page 7

110 9 0
                                    


9:30pm

On a cold saturday night.

Ya rabbil Alameena! Wai ya akayi mukayi dare haka?

Ikram ta furta tana daga tsaye a gefen kujerar dakinsu hanan, munirah kuma tana tsaye gaban mirrow tana ta feshe jikinta da uban turarukan dake kan mirrow,

"Calm down iky, an fa gama min, dauri akeyi"

Na fada duk da nima tawa zuciyar tana min babu dadi akan makarar da mukayi wajen tafiya dinner din, kuma ba komai bane yaja hakan sai rashin dawowar mu da wuri daga school....zan iya rantsewa Mr bola yana sane yaja lesson din yau har karfe 4 , muna dawowa gidan muka iske wasu daga cikin cousins da Kuma kawayen hanan anata musu makeup Kuma mai makeup din bata taho da assistant ba, saida mukayi da gaske sannan aka farayiwa munirah a lokacin magrib saura yan mintina kadan.
       A hakan ma tana Sauri sosai amma dai mun makara, jamaar gidan immediately bayan magrib suka dinga fita dan kaidar gidanmu baa African time, Abba is not a civilian hakan yasa yake matukar girmama lokaci muma kuma duk yabi jikinmu aduk wani shaani da zaayi. A hankali a hankali gidan ya dade yayi shiru babu kowa sai yan tsofaffin dake can part din yakumbo, Sauri muke tayi dan driver dake kaimu school yana waje yana jiranmu shi zai kaimu.

"Here you go"

Makeup artist din ta fada bayan ta soka last piece din pin ajikin head dina.

"Tabarakallah ahsanul khaaliqeen, Afy kinga yanda kikayi kyau kuwa"

Fadin ikram da munira a tare kamar yadda suka saba duk wani lokaci danayi yar kankanuwar kwalliya balle yanzu danayi makeup sosai,  tashi nayi ma nufi dogon mirrow din dakin ina duban kaina ta cikinsa.....I was speechless too dan wata halitta nake ganowa kamar bani ba, ban taba sanin purple color tana da matukar kyau haka ba!
Na tuna lokacin da ake zabar material din, I chose the color badan komai ba sai dan sabida baby pink din danakeso na lura shi ikram takeso, hakanne yasa na bar mata shi na dauki purple din.....nd it turns out a very good decision!

Kafata na zura acikin heels dina na shima purple just like my clutch bag, pictures da video Mai makeup din take ta mana har saida muka tsayar da ita, itama ta tattara komatsanta ta bimu sabida da an ajiyemu driver zai mayar da ita gida,  lokacin da muka fito compound din mu saida muka rena kanmu sakamakon wani sanyi daya ratsa mu kamar ana snow, dukda dinkin da akayi mana long sleeve ce but it is extremely cold,
       Munirah ce agabanmu dan tafi mu sauri sabida tafimu kwarewa da tafiya cikin heels, muka isa gate din muka kwankwasa dan masu gadi su bude mana ta waje, bude kofar da akayi yayi daidai da shigowarshi kamar dama jira yakeyi munira tayi knocking,

Gabanmu ya yanke ya tsinke ya fadi kasa wanwar da ganin YA ALIYU,

"Innalillahi, ya Aliyu!"

Ikram ta fadi a hankali tana jin tabbas basu da Rabo a dinner dinann Ashe

"Yaushe yazo ne ma?"

Na ambata a hankali nima yanda iky dake gefena ce kawai zataji,

Sanye yake cikin wata Farar Hoodie mai dogon hannu da kuma wandon sojoji, hannunsa sanye cikin aljihunsa lokacin da ya shigo tare da Abokinsa Farouk,magana suke yana dan murmushi kadan amma da ganin yaran fuskarshi ta hade ta kuma murtuke tamkar bai taba murmushi ba, daya bayan daya yake binsu da kallo har ya iso da kallonsa kan Afifah! Zuciyarshi ta kada ta yi rawa a kirjinsa har saida ya sauke ajiyar zuciya. Ina yaran nan suke nufin zasu je a haka?

"Me kukeyi anan?"

Ya wurgo musu tambaya tunda an rasa mai magana acikinsu kamar kurame, wata tambaya sai kace bai san abunda akeyi agidan nan ba.

"Yaya Aliyu wajen dinner zamu tafi, baba musa yana waje yana jiranmu Kum.....""

Iky tayi shiru sakamakon wani kallo da yayan nata yake watso mata ,ita kam tasan tasu ta kare.

AFIFAHWhere stories live. Discover now