya fara nafiloli har akayi kiran sallah bayan ya gabatar da sallar asuba ne,yana zaune yana jan tasbaha har barci ya d'aukeshi anan zaune,koda Jamil ya farka yaga yana sallah to shima sai yabi sahunsa bayan sun gama ne ya kishingid'a sai barci shima ya d'aukeshi shine bai farka ba sai karfe goma na safe,don bayan hajiya KHADIJA ta tashi ne koda ta shigo ta riskesu suna barci sai ta juya bata katse musu barcin ba,bayan sun farka ne kowa yayi wanka suka shirya suka fita zuwa gaida momy koda suka je sun risketa tana breakfast,suka gaidata suma suka zauna sukayi fara breakfast, bayan sun gama ne suka je saman kujerun parlour suka zauna anan ne ma suke gaya mata yadda sukayi da mahaifin Hafsatu domim basu ga Laure dillaliya ba mahaifinta muka samu ganawa dashi,domin dak'yar muka samu wadda tasan gidan ta nuna mana, bayan sun gama gaya mata ne take cewa"gaskiya na jinjinawa wannan uban na Hafsatu mai saurin yafiya,kuma har ya yarda nan take ya baka aurenta,gaskiyar magana masu imani irinsu k'aranci ke garesu kuma dattijon arzik'i ne,Allah yayiwa aurenku albarka Allah ya bayyana mana ita cikin k'oshin lafiya".....................

*Muje zuwa koya zata kaya idan Hafsatu ta dawo ta iske cewar Jalaluldeen ya zamo miji agareta,shin zata karb'eshi ne amatsayin miji ko kuwa akasin haka?Ku cigaba da bibiyata sannu ahankali zan warware muku zare da abawa.*

*Gaskiya comments d'inku yayi k'aranci idan bakuyi comments ba zan daina rubutawa don inaga baku buk'atar karanta cigabansa.*


_Yawan comments yawan typing._

_Comments&Shares_

LAIFIN SHI NEWhere stories live. Discover now