LAIFIN SHI NE

6 0 0
                                    

💙💜💙💜💙

*LAIFIN SHI NE*

💙💜💙💜💙

_Na Maman Afrah Ik_

~Editing by Mugirat Musa.~

4️⃣1️⃣

Haka zamansu Jalaluldeen ya kasance baby yabo babu fallasa, domin ko yayi mata magana bata kulashi amma tana yi masa girki iri-iri kala daban-daban,saboda  idan ta tuna hud'ubar mahaifinta sai taji kamar ta yafe masa,kuma sai ta kasa haka dai zaman nasu yake ta gyara muhallinsu tareda masu yi mata aikin gida, saboda bata yarda ta zauna bata komi ba dan ko girki ita keyiwa mijinta,Hafsatu bata bari mai aiki tayi mata komai, haka dai ranar Hafsatu tana zauna tana gyaran akaifa,sai gashi Jalaluldeen ya shigo cikin gidan da sallama na amsa sai na gaidashi, don yanzu na sauko ina gaidashi bayan ya zauna saman kujeran dake facing d'ina sai ya mik'omin wani ambulof yace" gashinan na samar miki aiki a kotun jaha acan zaki rik'a aikinki".Ai kuwa Hafsatu bata san lokacin da ta mik'e tsaye ba,ta fara murna saida tazo har kusa ga jikinsa ma bata lura ba,shi kuwa Jalaluldeen gogan naku sai murna ta kamashi domin harga Allah yana son ya ganta cikin farin ciki,gashi kuwa ya ganta amma har alokacin idan ka ganshi zakaga har yanzu bai maida jikinsa ba,saboda damuwa dan babban burinsa shine tace ta yafe masa amma abin yaci tura,haka Jalaluldeen ya tashi ya shige d'akinsa jikinsa amace,bayan Hafsatu ta gama murna ne ta bud'e ambulof ta fara karantawa bayan ta gama karatun ranar monday zata fara fita office d'in nasu, haka kuwa ce ta kasance da ranar monday  tazo ta fara fita aikin nata, Jalaluldeen shi yake ajiyeta abakin k'ofar get d'in kotun,dayake mace ce mai basira da hazak'a shiyasa data fara aikin cikin aminci kuwa ta rik'a samun nasara,haka dai Hafsatu takeyi ta rayuwa da mijinta har tsawon shekara d'aya babu wani jituwa ko soyayya atsakaninsu,wata ranar da bazan tab'a mancewa ba itace ranar da wanda ya bat'amin rayuwa wato mijina Jalaluldeen ya k'ara neman yafiyana,ni kuma Hafsatu naga wahala kuma na jigatar dashi sosai, saboda babu mai iya hak'urin nakkasa da sharewa matarsa sai shi,kuma har a idanuwansa na fahimci cewar tabbas yayi matuk'ar nadama kuma ya shiryu,shiyasa nace masa na yafe masa tsabar farinciki da tsantsar annushuwa ta bayyana afuskar Jalaluldeen banyi tsammani ba naji ya rungumeni yana hawaye yana yimin godiya, saida ya bani tausayi matuk'a domin abinda yasa na yafe masa shine naga dai ya tuba,kuma a k'ark'ashinsa nake har ayanzu idan ban yafe masa ba ban san wane irin rayuwa zai k'ara shiga ba,don naga ya tuba haka dai sukayi ta gudanar da rayuwarsu gwanin sha'awa cikin soyayya,k'auna,kulawa da tarairayar juna domin idan kagansu yanzu kaga yadda suke gudanar da rayuwar aurensu sai sun burgeka kamar basu ba,kamar basu tab'a fuskantar wani k'alubale ba aduniyarsu,wani lokacin Hafsatu tana zaune Jalaluldeen ya dubeta cikeda tsagwaron k'auna yace mata"kije ki shirya zamu je wani unguwa".Hafsatu ta saki murmushi mai k'ayatar da fuskarta tace"okay dear".Haka Hafsatu taje ta shirya sukafita basu tsaya kowane wuri ba sai wani had'ad'd'en gida dayake iya saninta basu zuwa kowane wuri bayan gidan iyayensa,sai kuma gidansu Jamil amininsa shiyasa da taga sun tsaya sai tayi mamaki, haka yaja hannunta sai cikin gidan suna shiga wa zata gani illah mahaifinta kuwa da Innah Jummai,cikin wani k'ayataccen parlor zaune suna karyawa tsabar murna da gudu taje ta rungume mahaifinta, sannan ta koma ta rungume Innah Jummai tace"baba yaushe kuka dawo cikin gari?Shine gashi ko d'azu munyi waya bakacemin zaku shigo ba". Malam Kabiru mai kayan miya yace mata"d'iyar albarka ko mu mijinki ne yayi muna bazata shine ya sai muna wannan gidan da kika ganmu ciki,ki tayamu yi masa godiya tunda mu ya hana muyi masa".Saboda tsabar murna Hafsatu taje wurin Jalaluldeen ta rungumeshi tayi ta murna tanata godiya saida ta gaji don kanta ta tsagaita,haka suka sha fira dayake yau basuda wani case ne akotu shiyasa suka wuni sai magariba suka wuce sukayi musu sallama suka koma gidansu.Haka dai rayuwarsu tayi ta tafiya gwanin ban sha'awa,yau da gobe sai Allah kawai sai ga cikin Hafsatu ya girma,wani lokaci suna zaune suna yin lunch sai Jalaludeen yace mata"ki shirya muje asbiti adibar min ke ina tunanin  ciki be gareki,wannan irin k'aton ciki haka".Hafsatu ta shagwab'e fuska tace"ni banida wani ciki dear zolayata kawai kakeyi". Jalaluldeen ya shafi kumatunta yace"naji bakida komai sweety amma ki tashi muje asibiti sai araba gardama".Ai kuwa zanje domin in gasgata zancenka ko akasin haka".Hafsatu ta fad'a tana sakin k'ayataccen murmushi,haka kuwa taje ta shirya suka je akayi mata gwaji kuwa sakamakon ya nuna ciki gareta harna tsawon wata biyar kosu saida sukayi mamaki,saboda basu tab'a zaton tanada ciki ba ko shi Jalaluldeen hasashe ne kawai yayi akan yaga cikinta nata girma,kuma bayan sun fito ne takece masa"my dear ciki gareni daman ana ciki ba laulayi ba komai?".Jalaluldeen ya dubeta cikin tsabtatacciyar k'auna yace"to baby ta yiyu namu ne Allah ya bamu ba mai wahalarmin dake ba,Allah ya raya manashi".Tare suka karb'a da amin haka suka je gidansu fuskansu k'unshe da tsananin farin ciki da murna mara misaltuwa,Jalaluldeen bakinsa yana rawa yasanar da mahaifansa da nata iyayen, bayan sun fito ne ya zarce da ita sai gidansu chan suka wuni sai dare suka dawo bayan sun ci abinci tuwon shinkafa da miyar d'anyar kub'ewa.

B'angaren Dr.Mansur kuwa matarsa Mansura ta haifu tuni har ma ta kusa yaye d'iyarsu da suka samu mai suna Hafsatu,asanadiyyar k'auna da soyayyar da yakeyiwa Hafsatu Kabiru shiyasa ya sanyawa 'yarsa sunanta,da nufin yayiwa k'anwar Mamansa Hafsatu takwara Innar Mansura,shiyasa Mansura bata gano dalilin dayasa Mansur ya sakawa 'yarta sunan tsohuwar budurwarsa ba.................................

_Comments&Shares_

LAIFIN SHI NEWhere stories live. Discover now