💙💜💙💜💙
*LAIFIN SHI NE*
💙💜💙💜💙
_Na Maman Afrah Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
3️⃣8️⃣
Haka kuwa ce ta faru don gaskiya Hafsatu taga kulawa sosai, saboda har Meri ma na yawan zuwa gun 'yar uwarta don daga Inna Jummai har d'iyanta sun rok'eta gafara kuma ta yafe musu yanzu, damuwarta d'aya mijin da akace anyi mata aure dashi shine matsalarta, don ni har ga Allah na tsaneshi,b'angaren mahaifinta Malam Kabiru kuwa satinta biyu da dawowa ya kira Jalaluldeen ya sanardashi an ganta, tsabar farin ciki sai da Jalaluldeen yayi sujjada anan gun da yake bayan sunyi sallama ne da mahaifinta,don Jalaluldeen ya gaya masa zai zo yau sai mahaifinta yace ya bari ko wata d'aya ta cika,sai yazo su gana bayan sati biyu ya dawosu wuce da ita haka dai Jalaluldeen ya daure har tsawon wata d'aya,saboda ya gayawa (momy) hajiya KHADIJA cewar an ganeta cikin k'oshin lafiya.
B'angaren Dr.Mansur kuwa bayan sun bi hanya ne mahaifiyarsa ke gaya masa yadda sukayi da da mahaifin Hafsatu,tsabar rud'ewa Dr.Mansur tashi hatsari sukayi Allah ne kad'ai ya kaisu gida lafiya,haka dai bayan sun je gida sun huta ne sun ci abinci duk dashi Mansur ba dad'in rai yake ci ba, yana ci ne kawai don sun kwaso yunwa,haka dai da hajiya KHADIJA ta lura da cewar d'anta ya shiga cikin mayuwacin hali da tsantsar damuwa,nan take ta dinga bashi baki da yi masa 'yan nasihohi masu nuni da hak'uri da kuma dangana arayuwa,cikin dauriya Dr.Mansur yayi tawakkali don shi mutum ne mai biyayya ga iyayensa,duk da har ga Allah yaso ace shine mijinta to ya ya iya da tsarin ubangiji,Allah ya bani hak'uri da dangana azuciyata fad'ar Jalaluldeen a k'ark'ashin zuciyarsa.
Ba suyi wata biyu ba aka saka ranar aurensu da Mansura,nan da sati biyu haka kuwa akayi don rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya, bikin kuwa har da Hafsatu saida ta halarci bikin don yanzu sun zama 'yan uwa,don koshi sau biyu yana komawa k'auyensu bayan auren Dr.Mansur da sati d'aya ta fito zata je gidan Meri don ta aiko tana kiranta saboda bata jin dad'in jikinta,to ta fito ne taga mota bakin garka batayi tunanin komai ba sai kawai Hafsatu ta ruga aguje taje ta bud'e murfin motar tana kiran"yaya kaine kazo babu sanarwa..?". Bata k'arasa maganarta ba sauran ta mak'ale tsabar firgicin wanda ta gani a cikin motar,domin ta zata yaya Mansur ne don sunada mototi masu yawa shiyasa bata tsaya dogon bincikar kowaye ba,shi kuwa gogannaku(Jalaluldeen) tsabar farin ciki kasa rufe baki ma yayi,yau gashi ga Hafsatu d'insa abin soyuwarsa,ita kuwa Hafsatu fita tayi ta shiga gida da gudu tana kuka saboda bazata tab'a mantawa da bawan Allah nan ba arayuwarta, shi kuwa Jalaluldeen da ganin haka sai jikinsa yayi sanyi zuciyarsa tana k'una da rad'ad'i,don bai zaci har yanzu bata yafe masa ba,haka dai ya fito acikin motarsa ya kira mahaifinta ya sheda masa cewar ya iso,don yace masa zai zo kuma yace idan yazo zai bashi matarsa su wuce,bayan sun gaisa cikeda girmamawa da karamci,Malam Kabiru ya koma cikin gida bayan ya iso ne ya shiga cikin gida ya shaida mata cewa ta shirya mijinta zai wuce da ita,ai kuwa nan Hafsatu ta birkice musu ta ratsa kuka don har ga Allah bata k'aunarshi,kuma ta tsaneshi tsana mafi muni arayuwa ta duk'a ta rik'a rok'on mahaifinta tana hawaye tana cewa"don Allah baba ka warware wannan auren wallahi bana sonsa na tsaneshi azuciyata..!!!".Haka dai Hafsatu tai ta rok'onsa da Malam Kabiru yaga d'iyartasa da gaske takeyi ya jata ya shiga d'aki da ita,yayi mata nasihohi masu ratsa jini da jijiyoyi ya dinga janyo hadissai da ayoyin al'aqur'ani masu nuni da hak'uri da yafiya arayuwa, har dai ya samu ya ciyo kanta ta hak'ura, Hafsatu ta dai k'udurta azuciyarta da sai yayi daya sanin aurenta arayuwarsa sai ta musguna masa...........................
_Comments&Shares_
YOU ARE READING
LAIFIN SHI NE
General FictionLabari akan wata yarinya mai suna Hafsatu wadda ta had'u da gwagwarmayar rayuwa da uk'ubar kishiyar uwa.