LAIFIN SHI NE

4 0 0
                                    

💙💜💙💜💙

*LAIFIN SHI NE*

💙💜💙💜💙

_Na Maman Afrah Ik_

~Editing by Mugirat Musa.~

4️⃣2️⃣

Mansura kuma bata kawo komai aranta ba saboda tasan sunan mahaifiyarta ne,kuma mijinta yana kulawa da ita tareda nuna mata zallar k'auna mai tsayawa azuciya,saboda Dr.Mansur gwani ne a fagen soyayya shiyasa itama takeji da abinta, don bata son ko k'uda ya tab'a matashi zamansu gwanin burgewa.

Jalaluldeen kuwa bayan sun koma gida ne suka je sukayi wanka atare,suka sanya tufafi barci suka fito parlour suka zazzauna akai cushion gab da juna,Hafsatu ce ta mik'e tsaye ta kunna musu TV ta sanya tashar mbc bollywood,ta dawo ta zauna kusa ga mijinta suka rik'a kallon wani fim mai suna Kris don fim d'in ya had'u sosai,suna kallo sunata tab'a juna suna wasanni gwanin burgewa,har saida Hafsatu ta fara jin barci sannan ne Jalaluldeen ya tashi ya kashe kallo, sukaje suka kwanta koda suka kwanta saida suka k'ara wasanni masu rikita hankali da k'wak'walwa, sannan suka raya sunna suna kammalawa suka tsarkake jikinsu sannan suka dawo suka kwanta bayan sunyi addu'ar barci ne kowa sai barci,dayake an d'auko gajiya yau a yawon hospital da kuma gidajen iyayensa,haka garin Allah ya waye dayake Jalaluldeen yana rigata fita tare suka shiga kitchen sukayi girki bayan sun kammala, suka je sukayi wanka ko acikin toilet ma saida suka lugudi juna son ransu kafin su fito su shirya,suka hau dining table sukayi breakfast bayan sun karya ta d'auko masa jikarsa ta fita office,sai da Hafsatu ta rakasa kafin nan ta dawo tayi shiri zuwa nasu office dayake yau tanada wani case.

Bayan Hafsatu ta dawo ne tana zaune dear d'inta ya kirata yana shaida mata cewar k'anwarsa Zainab ta sauka ta samu baby boy,don haka ki shirya da dare sai muje daman mu biya gidan yaya da kuma gidan k'anen mahaifinna,kinga da muka fita bamu samu biyawa ba,ya kamata ki shirya da wuri mu fita yanzu zan dawo gida kinji babyna,Hafsatu ta kad'a kai tace babu damuwa dear sai ka dawo take care, Jalaluldeen yace mata i will bye,saida suka kammala zancen soyayya sannan suka ajiye wayoyinsu, haka kuwa akayi bayan Jalaluldeen ya dawo ne suka shirya sai gidan kawu Ibrahim sukayi musu barka,basu dai jima ba suka fito sai gida suka ga jariri har momy takeyi masa k'orafin cewar yabar wahalar mata da sarakuwa,domin ko ita tanada juna biyu karka wahalarmin da ita, Hafsatu sai kunyar maganganun momy takeji yayinda Jalaluldeen yake sakin murmushi afaikace, bayan sunyi sallama ne dasu momy da kuma daddy,basu zarce ko'ina ba sai gidan yayansa suka sha fira basu baro gidan ba sai misalin k'arfe 11 na dare.............................

_Comments&Shares_

LAIFIN SHI NEWhere stories live. Discover now