LAIFIN SHI NE

10 0 0
                                    

💜💙💜

*LAIFIN SHI NE*

💜💙💜

_Na Maman Afrah Ik_

~Editing by Mugirat Musa.~

2️⃣

Shiyasa da Meri bata zuwa makaranta bai tab'a cewa komai ba,don shi mutum ne da ba yayin yawan binciken me ke tafiya acikin gidanshi,babu ruwansa da lura da lamurran 'ya'yansa shiyasa ko mi ake yi ba cika sani yayi ba.Bayan su ci tuwo kowane ya tashi ya shige d'akinsu babu abinda suka iya balle su tsinana acikin gidan,sab'anin ita Hafsat da take kwana d'akin da mahaifiyarta ke ciki alokacin da take raye,domin yanzu ba komai cikinsa sai 'yar tabarmar da take shinfid'awa ta kwanta bayan taje tayi sallah sai ta kwanta ashimfid'arta, tana tunanin shin mi ta yiwa matar babanta Innah Jummai da ta tsaneta har haka?Don dai ita tasan iya gwargwado duk abinda aka sata yi take yi, bata tab'a musawa ba saboda a kodayaushe aikin gidan ita keyinshi gaba d'aya ko kauda kara Meri bata yi,sai yawon gantali ta d'aurawa gari jakah.

Tana cikin tunanin munanan al'amurran da suke faruwa da ita,har barci ya d'auketa,da garin Allah ya waye haka dai take tashi tayi aikace-aikacenta kamar yadda tasa ba,don ta san idan ba tayi ba itace zata sha duka da bak'ar uk'uba awurin Innah Jummai muguwar mata.

Haka rayuwar Hafsat ke tafiya da dad'i daba dad'i, har ta kai shekara goma sha hud'u  tana cikin ha'ula'i da k'angin rayuwa, Meri ko an mata aure da wani mai suna Malam Buba acikin garin yake kuma yana da matarsa d'aya da 'ya'yansa ukku, yana da sana'arsa domin cin kasuwa yake zuwa yi acikin birni,acewar Innah Jummai gwara tayi mata aure kar taje taja mata abin fad'e a gari,saboda ana yawan kawo mata k'orafe-k'orafe da fad'in yawan tara samarin da take yi,don wani lokacin har tab'in jikinta sukeyi suna lagudartaa b'oye,an sha ganin Meri tana kwantawa cikin kango da namiji yana iskanci da ita ba sau d'aya ba sau biyu ba,shiyasa Innah Jummai ta matsawa malam Kabiru aka yiwa Meri aure,sai dai Sule shi ma k'arami ne don yanzu ma ya cika shekara goma cikin ta sha d'aya yake,haka dai da ruwa take tafiya.Kwatsam! Wata rana Hafsat ta dawo daga wajen tallah, sai ta iske Laure dillaliya cikin gidansu, to da yake kowa yasan Laure dillaliya d'iyan mutane take tdauka ta kai birni suje yin aikatau, wasu kuma ta turasu karuwanci iyayensu basu da labari,domin in ta zo k'arya take musu saboda ce musu take yi aikatau zata taimaka samo musu don su rage wahalar rayuwa,dan yanzu a halin da ake ciki na tsadar abinci da suturu domin  wani na dare ma sai ya gagareshi,shiyasa idan ta zo musu da dad'in baki suke bata d'iyansu jikinsu yana k'yarrmar murna,tana kaiwa birni duk wata tana kawo musu dubu biyar ko bakwai da yake sun san dubu d'aya ma wuya take musu wurin mallakarta,suna zaune abasu dubu biyar ko bakwai shiyasa suke d'aukar yaran suna bata a sab'e.

Hafsat dai ta shigo gida da sallama ta zuk'unna k'asa ta gaidasu,suka amsa mata adak'ile jiki asanyaye Hafsat mik'e tsaye ta ba Innah Jummai  kud'inta na tallah,da yake yanzu duk k'awayenta biyu an musu aure daga ita sai A'isha ne kawai ba'a yiwa aure ba,data mik'a mata kud'in taje ta fara aikin gida kamar yadda ta saba yi a kodayaushe akowane lokaci..

Laure dillaliya ta zurawa Hafsat idanu kamar zata lasheta,can ta k'udurta wani abu azuciyarta tana k'issima abubuwa da dama-dama game da Hafsatu,dogon numfashi ta safke bud'ar bakin Laure dillaliya tace" tafd'ijam ke yanzu Jummai kina da kamar wannan budurwar kike zaune kud'i na miki wuyar samu..?".Innah Jummai tace "to ya zanyi Laure?Ai gashi nan tana yimin bauta kuma har tallah take ymin domin tun tana yarinya nake d'ora mata tallah,gashi har yanzun nan ban bari ba".Laure dillaliya cike da iyayi da munafurci ta bintsire baki tace" hmm yanzu ke Jummai har wasu kud'i ne take yi miki a yini  da in yayi yawa bai wuce d'ari biyar,d'ari biyar har kud'i ce da za ki dogara ga wannan k'aramar sana'ar,shawarar da zan baki ki bani ita na kaita birni ki ga yadda ta ke mai k'yau haka,wlh ba k'ananan kud'ad'e  zaki samu ba".Innah Jummai tace" Allah kuwa Laure dillaliya?To bari Kabiru ya shigo zanyi masa bayanin komai,zuwa jibi sai ki dawo ki je da ita ko". Laure dillaliya kuwa cewa tayi"wane jibi kuma Jummai gobe dai don ni in nabar gari bana dawowa sai k'arshen wata na kawowa iyayen yara kud'insu,don haka ni gobe zan koma keyi yadda zaki yi ya aminta naje da ita gobe zaki yi kud'i nan take.".

Innah Jummai ta washe baki tace" baki da matsalah dani k'awata Allah ya kaimu gobe,sai tace"amin ni kinga tafiyata sai na dawo".Innah Jummai tace"ki dawo lafiya".K'awarta Laure dillaliya tace"ubangiji ya k'addara".Tana rufe baki ta sanya kai ta fice daga cikin gidan da azama,ita dai Hafsat sai da ta gama aiki ta shige d'akinta ta sha kukanta, da yake taji komai da suke cewa don waje ne take aikin tana jinsu, bayan ta gama kukanta ta tashi taje tayi alwalah tayi sallah, saboda yanzu tayi hizo kusan talatin shiyasa yanzu take yin sallanta daidai,don tana da ilimi gwargwado yanzun nan.

Bayan ta je ta d'au abincinta ta ci ta je ta kwanta har barci ya d'auketa bata sani ba,da yake yanzu tunanin abubuwa da k'uncin rayuwa sunyi mata yawa.....................

_Comments&Shares._

LAIFIN SHI NEWhere stories live. Discover now