💙💜💙💜💙
*LAIFIN SHI NE*
💙💜💙💜💙
_Na Maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
2️⃣0️⃣
Bayan Hafsatu ta kammalah karatunta, sai ta imike ta gabatar da sallar azahar data k'are sai ta fita taje sashen hajiya KHADIJA,domin ta gaida Alhaji Abubakar mai gishiri daya dawo daga tafiyar da yayi, bayan Hafsatu ta gaida shine taje ta cigaba da ayyukanta kamar yadda takeyi wasu lokutan in an sakata aikin marece, dayake bata cika yawan aikin marece ba sosai shiyasa bata k'arasa aikin ne ba ta je ta cigaba da bitar karatunta,har dai tsuwa marece data tashi shiga barci sai da ta rufe d'akinta don gudun kada yaya Jalaludeen ya shigo mata d'aki, saboda ita ganin da takeyi idan jarabarsa ta ciyoshi zai iya biyota koma ina ne, shi Jalaludeen ba ruwanshi don yadda ta lura da d'an fahimtar halayyensa kunya ba ta cikin lissafinsa,shiyasa yake tab'ata son rasa ko tsoron Allah ubangiji ba yaji.
B'angaren Hajiya KHADIJA kuma bayan sunyi fira da yaranta,da mai gidan nata wanda tafi so fiye da komai arayuwarta bata had'ashi da kowa ba, bayan yaransu sun shige sashensu,sai hajiya Khadija ta matso gun mijinta ta k'ara rungumeshi cikeda annushuwa da tsantsar farin ciki mara misali tace"gaskiya nayi missing d'inka da yawa fa uban 'ya'yana".Alhaji Abubakar ya saki k'ayataccen murmushi mai kwantarwa mutum da zuciya yace"hajiya dai baki tsoron yaran namu su dawo su riskemu ahaka,kin san fa mun tsufa yanzu".Hajiya Khadija ta langwab'e wuya cikin sagarci tace"a'a kam Alhajina ko mun tsufa soyayyarmu ai bata tsufa ai,kuma ina son idan ka huta mu tattauna maganarsu Zainab akan baza tafi wata d'aya ba ta kammalah karatunta, shiyasa nake son bayan wata biyu da k'arewarta ayi bikinsu don hankalina zai fi kwanciya,idan har muka wanketa..".Bayan ta nisa da takai k'arshen zancenta,shi dai Alhaji Abubakar mai gishiri shiru yayi ya kashe kunne yana sauraron bayanenta sai da ta k'arasa zancen sannan yace"ba matsalah yanzu ki tashi mu shiga daga cikin,idan Allah ya nuna mana gobe lafiya sai mu tattauna komai yadda ya kamata..."Jijjiga kai hajiya KHADIJA tayi tace"ba damuwa Alhaji ubangiji ya kaimu goben lafiya"."Ameen Hadizatuwanah"..Alhaji Abubakar mai gishiri ya fad'a azolaye,atare suka mik'e tsaye suka nufi b'angaren apartment d'in daddy Abubakar mai gishiri,hajiya KHADIJA ta sake kakkab'e zanen gado ta shimfid'a.Sannan suka yi addu'o'i suka shafa ajiki sukayi shirin barci suka bi lafiyar gado......................
_Comments&Shares._
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.