page 12

71 6 0
                                    

Fika,

Damaturu.

12pm.

Tayoyin mota kirar Hilux ke falfala uban gudu akan titin tana keta dazuzzuka da gonaki da matsanancin gudu tun misalin awa 2 da suka wuce, motar shiru babu mai cewa komai sai radio da AC keyi kadai, Mal musa Driver da kuma Security dinta agaba sanye cikin Uniform din sojoji, Mutum ne inyamuri kuma christa mai suna Chike, chike Giant ne ga tsawo da kauri kuma jarumin gaske daya tsinci kansa a jerin gwanon team masu yiwa retired general din hidima, bayan kasancewarsa agidan general din kuma ya kara kasancewa main security din Hajiya Zulai kuma amintaccenta mai kare rayuwarta da tasa rayuwar.

Jakar ta ta bude ta ciro wayarta ta duba , sun kusa isa, nan da minti 15 zasu iya isa gidan malam din. Umma zulai sanye take da wani hadaddan leshi na alfarma, taci kwalliya ta hade kamar mai shirin halartar taron manyan mata na duniya, babu karya zulai matar manya ce, ta dade da gane hakan tun tana yar talla, tasani ta kuma ji ajikinta ita ba matar talaka bace, dalilin dayasa da auren kaddarar malam ashiru ya fada mata batayi kasa a guiwa ba ta wancakalar dashi da dukkan iyawarta ta fito ta kuma fada hannun namijin daya dace da ita, ta fada hannun uban daya dace a haifarwa ya'ya.

Duk a kokarinta na kokarin fara gyara alamura ne yasa ta shirya zuwa wajen Amintaccen ta, Aminin ta, dogaronta, majibin cin lamuranta Malam mai kankat, yau kwanansu biyu kacal da dawowa daga kasa mai tsarki bayan sun shafe kwanaki 10 acan tana yawon sanaarta dakuma yawon shaguna da kasuwanni dan abunda ya kaita kenan ita.
       Gajiya ce sosai ajikinta , akwatinta ma ko budeshi batayi ba ta shirya ta fito a yau dinnann basai gobe ba dan ayiwa tufkar hanci....bataga ta zama ba sabida wani bakin gani da tayi a jiya da dare da misalin 12 na dare.....General Mahfuz ya fito a wannan daren Daga dakin Gaji, tana zaune a falon nashi Bayan ta gama nemansa bata ganshi ba, ta kira number shi sai taga a dakin ya barta, shigowar da zaiyi ta tambayeshi daga ina yake ya kuma dubi kwayar idonta yagaya mata daga wajen Gajin yake

Gaji kuma?

Ta tambaya a lokacin kamar wanda yace yaje dakin mai aikinsa, babban Abun mamaki daya sameta shine Abban har ya iya bude baki ya tabbatar mata da cewa daga wajen matar tasa yake. A nata tunanin ko yakumbo bata isa tasa ya fita a cikin wanann daren yaje wajenta ba balle dutse irin Gaji, Gajin da ita inso samu ne kujerun dakunan Abban su fita matsayi da daraja a idon shi abban, amma an wayi gari Abban ya zagaya ya je dakin Gajin.

Kwafa takeyi a ranta tanajin kamar ta karbi motar ta tuka da kanta dan mal musa baya sauri sam, ta kosa ta isa ga malaminta, ta kagara ta isa ga inda zaa share mata hawayenta.
         Motar tayi parking a daidai bakin kwanar gidan mal Rabe mai kankat, sabida kankantar layinsa mota ba ta shigarsa saidai duk wanda yazo da mota ya sauka a bakin layin, Chike ya fito daga gaban da azama ya budewa hajiyarsa kofar at the same time ya kame ya kuma Sara mata kamar yadda sukeyi a ko yaushe, wannann gesture din shi yafi komai mata dadi a zuciya, ta fito ta gyara zaman mayafinta mai girma da rufe jiki ruf, indai shigar mutunci ce saidai  mata su koya a wajenta.

" Ku jirani chike"

Ta fada ba tare da ko ta dubeshi ba ta wuce ta tsallaka kwatar da zai kaita cikin gidanmalan din, wani gida daya zame mata kamar dakin bauta da ibada ga irinsu da suka bata a duniya, gida ne mai zurfi kuma daga farkonsa duk ginin kasa ne wasu kuma na siminti, tsakar gidan nada fadi da girma iya dubanka. ta shiga bakinta dauke da sallama , uwargidansa na daga dakin hatsi ta leqo tana ta lale maraba da hajiya zulai kamar zata goyata, taita mata barka yayin da suka zagaya ta baya sai gasu gaban wani ginin zamani mai kyau , wanda bai taba zagayawa bayan ba bazai taba yarda ginin acikin gidan yake ba , ta bude kofar falon ta daga labule hajiya zulai ta shiga ta zauna a daya daga kujerun falon masu rangwamen kyau a birni amma hamshaqai a kauye, matar malam ta bude fridge din dake gefe ta ciro ruwan roba swan mai sanyi ta ajiye agabanta sannna ta tsugunna tanata zuba gaisuwa, sun jima rabon dasuga hajiya agidan amma tasan suna waya da malam din, hajiya Zulai duk ba abunda takeson ji kenan ba,  ina malam din bayan yasan sunyi dashi zatazo ayau din,

AFIFAHWhere stories live. Discover now