💜💙💜
*LAIFIN SHI NE*
💜💙💜
_Na maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
3️⃣
Koda garin Allah ya waye,Hafsat tayi aikinta kamar yadda tasa ba data gama,da yake jiya tasan babu batun zogale, dan bata ga abuhu ba. Kenan ba'a samo bane shiyasa bayan tayi sallah ta gama aikin gida,sai ta zauna jiran Innah Jummai ta fito taji me zata yi mata,bayan Innah Jummai ta fito tace mata"kawai tayi taje tayi wanki",harda bata d'ari biyu ta sayo sabulun wanki da yake harda na Sule ta mik'o mata taje ta wanke ga baki d'aya,tace mata"sannan ki tabbatar kinyi wanki da wuri don birni za'a da ke ,kina ji na ko".D'aga kai nayi domin haka kawai nake jin gabana yana fad'uwa akan wannan tafiyar da ake son turani,ban san mi yasa babana baya tab'a magana akan cin zarafin da akemin agidan nan,nisawa Hafsat tayi cikin tuk'uk'in bak'in ciki da damuwar da ke wanzuwa azuciyarta tace"ba komai Allah ya shigemin gaba".
Yadda akayi Innah Jummai tasa mu kan malam Kabiru jiya,shine bayan ya dawo yaci abinci,cikin natsuwa da kwanciyar hankali Innah Jummai tace"Kabiru magana nake son mu yi da kai".Malam Kabiru ya d'ago idanunsa ya dubeta yace"magana,wace irin magana kenan?Innah Jummai tayi murmushin mugunta tace"dad'ina da kai Kabiru saurin azarb'ab'i idan ka bari ai zan gaya maka zanyi ko".Malam Kabiru ya musk'uta yace"to ina jinki Jummai..".
innah Jummai ta gyara zama tace"daman Kabiru jiya ne Larai dillaliya tazo min da wata shawara, tace min na bata Hafsat ta kaita birni tayi aiki,domin mu samu kud'i shi ne nace mata sai nayi shawara da kai naji abinda zaka fad'a,mi ka gani don gobe ne tace zata wuce da ita,in ka aminta shine nake son naji ta bakinka,don ba zai yiyuwa ba na turata bada saninka ba..".
Malam Kabiru yayi jimm yana tunanin abinda zai iya zuwa ya dawo,har azuciyarsa baya son ya tura 'yarsa Hafsat aikatau amma yana shakkar matarsa ba zai iya musa mata,sai da Innah Jummai tayi magana sannan ya dawo da tunanin daya tafi dashi, sannan yace"Jummai ba wai tafiyar Hafsat ce matsalar ba,a'a ina gudun Hafsat ta shiga matsala ne,dan ina yawan jin mutane na fad'in illolin tura yara birni aikatau".Innah Jummai ta saki doguwar ajiyar zuciya tace"hmm
Kabiru kenan daman ita duniya idan ka biyewa mutane,to ba zaka tab'a cigaba arayuwa ba,dan mutane sun fison yadda suka k'are atsiya ce kowa ma ya k'are".. Kuji maganar Innah Jummai sai kace ita tana sauke hak'k'in wani akanta ne. Allah ubangiji yasa mu dace Ameen.....Innah Jummai ta karkace baki cikin kissa da makirci tace"Kabiru kawai ka amince Hafsat ta je birni dan kila ma muyi kud'i ta hanyarta".Malam Kabiru ya numfasa yace"to shikenan daman ni bak'in zuwanta nayi ba,kuma bana son ki b'ata ranki ko kad'an, saboda kin san ina sonki sosai..".
Ya cigaba da cewar"Jummai shiyasa komi kika cemin bana jayayya da ke nake amince miki".Innah Jummai ta nisa aranta hmm Kabiru dai tace azuciyarta,ta cigaba da fad'in ba dole ka amince min ba tunda na riga na gama da kai..!Ganin tayi shiru yasa Malam Kabiru yace mata"to kin zo kina yita magana har lokaci ya tafi bamu yi barci ba, don haka tashi muje muyi kwana,ita kuma kice mata ta shirya gobe Allah ya kiyaye hanya". Bayan sun kwanta ta rik'a tunanin kud'in da zata yi azuciyarta sanadin zuwan Hafsat a birni..Wannan shine sanadin fad'awata wata rayuwar da ban tab'a fuskanta ko afkawa cikin irinta ba ni Hafsa Kabiru...
_Comments&Shares._
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.