💙💜💙💜💙
*LAIFIN SHI NE*
💙💜💙💜💙
_Na Maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
3️⃣3️⃣
Fitar Jalaluldeen keda wuya bai zarce kowane gu ba,sai wajen abokinsa Jamil ya natsu ya gaya masa yadda yayi da iyayensa,ya furzar da iskar bakinsa cikin tarin damuwa yace"na rasa ina zan tsuma zuciyata naji sanyi,na rasa mi yake yimin dad'i aduniya,don yanzu haka ma su hajiya sun d'auki zafi dani asanadiyyar fyad'en dana yiwa Hafsatu,Jamil fiye da yadda baka tunani saboda na zata idan na sanardasu zasu tayani nemanta ne,sai gashi fad'a musun dana yi ya k'aramin damuwa fiyeda da,don Allah ya gani na zata zasu yimin fad'a ne daga baya su sa ayi nemanta,to yanzu zancen da nakeyi maka ni zanyi nemanta da kaina domin sun bani lokaci mai d'an tsawo, amma rashin ganinta shine babbar damuwa agareni,kanaga ta ina zamu fara ne Jamil don nidai na rasa mafita tunanina duk ya k'ulle wuri d'aya,na rasa yadda zanyi inda ko momy ta saurareni da zan tambayeta ko wane gari ne wadda ta kawo mata yarinyar take,kaga nemanta zai muna sauk'i to ba wanda ya saurareni ko yanzu kafin na fito ma kanaga ya zamu yi ?".Sai da Jamil ya natsu yana nazari da neman mafitar data dace sannan yaja gwauron numfashi yace"to ni dai Jalaluldeen mafita d'aya ce agurina zuwa biyu wanda nake ganin idan muka bita wata k'ilah muda ce,mafita na d'aya shine muyi ta zuwa wurin momy muna rok'onta ko Allah zai sa ta gaya muna ainahin k'auyensu Hafsatu,mafita na biyu kuwa itace muyi ta zuwa wurare da dama nemanta agarin nan,kai idan ta kama ma har k'auyuka mu rink'a zuwa ko zamu dace". Jijjiga kai Jalaluldeen yayi alamar ya gamsu da bayanensa can ya safke ajiyar zuciya yace"ka kawo shawarwari masu ma'ana sosai,zamuyi dukkanin abubuwan daka ambata".Jamil ya bugi kafad'arsa yace"karka damu akwai alamun nasara da izinin ubangiji zamu ganta matuk'ar tana raye"."Ubangiji ya k'addara faruwar hakan".Cewar Jalaluldeen,haka dai su Jalaluldeen suka yanke shawarar zasu d'auki hutu wurin aikinsu,duk da companyn d'in ya kasance na Jalaludeen ne,dole zasu d'ora wanda zai cigaba da lura da tafiyar da companin cikin rik'on amana da gaskiya, wanda zai kula musu da wurin har na tsawon wani lokaci kafin su gama neman nata ko Allah zai sa suda ce.Jamil ya fara mik'ewa tsaye yace masa"tashi mu fara zuwa office daga nan mu fara nemanta acikin gari,duk da abu ne mawuyaci mu ganta amma wata k'ilah mu dace"."Haka ne abokina..". Fad'ar Jalaluldeen yayinda yake shirin mik'ewa tsaye,haka dai suka je sukayi duk abinda ya dace suka fita nemanta awurare da unguwanni,haka su Jalaluldeen suka wuni nemanta basu ga ko mai kamada ita ba,kuma ba labarinta duk da haka basu daina ba sai da suka ga sun shafe kusan wata biyu ba labarinta, sannan suka hak'ura da zuwa cikin gari da k'auyuka,suka fara zuwa gun momy sunata bata hak'uri da kwantar da kai cikin rarrashi dak'yar suka shawo kan hajiya KHADIJA ta amince ta hak'ura,k'arshe dai dole ta sauko ta sauraresu har ta gaya musu garin da Laure dillaliya take,ta kuma ce musu ba lallai bane ku ganta don ko Laure dillaliya tazo nan karb'ar kud'in aikinta ne,sai nake gaya mata abinda ya faru bayan fitarmu cikin gari ne koda muka dawo babu ita ba labarinta,amma kuje wata k'ilah ku dace but mahaifinka yayi rantsuwa akai ku dage da nemanta ko Allah zai sa ku dace, Allah yasa kuma ta saurareka idan kuka ganta,cikin ransu suka amsa da ameen sannan sukayi mata godiya, haka dai suka tashi suka fita jiki babu k'wari, bayan sun fita ne Jamil ke ce masa"aboki ba kace ka tab'a ganin mai kamada ita ba?Mi yasa ba zamu jaraba zuwa unguwar ba ko Allah zai sa mu sake ganin mai kamada ita ne mu gani wata k'ilah 'yan uwa ne".Jalaluldeen ya ciji leb'en bakinsa yace" haka ne fa abokina..". Saboda shi har ya manta ma da yarinyar daya tab'a gani mai kamada Hafsatu.Jalaluldeen ya k'ara da cewar"amma yadda za'ayi shine mu rink'a zuwa akodayaushe wata k'ilah mu dace,idan muka rink'a zuwa ko na tsawon wata uku ne k'ilah wata rana mu ganta tunda kaga saura wata hud'u ne lokacin da aka d'ibarmin ya cika, komai kace gobe kuma muje k'auyen mu nemi Laure dillaliya ko zamu sameta".Jamil yace"karka damu ubangiji ya kaimu gobe lafiya". Tattaunawa suka cigaba dayi atsakaninsu har suka kammala tsare-tsaren yadda hak'onsu zai cimma ruwa,haka kuwa akayi washe gari bayan su Jalaluldeen sunje k'ofar gidan hajiya Hafsatu k'anwar Maman Dr.Mansur sunyi jira har sun gaji komai kamada ita basu gani ba,haka dai suka baro shiyartasu jiki asanyaye sukayi gida, don yanzu Jamil wani lokacin ma yana yawan barcinshi gidansu Jalaluldeen don su rik'a fita da wuri saboda son ganin burin Jalaluldeen ya cika.Ashe dukkanin abubuwa da tattaunawar dasu Jalaluldeen sukeyi da hajiya KHADIJA Iya Luba tana bakin k'ofar parlour tana saurarensu,jin cewar Jalaluldeen shine sanadiyyar barin Hafsatu cikin gidan da kuma gurb'acewar rayuwarta,alal hak'ik'a Iya Luba ta k'ara tausaya mata domin jin aika-aikar da yayi mata saida ta zubar da hawayen takaici da tausayin Hafsatu,abu dai ne yafi k'arfinta da sai ta bawa Hafsatu shawarar ta kaishi k'ara kotu abi mata hak'k'inta idan ta bayyana,aranar haka Iya Luba ta wuni cikin gidan suku-suku babu kuzari balle k'arfin jiki,tabbas tasan Jalaluldeen ya cuci rayuwar Hafsatu cutarwa mai muni aduniya.
Awashegari ne suka tashi da wuri suka shirya don zuwa k'auyen rafin k'irya ko zasu dace suga Hafsatu,bayan sun yiwa momy sai sun dawo ne takeyi musu fatan Alkhairi, tabbas jini jini ne amma hajiya KHADIJA taji ba dad'i tana fatar aga Hafsatu saboda ta hak'ik'ance da cewar alhakinta ne yake bibiyar Jalaluldeen ya hana masa kwanciyar hankali, kallonsu kawai takeyi tana mai tausayin d'an nata don har ga Allah duk ya fita hayyacinsa gaba d'aya,sai dai ko waye yaji abinda ya aikatawa 'yar mutane dole yaji ba dad'i, amma koma minene aikin gama ya riga ya gama,Allah ya yafe masa damu ga baki d'aya saboda da mun masa aure da hakan bata kasance ba,kuma ba wanda ya wuce k'addaransa Allah yasa mu dace yasa mu gama da duniya lafiya.B'angaren Hafsatu kuwa bayan tayi sallah tayi addu'o'inta gari ya waye ne, ta gyara bedroom d'inta da sauran room's and parlours na hajiya Fatima,ta kawo room fresher ta fesa tasa turare cikin burner nan take lungu da loko na gidan ya karad'e da k'amshin dad'i,sai da tayi breakfast tayi wanka ta sanya jallabiya black with stones red, light make up tayi ta yafa veil d'in akanta bayan ta fesa performs masu sauk'in k'amshi,tana kammalawa ta tashi ta fito domin ta yanke shawara har azuciyarta zata sanar dasu gaskiyar mi ya faru da ita,saboda tana son taje taga wane hali mahaifinta yake ciki, gefe guda kuma auren Dr.Mansur da Mansura ya kusa domin yanzu Hafsatu tama rage yawan shige masa,don daga farko na zata ni yake so domun ko ni Hafsatu na kamuda sonsa,ko dan ya taimakeni ne nake sonsa ban sani ba saboda lokacin da naji cewar Mansura zai aura nayi kusan sati bana walwala ina cikin tsananin damuwa,amma haka na hak'ura har dai idan na tuna cewar ni ba kowa bace agunsu face wadda suka taimaka suka rik'eni amana,don awannan zamanin ba kowane zai rik'e d'an wani amana ba kamar yadda suka rik'eni, shiyasa nake son komawa mahaifana domin susan ina raye kuma ina cikin k'oshin lafiya,dangane da soyayyarmu da Dr.Mansur kuma ya samo asali ne tunda na shiga Jss 3 ubangiji ya jarabceni da soyayyarsa mai girma,to dayake shi yake kula da ragamar rayuwarta yana shagwab'ani sosai kamar k'anwar cikinsa,shima alokacin ya kamu da tsananin k'aunata,to haka muka fara soyayya muna kulawa da juna,idan yaje office bini-bini ya kirani awaya yana kasheni da kalaman k'auna ni kuma zuba shagwab'a nakeyi,idan lokacin dawowarsa yayi zan shek'a kwalliya na sanya tufafi masu k'yawo in zo harabar compound gidan in tarbeshi,yayinda shi kuma zai nuna zallar farin cikin kulawar da nake nuna masa ya cikani da tsarabobi irinsu chocolates and cosmetics,haka zan amshi briefcase ahannunsa in shiga gaba yana biye dani har cikin room d'insa,ni nake zuba masa ruwan wanka masu d'umi in fita idan na daidaici ya shirya,in kawo masa lunch d'insa ya cika cikinsa haka zamuyi fira yana gama cin abinci yaje ya gaisa hajiyarsa ya dawo wurina mu cigaba da soyewarmu,haka soyayyarmu ta cigaba da wakana lafiya k'alau har fara karatun lawyer wai ni duk hauka da soyayyar Dr.Mansur dake dank'are azuciyata akansa,ashe ban sani ba haukana nakeyi domin tun ba yau ba mahafiyarsa hajiya Fatima da k'anwarta hajiya Hafsatu sukayi alk'awarin cewar zasu had'ashi aure da 'yar uwarsa Mansura,sai da mukayi nutso acikin kogin soyayya sannan hajiya Fatima ta fahimci cewar muna k'aunar junanmu,shine dalilin dayasa wata rana ta kirani ta bani hak'uri akan inyi hak'uri da soyayyar Mansur domin ta riga tayi alk'awarin zasu had'ashi aure da'yar uwarsa,maganar ta dokeni matuk'a amma haka na jimami da bak'in ciki da kwanaki da yawa,hatta shi kansa Mansur saida nayi fushi dashi na tsawon lokaci,domin laifinsa na gani daya gayamin gaskiyar magana tun farko dole na hak'ura saboda ba komai ne zuciya ke so take samu ba,dak'yar ya rarrasheni ya tambayeni dalilin fushin da nakeyi dashi na fad'a masa maganar da mahaifiyarsa ta gayamin, hak'uri ya bani tareda cewar da babu alk'awarin aure atsakaninsa da Mansura dani zai aura,haka na nuna ni na hak'ura ya auri 'yar uwarsa saboda k'yautatawa da rik'on amanar da suka yimin ba zai sa na zamo silar ruguza wannan dad'ad'd'en alk'awarin ba, wannan shine silar rabuwata da mai tausayi wanda yasan kima da darajar 'ya mace wato Dr.Mansur,bayan Hafsatu ta gama tunani ne taje ta gaida hajiya Fatima tayi sa'ar kuwa Dr.Mansur na wurin shima ya fito ne zai wuce aiki,amma sai yayi breakfast don yana gamawa sai sha d'aya zai fita, bayan Hafsatu ta gurfana ta gaidasu ne ta fara fad'a musu cewar mahaifinta yana raye da kuma mafarin barowarta garinsu,har dai izuwa kad'etada Mansur yayi, amma ta b'oye musu cewar agidan aikinta ne muguwar k'addara ta sameta,saboda d'an gidan ne yayi mata fyad'e ya tarwatsa mata rayuwa da kuma martabarta,ta nasa azuciyarta har abada baza tab'a mancewa da zalunci da cin amanar da Jalaluldeen yayi mata, akullum addu'arta akanshi ubangiji ya hana jin dad'i da farin cikin duniya kamar yadda ya hana walwala da sukuni arayuwarta......................
_Muje zuwa ko yaushe Jalaluldeen zai ga Hafsatu har ya cika burinsa akanta na neman yafiyarta da kuma aurenta?._
_Ku cigaba da kasancewa dani Maman Afrah domin yadda wannan littafin zai kasance a k'arshe,ina matuk'ar godiya da bibiyata da kukeyi akodayaushe masoyana.__Comments&Shares_
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.