💜💙💜
*LAIFIN SHI NE*
💜💙💙
_Na maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
1️⃣1️⃣
Bayan ta fito daga cikin kitchen sai ta fara zuwa d'akin hajiya KHADIJA, domin ta gyara mata d'akinta koda ta shiga hajiya Khadija na zaune bakin tangamammen gadonta zaune ta hakimce,tana saka sark'arta ta gwal awuyanta,da sallam ta shigo hajiya Khadija ta amsa mata dak'yar kamar an matsi bakinta, har k'asa Hafsatu ta duk'a tace"hajiya ina kwana..? Hajiya Khadija ta bintsire baki tace"lafiya...".Kawai tace mata,hajiya Khadija ta tashi ta fita ta bata waje domin ta fara gyaran nata kafin taje ta gyara na yaranta guda biyu,ban da room d'in mijinta domin ba taba ta izinin shigowa har cikin d'akin mijinta ba,komai k'asaitarta ita ke shiga ta gyarawa mijinta shimfid'arshi,shiyasa Alhaji ke matuk'ar son matarsa saboda in dai ta gefen kula dashi ne bata wargi,bayan ta kammalah gyaran gado ta share d'akin ta mofeshi, sai ta shiga cikin toilet shima ta gyarashi da yake Iya Luba duk ta nuna mata yadda zata yi kowane irin aiki,shiyasa tayi komai atsanake kuma tasa ba da aikin gidansu shiyasa bata ji komai ba.Sai dai na nan da na gidansu akwai banbamci nesa ba kusa ba,shiyasa ta jigata sannan ga kuma rashin sabo,bayan ta kammalah gyaran d'akin hajiya KHADIJA sai ta shiga d'akin Zainab shi mata gyarashi ta goge komai don ita Zainab koda ta fita cin abinci ma bata san da mai gyaran d'akinta ba,bayan sun kammala breakfast momy take gaya mata cewar" to yanzu ki daina yimin k'orafin mai aiki na samo muku mai gyaran d'akunanku kinji..". Saboda tsabagen murna saida Zainab ta rungume mamanta cikin shagwab'a tace"momy mun gode sosai I love you so much momyna".Cikin jin dad'in ganin farin cikin Zainab hajiya KHADIJA tace"love you too ki jayemin can karki k'arasa ni..".Farin ciki bayyane afuskarta Zainab ta janye jikinta ana mahaifiyarta cikeda tsananin annushuwa.
Ita kuma Hafsatu bayan ta gama gyaran d'akin Zainab,sai ta shiga na Jalaludeen da yake baya gari koda ta shiga gaskiya akwai datti sosai acikinsa shiyasa ta dad'e tana gyaranshi, kafin ta kammalah ta wuce in da hajiya kadyija ta gaya mata ta gama, bayan ta gaya mata sai tace ta wucewarta shine kad'ai aikinta sai dai idan tana nemanta zata sa akirata, bayan Hafsatu ta fita d'akin hajiya KHADIJA bata zarce ko'ina ba sai wajen Iya Luba koda taje Iya har ta fara girkin rana, sai ta mik'a mata abincinta ta zauna nan zata ci Iya Luba tace"a'a Hafsatu tashi ki je d'akinki ki ci kar hajiya ta fito ta ganki tayi fad'a don bata bari ayi mata zaune a kitchen cin abinci,sai dai mutum yaje d'akinsa ya ci kin ga za ki fi ma sakewa..". Hafsatu bata ce komai ta mik'e tsaye sai Iya Luba ta mik'o mata ruwa ta wuce d'akinta,da yake ita ta riga ta saba da rashin cin abinci da wuri shiyasa bata damu ba, don can ka'uyensu ko ta girka watarana sai anga dama ake bata ma,shiyasa da ta kai sha d'aya ba tayi kari ba bata ma damu ba,bayan ta je d'akinta ta zauna taci abincinta sai tayi zaune tana tunanin rayuwarta alokacin da ta ke gidansu wurin Innah Jummai...........
_Comments&Shares._
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.