💜💙💜
*LAIFIN SHI NE*
💜💙💜
_Na maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
9️⃣
Bayan hajiya KHADIJA ta haihu ranar suna ta zagayo,aka sakawa yaro suna Usman,shekaran Usman uku k'anen Alhaji Abubakar yayi aure,ya auri wata nutsattsiyar yarinya mai k'yau sunanta Hajara suka tare asabon gidansu,dan shi Abubakar yana tare da mahaifiyarsu da batada cikakkiyar lafiya har yanzu,don gidan mai girma ne sosai sai dai an k'ara k'awatashi da wasu abubuwan sosai acikinsa,wanda idan ba wanda ya san gidan tuntuni ba,mutum zai iya cewa sabon gida ne aka gina.
Bayan shekara biyar da haihuwar Usman, hajiya KHADIJA ta sake haihuwar wani d'a namiji aka saka masa suna Jalaludeen,haka rayuwa take tafiya har yanzun nan, haka aka saka Usman da Jalaludeen makaranta mai shegen tsada da 'ya'yan masu fad'a aji,bayan wasu shekaru da dama suka gama primary and secondary School aka turasu k'asashen waje karatu,bayan kuma mahaifiyarsu ta sake haihuwa d'iya mace aka saka mata suna Zainab.To haka rayuwa take tafiya acan k'asar India kuma Jalaludeen tunda ya k'ara wayewa ya fara neman mata don Allah yayisa mutum mai yawan sha'awa kuma mabuk'aci,shiyasa yake lalata 'yan mata gashi daman duk agidan nasu yafi kowa k'yawo sosai, don shi Allah ya masa zubi kaman d'an larabawa idan ba ma baka sanshi ba zaka iya rantsewa shi d'an cen ne, shiyasa matan India ke yawan kawo masa hari akowane lokaci da yake shi mai yawan sha'awa ne,shiyasa yake da saurin aminta da mace domin idan dai zata bashi kanta to shi kuwa zai ci ba ruwansa,duk da biyar da mata ke masa shi mutunm ne kuma mai wulak'anta na k'asa dashi shiyasa duk macen da bata masa ba, ko kulaki ba zaiyi ba ma duk da neman matanshi budurwa biyu ce gareshi da sune yake watsewarsa,ba ruwanshi amman duk da haka ilimi ke gareshi sosai shiyasa yanga,'yan aji da kuri ya masa yawa da izza da kuma wulak'anci don yana ruwa da mahaifiyarsa sosai don kona cema ita ya biyo don wulak'anci ke gareta a jininta yake yawo.Haka rayuwa take tafiya yau da dad'i gobe ba dad'i,yau farin ciki gobe bak'in ciki yanzu haka shima Ibrahim nada yara biyu Mustapah da Farida Mustafa yanzu yanada shekara 29 while Farida she was 17 age ba wani tseraiya garesu ba ita da Zainab ba don kusan sa'annin juna ne ma.
Haka rayuwa gidajen nan biyu ke tafiya cikin son junansu da tsabtatacciyar k'auna ta hak'ik'a, saboda kowanensu nada kud'inshi basawa juna hassada shiyasa zamansu yake burge mutane da dama ahalin yanzu.
Yanzu haka sun yiwa juna alk'awarin had'a yaransu aure Mustapah da Zainab idan ta kammala karatunta..........
_Comments&Shares._
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.