LAIFIN SHI NE

13 0 0
                                    

💙💜💙💜💙

*LAIFIN SHI NE*

💙💜💙💜💙

_Na Maman Afrah Ik_

~Editing by Mugirat Musa.~

2️⃣8️⃣

Bayan Dr.Mansur ya koma gida ya sanarda mahaifiyarsa hajiya Fatima komai ake ciki,cikeda jimami hajiya Fatima ta rik'e hab'a tace"son don't worry insha Allah zan kula da ita".Dr.Mansur yace"wallahi Mama ina tausayawa rayuwar Hafsatu saboda wanda yayi mata fyad'e ya cuci rayuwarta da kimarta"."Hmm Mansur ai wannan rayuwar da kake gani marasa imani da tsoron Allah sunyi yawa acikinta..".Dr.Mansur ya musk'uta yace"haka ne gaskiya amma naso ace ta san ko waye yayi mata fyad'e,da sai na shige mata gaba an bi mata hak'k'inta..".Hajiya Fatima ta jinjina maganar aranta tace"ka ce bata san ko waye yayi mata fyad'e ba,ta yaya al'amarin ya kasance haka..?".Dr.Mansur ya safki nannauyar ajiyar zuciya yace"Mama ita ta fad'amin cewar bata san ko waye ba,wata k'ila wanda yayi mata fyad'en saida ya gusar mata da hankali yayi mata fyad'e..".Hajiya Fatima ta nisa tace"tabbas lahira akwai shari'a,son kaje kayi wanka kaci abinci..".Dr.Mansur yace"haka ne Mama okay bari in je apartment d'ina..".Yana rufe bakinsa ya mik'e tsaye directly ya nufi room d'insa,hajiya Fatima ta k'udurta azuciyarta zata kula da Hafsatu kuwa tamkar ita ce mahaifiyarta,da garin ya waye bayan sunyi breakfast sun shirya Dr.Mansur ya je da mahaifiyarshi domin kulawa da Hafsatu,koda suka je kuwa Hafsatu ta farka suna shiga,Hafsatu ta gaidata daga kishingid'en da take don tana iya zama sai dai ba'a son tana yawan dogon motsi shiyasa da Maman Dr.Mansur ta nemi waje ta zauna,ita ta had'a mata tea mai zafi Hafsatu ta sha taji dama-dama acikinta,shi Dr.Mansur kallon tausayi yayi mata yace"ya jiki..?".Cikin muryar rashin lafiya Hafsatu tace masa"da sauk'i..".Dr.Mansur ya juya b'angaren Hajiya Fatima yace mata"Mama kinyi waya da Momy Hafsat..?".Hajiya Fatima ta jijjiga kai tace"nayi waya da ita akan zata zo anjima d'an Momy Hafsat".(I'm sorry please my fans Momy Hafsat k'anwar hajiya Fatima ce,uwarsu d'aya ubansu d'aya da hajiya Fatima,ta nunawa Dr.Mansur soyayya da gata tun yana yaro,ta k'aunaceshi tamkar ita ce ta haifesa shiyasa yake karrama duk wata mace mai suna Hafsatu saboda k'auna da soyayyar da momynsa Hafsatu ta nuna masa arayuwarsa).Daga k'arshe Dr.Mansur fita yayi domin yayi dubiyar patient's d'in da yayiwa aiki,bayan ya dawo wurin Hafsatu ya tsura mata idanuwa yana kallonta lura da tayi ya k'ureta da kallo shiyasa Hafsatu ta gaidashi domin tana ganin kirki darajarsa sosai,wanda ya d'auko mahaifiyarshi don kulawa da ita to idan ba mutumen kirki ba wa zai yi mata haka?Da yake ita Mamanshi ta gaya mata ita ce mahaifiyarshi,suna fira jefi-jefi atsakaninsu ba'a jima ba aka kira hajiya Fatima awaya tayi receiving call tana kwatancen room d'in da aka kwantar da Hafsatu,tana gama wayar da minti biyar aka turo k'ofa d'auke da sallama,suka kalli k'ofar tare da amsa sallamar muryar hajiya Hafsatu ce ta doso wurin yayarta tana cewa"Aunty gani na k'araso ashe wurin babu wuyar ganewa"."Hmm Mominsu akowane lokaci kina yawan zuwa asibitin d'anki amma kike tunanin bazaki gane a wane d'aki muke ba..".Cewar hajiya Fatima k'ayataccen murmushi hajiya Hafsatu ta saki tace"ko ban gane ba ai d'ana zai zo ya kawoni..".Dr.Mansur ya zo gab da hajiya Hafsatu ya gaisheta yace"Momy ina wuni yasu Mansura..?".cikeda tsabtatacciyar k'auna hajiya Hafsatu ta shafi fuskar Dr.Mansur tace"duk suna lafiya doctor but momintaka tayi fushi da kai..".Ashagwab'e Dr.Mansur yace"afuwan Momy laifin mi nayi miki..?"."Kwana biyu ka daina zuwa gaisheni ban san laifin mi nayi maka ba,su Mansura sai damuna suke yi a ina kake miyasa ka daina zuwa..?".K'eyarsa ya shafa jiki asab'ule yace"I'm so sorry my lovely Momy ayyukan asibiti ne suka yimin yawa shiyasa kwana biyu na daina shigowa" .Numfasawa hajiya Hafsatu tace"to ka dinga k'ok'artawa kana shigowa saboda sada zumunci abu ne mai matuk'ar muhimmanci ga kuma lada".Dr.Mansur yace"insha Allah zan kiyaye Momyna"."Good doctornah may God bless you".Fad'ar hajiya Hafsatu hajiya Fatima ita ce ta gabatar da Hafsatu ga k'anwarta hajiya Hafsat, Hafsatu ta gaisheta cikeda girmamawa sannan suka zauna suka bata labarin suk ire-iren k'alubalen da Hafsatu ta shiga kamar dai yadda ta gayawa doctor Mansur,alal hak'ik'a hajiya Hafsatu ta tausaya mata matuk'a tareda jinjina al'amarin aranta,bayan sun kammala firarrakinsu Dr.Mansur ya taimaka ya gyarawa Hafsatu zama,hajiya Hafsatu ta bata magunguna tareda abincin da ta zo dashi,Dr.Mansur sai ya koma office d'inshi don cigaba da lura da patient's d'insa,dayake ita Mama Fatima tabar mai aikinta tayi mata girki don saida ta nuna mata komai sannan suka fito,kuma ta gaya mata cewar zata kawo mata wadda zasu yi lunch dashi,haka dai Hafsatu tayi jinya har na tsawon sati d'aya mahaifiyarshi da k'anwarta hajiya Hafsatu suke kulawa da ita,dayake shi kad'ai Allah ya bata kuma mahaifinsa ya rasu shiyasa ta d'auki son duniya ta d'ora akansa, azaman jinyar datayi na Hafsatu ta sake tambayarta ita wacece kuma tayi mata alk'awarin zata zauna da ita amatsayin d'iyarta zata rik'eta tamkar d'iyar da ta haifa.

Bayan wata biyu lokacin Hafsatu ta warke garau baza kace itace ba,don Mama da Momy Hafsatu sun siya mata sutura kusan kaloli fiyeda talatin na sawa,don ita hajiya Fatima a d'iya ta d'auketa ba 'yar aiki ba,shiyasa idan kaga Hafsatu tayi k'iba tayi k'yau ba d'an kad'an ba,wata rana ne bayan sun je cikin gari sun dawo ne take cemata"Hafsatu gobe Monday zaki fara zuwa makaranta,amma daga aji biyar zaki fara don kinyi girma sosai".Haka kuwa akayi washe garin ranar Monday Hafsatu ta fara zuwa makaranta babu kama hannun yaro, kuma tana maida hankali  sosai wurin karatu don bata wasa,saboda babban burinta shine tayi ilimi haka rayuwar Hafsatu keta tafiya wata rana datdi wata rana akasin haka domin duk yadda kake wata rana sai kayi laifi ko yaya ne, amma duk da haka suna matuk'ar nuna mata so bana wasa ba, haka rayuwa ke tafiya har gashi ta kammalah secondary school tana batun shiga gaba da secondary school, lokaci-lokaci Dr.Mansur yana yawan kaita ziyara wurin momynsa Hafsatu saboda akowane lokaci cikin ambaton sunan takwararta take,kuma alokacin ta zama budurwa sosai don shekarunta sun kai na cikakkar budurwa ko yanzu aka aurar da ita zata zauna gidan mijinta, ga gefe guda kuma sun shak'u da Dr.Mansur fiye da tunanin mai karatu domin zamu iya cewar soyayya ce ba shak'uwa ba..

B'angaren Jalaluldeen kuwa ko shekara da tafiyar Hafsatu ba'a yi ba ya kamu da tsananin sonta,da kuma tausayinta don koda yaushe idann ya kwanta sai yayi mafarkinta baida tunani sai nata akodayaushe,nan take wata irin mahaukaciyar soyayya da k'aunar Hafsatu tayi masa kamun kazar kuku duk ya gigice ya rasa a ina zan tsoma zuciyarsa yaji sanyi.........................


_Comments&Shares._

LAIFIN SHI NEWhere stories live. Discover now