💙💜💙💜💙
*LAIFIN SHI NE*
💙💜💙💜💙
_Na Maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
3️⃣1️⃣
Laure dillaliya yanzu tace musu haka ne saboda tasan ko karen hauka ya cijeta bazata tab'a iya tunkararsu da zancen cewar Hafsatu ta b'ata ba,haka dai Laure dillaliya ta koma gida jikinta asab'ule,da yiyuwar ta sake dawowa ko zataga Hafsatu don harga Allah bazata iya tunkararsu dacewar d'iyarsu bata gidan aikin data kaita ba,domin tasan ba k'aramin tashin hankali zasuyi ba idan suka ji d'iyarsu ta b'ata, haka dai Laure dillaliya ta cigaba da sha'aninta har tsawon wasu shekaru awata k'asar daba tasu ba,dayake yanzu batada nauyin kowa akanta mijin nata ya k'are,shiyasa ta koma sana'arta wani gari babu wanda yasan inda ta shiga,Laure dillaliya sai dai tana dawowa asirince kaima wasu iyayen yara kud'ad'en aikatansu,har Laure dillaliya ta shigo ta koma basu tab'a gamuwa da Innah Jummai ba,don bata bari tasan ta shigo cikin gari,gefen Innah Jummai kuwa tayi zaryan zuwa gidan Laure dillaliya har ta gaji da zuwa bata riskarta,Innah Jummai tayi zuwa karb'ar kud'i bata ganinta sai dai ta riske gidan kulle da padlock akodayaushe, itama Innah Jummai rashin ganin Laure dillaliya yana damunta kuma abin har ya fara bata tsoro,domin ace kodayaushe gida arufe kuma tana jin mutane suna cewar tana shigowa garin nemanta ne kenan bata yi tabata hak'k'inta, gashi kuma taji cewar tana kaiwa iyayen saura kud'ad'en aikinsu,amma babu komai idan kere na yawo zabo na yawo wata rana za'a had'u cewar Innah Jummai azuciyarta, bayan barinta bakin k'ofar gidan Laure dillaliya ne ta shiga tambayarta a mak'wabta koda tana shigowa suka ce mata bata shigowa nan amma ki je gidansu Balkisu,domin ke san ta kai Ulaifa aikatau kuma duk bayan wata biyu tana zuwa kai masu kud'insu, to wata k'ilah zasu gaya miki ranar da take zuwa kai musu kud'in.Suna kammala yi mata bayanin komai Innah Jummai tayi musu godiya sosai, bayan tayi musu sai anjima Innah Jummai ta fita bata zarce ko'ina ba sai gidansu Balkisu,da sallama ta shiga cikin tsakiyar gidan mutanen gida suka amsa mata fuska asake,bayan sun gaisa ne suke tambayarta mi ke tafe da ita?Kuma tana son don Allah su gaya mata ko wace rana ce Laure dillaliya take shigowa gari?Bayan sun fad'a mata ne tayi musu godiya sannan ta nufi gidanta ak'untacce zuciyar Innah Jummai sai suya da k'una takeyi,gaba d'aya jikinta rawa yakeyi saboda tsananin b'acin rai,haka Innah Jummai tayi ta jiran zuwan Laure dillaliya cikin k'auyen kuwa,kwatsam wata rana ranar lahadi Innah Jummai tana zaune tana tsintar k'wari cikin wake!Aka turo yaro ya kirata saboda anga shigowar Laure dillaliya cikin k'auyen yanzun nan,Inna Jummai kafin d'an aiken ya gama magana tuni ta sab'a gyalenta ta fito da hanzari tana gaba yaron na abayanta,tsabar sauri kamar Innah Jummai ta fad'i don ko rufe gidan ma bata tsaya yi ba, daman shi d'akinta ma arufe yake tun lokacin data zauna, saboda kajin dake shigar mata d'aki suna caccakar buhun gero shine dalilin dayasa ta kulle d'akin,haka kuwa akayi koda Innah Jummai taje gidansu Balkisu Laure dillaliya na batun fita ta wuce sauran gidaje biyu suma takai musu kud'in aikin yaransu,Innah Jummai tana ganin Laure dillaliya jikinta ya kwashi rawar disko mi Innah Jummai zatayi idan ba chakumar wuyan Laure dillaliya ba,kamar daga sama Laure dillaliya taji an shak'o wuyanta,nan itama Laure dillaliya ta ruk'unk'umeta sukavfara bala'i,dan kuwa ita Innah jummai cewa ta fara yi amasifance"bak'ar munafuka shekara takwas kin cinye kud'in marainiyar Allah,don kina azzaluma maciyiyya amana kud'in ma hak'k'innmu bazaki kawomin ba,amma su sauran gidanjen kina kai musu na yaransu".Laure dillaliya ta tauni leb'e k'asa azafafe cikeda tijara tace"ko ke Jummai sakeni wallahi kar na kwad'a miki mari,idan ba kina mara imani ba ki yima 'yarki aure ki d'auke d'iyar kishiya kishiyar ma da bata raye ki mik'a akaita wata uwar duniya aikatau,wane irin rashin imani ya wuce wannan?Gashi sanadiyyar haka Hafsatu ta gudu daga gidan aikinta ma,suma masu gidan sun zata ma Hafsatu tayo gida shekara takwas ba Hafsatu ba labarinta, waya sani ma ko ta mutu saboda sakaci irin naki da rashin tsoron Allah, gashinan ai Allah ba azzalumin sarki bane domin gashi ya nuna miki akan d'iyanki!Waya tsira acikinsu itada Meri wadda kikayiwa aure, gashi cen ana azabtar da ita sanadin hak'k'in marainiyar Allah,don haka ki bazama neman d'iyar mutane kafin kabiru mai kayan miya ya sani don nasan in ya sani sai kinbar gidanshi..!".Laure dillaliya tana k'arasa sakin zautukkanta Innah Jummai kam ta kasa yin k'wak'k'waran motsi ta kasa cewa komai tsabar imani da tsananin mamakin daya cikata, ace Hafsatu bata gidan aikin da aka kaita har tsawon shekara kusan nawa,to ina ta je..? Laure dillaliya bata yi aune ba taji mari afuskarta Innah Jummai ce ta kwasheta da mari biyu,Laure dillaliya sai da ta d'auke wuta na wucin gadi sannan suka kachame da dambe suna bugun junansu cikeda k'iyayya da takaicin juna,daman sun fara tarawa kansu jama'a soasai kuwa mutanen k'auyen suka dinga taruwa kamar tururuwaa......................
_Comments&Shares_
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.