💙💜💙💜💙
*LAlFIN SHI NE*
💙💜💙💜💙
_Na maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
1️⃣5️⃣
Bayan wata d'aya da dawowarsa kwatsam! Wata rana da bazan tab'a mancewa ba shine, naje gyaran d'akinshi ashe bai fita ba ya shiga toilet yin wanka da yake tun lokacin daya dawo bai tab'a had'uwa da ni ba, ko ni dai sau biyu ne na ganshi da ranar da ya dawo,daku ma zai fita cikin mota na hango giftawarsa amma shi bai ganni ba ko sau d'aya, ina cikin gyaran gado nayi nisa da gyarawa,kamar daga sama sai ganin mutum kawai nayi akaina,ai kuwa sai da na firgita domin har ga Allah na tsorata da ganinshi, gashi daga shi sai towel yake d'aure a kwankwasonsa abinda ban tab'a gani ba arayuwata namiji ba kaya ajikinsa sai yau,shiyasa jikin Hafsatu yanata makarkatar tsoro da fargaba, Jalaludeen kuwa mamaki ne yakeyi mai zai kawo 'yar aiki a d'akinsa kuma ace har ta shigo masa d'aki bada saninsa ba,wani b'angare na zuciyarshi kuma cewa yakeyi gaskiya yarinyar nan ta had'u duk daga gani 'yar k'auya ce,amma koma wa cece wata rana zan d'and'anata,jin tayi shiru kan Hafsatu yana sunkuye k'asa shi kuma Jalaludeen sai kallon k'urilla da sha'awa yake yi mata can ya numfasa yace"ke zo nan".Ba musu Hafsatu ta je ta duk'a har k'asa shi kuwa ba abinda ya tsana irin a duk'a masa, abin na bak'anta masa rai Jalaludeen cikin b'acin rai bai san lokacin da ya buga mata tsawa ba sai da ta razana,cikin kakkausar murya yace mata"ke tashi dabba ina ce akan wane dalilin zaki duk'amin!?".Bai yi wata-wata ba ya sharara mata mari sai da taga gilmawar taurari!Kuma Jalaludeen ya fisgota da k'arfi ya had'ata da jikinshi,ita kuwa Hafsatu abinda bata tab'a yi ba arayuwarta nan take ta rik'a k'ok'arin k'wace kanta daga hannunsa, tana kuka tana yakushinsa har dai ta samu ta gudu ta fita a d'akinshi, sashinsu na masu aiki ta shige d'aki ta kulle da k'arfi ta fad'a akan katifarta tana shure-shurenta,da sakin gunjin kuka mai cike da tarin bak'in ciki da damuwa nan take taji ta tsaneshi tsana mai muni arayuwarta,saboda ta fahimci cewar zai iya kawo matsa cikas da matsala arayuwarta..!
Haka dai ta wuni d'aki sai data ta kwatancei Jalaludeen ya fita agidan, sannan ta je ta ktare aikinta don ta san idan ba ta je ta gyara ba,to kashinta ya bushe, haka dai Hafsatu ta daure cike da k'unci ta gama aikinta ta koma d'aki tana ta tunani domin yanzu tunanin matsalolinta ya riga ya zamar mata jiki................
_Comments&Shares._
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.