LAIFIN SHI NE

8 0 0
                                    

💙💜💙💜💙

*LAIFIN SHI NE*

💙💜💙💜💙

_Na Maman Afrah Ik_

~Editing by Mugirat Musa.~

2️⃣1️⃣

Bayan sun shiga barci ne Alhaji Abubakar mai gishiri yake ce mata"idan gari ya waye zai je gun k'anensa Ibrahim tare da ita dan su tattauna batun aure"."Da yake mahaifiyarmu kinga shekararta biyu da rasuwa ban da gobe ne zata cika shekara biyu da rasuwarta,ina son muyi shirin zuwar mata sadaka da taimakawa  marayu kamar yadda muka saba kodayaushe, muna zuwa gidan marayu muna musu k'yauta dan Allah ya k'ara kai haske cikin kabarinsu".Jinjina zancen hajiya KHADIJA tayi aranta tace "to shikenan Allah ya tashemu lafiya Alhaji,gaskiya kayi tunani mai amfani ubangiji ya jik'ansu Innah". Alhaji Abubakar mai gishiri ya safke ajiyar zuciya yace"Amin Hadizatu".Bayan sun yi addu'ar shiga barci sai muce Allah ya tashesu lafiya.

Da garin ya waye Alhaji Abubakar mai gishiri sun je masallaci shi da Jalaluldeen,bayan sun dawo suke tattaunawa akan aikin da yaya Jalaluldeen zai fara yi, Alhaji Abubakar mai gishiri ya numfasa yace"on next monday zaka fara hallatar office d'inka,tunda yanzu ka kammalah karatunka kuma gashi an kammala komai,ya kamata ka fara zuwa ka gudanar da komai da kanka,duk da yake an zuba ma'aikata yanzu cigaba ne kawai zaka yi komai da kanka zaka dinga yi".Cike da sanin daraja da kimar mahaifinsa Jalaluldeen ya sunkuyar da kai yace"nagode daddy ubangiji ya k'ara arzik'i da nisan kwana"."Ameen Jalal karka damu yiwa kai ne aduniya idan ban tallafa muku ba kai da Zainab,ai dukiyar da nake tak'ama da ita ta zama ta banza"."Haka ne daddy shiyasa akowane lokaci nake alfaharin samunka amatsayin mahaifi,domin kana k'ok'arin ganin ka k'yautatawa rayuwarmu.."."Wajibi ne ga duk uba nagari ya tsaya tsayin daka domin ganin ya tallafi rayuwar iyalinsa har su mik'e da k'afafunsu,ta yadda ko uban baya raye 'ya'yan ba zasu tab'a tagayyara ba kuma ba zai bar baya da k'ura ba".Jalaluldeen ya nisa yace"zancenka dutse ne ya mahaifina..".Bayan sun yi fira sun k'are ne kowa ya wuce sashensa yin wanka,saboda zuwa anjima zasu halarta a parlor dukansu suyi lunch,Jalaluldeen daya koma d'akinsa mararsa ta fara masa ciwo domin rabonsa da mu'amala da mace tun daya baro k'asar waje,shiyasa ma yanzu yake fama da sha'awa ba don yana tab'a jikin Hafsatu mai aikinsu ba yana rage zafi da abin yayi masa yawa, dak'yar yake fitar da numfashin wuya hannunsa dafe da mararsa yana lumshe idanu yana bud'ewa can yace"amma to ni ina yarinyar nan ne ta shiga, don yau naji ma su daddy na batun fita, Allah ya bani sa'arta in cika burina akanta dana d'auka tun ranar dana ganta naji ina jin bala'in sha'awarta..".Yana ida kalamansa ya kishingid'a saman gado yana saukar da numfashi kad'an-kad'an.B'angaren Hafsatu kuma bayan ta tashi daga wani irin mummunan mafarkin da tayi,wai tayi mafarkin yaya Jalaluldeen ya biyota da bindinga zai kasheta idan bata amince ya kwanta da ita ba,ita kuma Hafsatu ta iya tsaya yi masa gardama shine ya hasala ya buga mata kan bindingar,shine dalilin dayasa Hafsatu ta farko da kuwwa arazane tana rok'onsa kada ya kasheta dukkanin ilahirin jikinta ya sharce da zufa,agaggauce ta fad'a cikin toilet ta yo wanka jikinta sai k'yarrma yakeyi  tana ta ambaton kalmar inna lillahi wa inna ilaihir raji'un...! Wannan kalmar Hafsatu tayi ta maimaitawa har taji ta d'an samu natsuwa da sukuni,ta samu ta gabatar da ibada kamar kodayaushe,sannan Hafsatu ta tafi ta taje sukayi aikinsu suka kare ta d'auke nata breakfast taje tayi karin kumallo, bayan ta k'are ne hajiya Khadija ta kirata tace mata ta shiga d'akin Zainab da azahar ta d'auko kayan wankinta tayi mata shi,domin yau ta fita da wuri saboda paper garesu da safe, bayan Hafsatu ta wuce ne  kamar da k'arfe sha biyu 12:00am taji fitarsu daga gidan,sannan tana zaune Iya Luba ta zo tace mata zata je dubiyar marar lafiya agidan k'awarta zuwa hud'u zata dawo,ki tsare gida kinji jikata,ita dai Hafsatu duk jikinta asanyaye yake bata san komai yasa ba cikin dauriya da mutuwar jiki Hafsatu tace mata"to Iya sai kin dawo".Iya Luba cikin k'auna ta shafi kanta tace"ki kwantar da hankali zan dawo akan lokaci".Rufe bakinta keda wuya Iya Luba ta janyo mayafinta na tsoffi ta yaba ta fice daga cikin harabar gidan,bayan fitar Iya Luba da kamar awa d'aya Hafsatu taje tayi sallah,ta nufi b'angaren sashensu Zainab zuwa wajen d'auko kayan wankin da aka sakata domin wasu lokuta tana yi mata wankin,idan mai wankinsu bai zo ba ta gifta kenan zata shiga d'akin Zainab,ashe Jalaluldeen yana lab'e gefe yana lura da duk wani motsinta kamar daga sama taji an janyota da k'arfin gaske, Hafsatu tayi kichaniyar k'wace kanta amma ta kasa saboda bata tantance ko waye ya kawo mata farmaki ba,aka kai Hafsatu sai cikin d'akin Jalaluldeen, koda ta dawo cikin hankalinta sai taga Jalaluldeen ne..!Ai kuwa jikinta nan take ya fara b'ari da rawar tashin hankali tsoro da tsananin zullumi ne ya bayyana k'arara afuskar Hafsatu,shi kuma Jalaluldeen ya jefata agadonshi da sauri ya je ya kulle d'akinsa dayake gidan yanada tazara da kowane b'angare shiyasa ba lallai bane komai kakeyi ajika ba,bayan Jalaluldeen ya hawo saman gado ya zo kusa gareta yana sakin murmushi wanda ake kiransa dana mugunta sai yace mata"yarinya kenan kin gama guje-gujenki gashi yanzun nan kin shigo hannuna don haka yau miki abinda nake so sai yadda nayi dake babu mai k'watarki ahannuna..!".............


_Comments&Shares._

LAIFIN SHI NEWhere stories live. Discover now