page 2

145 7 0
                                    

2019.

Kalapanzin barracks,
312 Artillery
Kaduna,Nigeria.

Sir!

Sojan ya fada bayan ya sara mishi ya kuma tsaya kikam ko numfashi mai yawa baya iya yi, duk da wanda ake sarawa baya kallonshi dan ya juya baya yana daga wani karfe mai mugun nauyi,  duk dagawar da zaiyi muscles dinshi da jijiyoyi ne ke murdewa su fito rudu rudu kamar zasu tsinke, bai kuma juyo yaji abunda subordinate dinsa yazo dashi ba sai da yayi sau 30 sannan ya ajiye karfen a mazauninsa ya tashi ya nufi kan wani table dake dauke da ruwan roba mai sanyi karara.
       Murzawa daya ya bude ruwan ya kafa abaki bayan yayi basmala ya sha har rabi sannan ya ajiye, sanyin ruwan ya ratsa duk wata magudanar jini dake jikinsa yana saukar mishi da wata nutsuwa, saida ya dauki wani karamin towel fari ya goge wuyan sa sannan ya juya ga wannan sojan dake tsaye kikam tun dazu, juyowar ALIYU HAIDAR yasa sojan kuma daidaita tsayuwar sa sannan ya ce ba tare da kuskuren duban Fuskar Aliyu ba,

" The battalion awaits you sir!"

"Noted"

Muryarshi dakakkiya mai wata irin launi dake fita daka bakin jajirtataccen namiji, murya ce cikakkiya mai gardin gaske da farfado da tunanin duk wani mai rai, murya ce irinta ta namijin daya amsa sunan sa namiji ako ina musamman mazan da ubangiji ya halitto su dan su zama sojojin yaqi aban kasa, maza ne kebantattu kuma zababbu agurin subhanahu wata'ala! 

Bayan fitar sa Aliyu ya shiga bandakin sa dake manne da dakin ya sakarwa kansa ruwan sanyi sannan ya fito a gurguje cikin azama ya shirya cikin uniform dinshi, uniform ne na Nigeria Army camouflage mai kyau,amma a wannan karan Aliyu ne yayiwa uniform din kyau,  hularsa ya dauka ya riqe ta a hannu ya fita daga dakin dake cikin quarters din officers.

Sojoji guda 2 dake tsaye bakin dakin suka sara mishi yayin da shikuma ya cigaba da kurdawa ta corridors da offices dan isa ga filin da zai sadashi da hundreds of soldiers dake jiran isowarshi,  wajen cike yake da kananun sojojin da zaa yaye nan da sati 3 masu zuwa wanda taro ne da zai kunshi shugabannin kasashe har guda 2 da manyan kusoshin Nigeria army da defence,

Surutu da hayaniyar dake wajen saika dauka duk mutanen garin ne awajen amma lokaci guda wannan hayaniyar ta dauke bat kamar babu mai rai awajen, bakomai bane ya haddasa wannan shirun sai bayyanar  LIEUTENANT COL.ALIYU MAHFUZ JAJERE . yana tsaye gaban 250 battalion of soldiers shi kadai tamkar rai! Alokaci guda duk wadannan mutanen suka gyara tsayuwarsu dakuma sara mishi da mayar da dukkanin tunanin da suka mallaka zuwa gareshi,  babu mai ko numfashin kirki dan tsananin tsoro dakuma tasirin abunda kwarjininsa ke haifarwa.
         Saida ya share kusan minti 20 ba tare da yace musu komai ba ,baiko motsa daga tsayuwarshi ba suma sojojin dake tare dashi dakuma wadanda ke gabanshi basu yi kuskuren ko motsa yan yatsansu ba, kallonsu kawai yakeyi daya bayan daya yana fatan ya samu wani da zai saba doka dan ya kaddamar masa amma bai samu ba,  ya zama dole ya zama very sure of his battalion da zai gabatar wa shugabansu harma da nigerian president gaba daya nan da sati 2 masu zuwa....he isnt gonna present anything less, dole they have to be Worthy of him and his rank!
       
"Attention!!!!!!"

Muryar Aliyu haidar ta ratsa kunnuwan daruruwan mutanen dake wannan filin tamkar saukar aradu, da ace akwai wani bako awajen daba soldier ba zaiyi ta jiran yaga ankawo speakers da mike dan Aliyu yayi magana da shi amma inaaaa!  Bahaka soja mazan fama suke ba barin Aliyu da daya tamkar da dubu ne ko acikin sojojin,ko dayake barewa bazatayi gudu ba danta yayi rarrafe.  Haka ya cigaba da gabatar musu da abunda zai ce tare dayi musu gargadi akan muhimmancin passing out din dake gabansu, kowani rai awajen yana jin muryar Aliyu tartar ba tare dawani tangarda ba , muryarshi tana isa ga kowa tana haifar da wani karsashi na daban. Murya ce ba irin ta Ajeboters ba, murya ce irinta mazan da rayuwarsu ta gini tun yarinta akan fagen daga, mazan da karar fitar harsashi da tashin bama bamai tsohon alamari ne agaresu.

AFIFAHWhere stories live. Discover now