💙💜💙💜💙
*LAIFIN SHI NE*
💙💜💙💜💙
_Na Maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
2️⃣7️⃣
Domin ta san ba komai zaka gayawa wani ya taimakeka ba,ita kuma Hafsatu tana son ta samu wanda zai taimaketa tayi karatunta,domin ta tsayu akan k'afafuwanta ta taimakawa mahaifinta Malam Kabiru mai kayan miya,shiyasa ma data bar gidansu Jalaluldeen bata koma k'auyensu ba don tana son ta zamo abin alfahari da koyi a k'auyensu,bayan Dr.Mansur ya sake ce mata"zaki iya gane wanda yayi miki fyad'e ne..?". Adalilin taddo mata da mikin dake cikin zuciyarta nan take wani irin narkakken k'unci ya manaye mata ruhi da jinin jikinta,gabanta ya fad'i daya tuna mata da wanda ya b'ata mata rayuwa,bata ce masa komai ba sai da ya sake tambayarta ne,saboda tun d'azu daya fara mata tambaya ta fara hawaye balai anzo inda yafi mata ciwo arayuwarta,haka dai Hafsatu ta daure tare da danne tuk'uk'in bak'in cikin dayake manne aranta,ta bashi labarinta amma ta b'oye masa cewar gidan aikin ne akayi mata fyadye don tasan wasu zasu ce sai an shigar da k'ara a kotu, ita kuma ba wannan ne agabanta ba ilimi ne take son tayi saboda ta taimaki iyayenta da kuma 'yan k'auyensu, bayan ta gama masa jawabi ne take ce masa ita batasan ko waye ba, an aiketa ne cikin gari dayake marece ne sosai hanyarta ta dawowa ne taji anjata sai cikin mota, ita dai daga nan bata sake sanin mi ya faru ba, sai da ta farka ne ta ganta a wani kango gudun kar na tashi na biyo hanyar komawa gidan aikin nawa, na kwashe kayana domin na gudu nabar wannan gidan, saboda sanadinsu ne aka b'atamin rayuwa, bayan ta gaya masa komai ne ,Dr.Mansur yake ce mata "Allah ya tsare gaba kuma nayi miki alk'awari zan yi miki aiki,na kuma taimakeki". Bayan Dr.Mansur ya fita ne daga d'akin ya koma office d'inshi ne yasa wasu nurses suka had'a masa komai dayake buk'ata na aikinsa ne,kayayyaki ne wanda zai mata aiki da suwa yasa kuma aka shigar da ita Hafsatu d'akin da akeyiwa mutane d'inki ko tiyata da dai sauransu, bayan wasu awoyi an kammalah komai ne yaje yayi mata allurar barci da kuma ta kashe rad'ad'i in anawa mutum aiki,haka yayi mata aikin cikeda k'warewa ya k'are mata shi lafiya sai dai fatar Allah ya k'ara bata lafiya, Allah ya k'ara tsarewa kuma bayan an maidata d'akinta ne aka kwantar da ita,shi kuma Dr.Mansur ya fita yabarwa masu kular masa da ita,don shi lokacin tashinshi yayi yana son ya koma ya turo mata mahaifiyarsa, don ta cigaba da kulah da Hafsatu dayake Mamansa mai suna hajiya Fatima mace ce mai halin k'warai mai tausayin na k'asa da ita, da kuma tausayin talakawa sosai bata tab'a raina d'an adam ba domin tasan kima da darajar d'an adam arayuwarta......................
_Comments&Shares._
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.