page 10

96 9 0
                                    

Shirye shiryen tafiyar mu Umra yanata dada kankama , farin cikin dake zuciyoyinmu musamman ni, Iky, munira da Rais baa magana dan mune bamu taba zuwa ba. Bamu da wani zance sai na in anje umrah ga abunda zaayi ga abunda zamuyi, takanas naje wajen abba nace zan duba library dinshi dan na taba cin karo da wani littafi mai sunan "ladubban Hajj &Umrah"a book shelf dinsa, aikuwa naga littafin kuma daga ranar ya zama abun karatuna, zaunar da su iky nakeyi ina fada musu do's and don't's din dana koya a book din.
          Abba ya bamu kudi masu yawa mukaje wani sabon shopping mall muka sayo sabbin kaya mostly Abayas, sneakers da crocs da kuma mini bags har da sabon akwati da zamu sa kayan mu,  zuciyata a bude ainun nake jinta iska na shiga cikinta har ma yayi Mata yawa....amma inaji ajikina cewa wani abu na shirin faruwa dazaiyi sealing wannan mahudar da nake ji, something is coming to complete me, maybe it will be the sight of the Kaaba.
          Wani sabon Alamari daya bijiro a rayuwata shine Tunanin Yaya Aliyu, I don't know how , when or where that comes from actually nide na tsinci kaina da tunaninshi da kuma burin ganinshi ako yaushe, wani abun mamaki kuma shine kamar yasan muradin dake zuciyata sai ya dawo cin abincin dare a bangaren yakumbo,duk dare bayan sallah isha zaizo shi kadai ko shi da faruk wata Rana suci abinci anan, naji dadin hakan ko ba komai ya sa taron meeting din dasu sabirah keyi an daina yanzu. 
          Idan sukazo yakumbo zata kira ni na kawo musu plates da ruwa wani sain da furar datake damawa duk dare, idan na fito kawo mishi bana yadda na hada ido dashi amma inajin nauyin wasu idanuwa akaina , wannan wani nauyi ne da ban taba jin makamantan shi ba, wani nauyi ne dayafi duk wani dutse nauyi......idanuwan ya Aliyu a kaina sunfi komai min nauyi kuma sunfi komai dadi.

Wani sain sai na tsinci kaina da leke ta window inda nake hango parking lot, na riga na Fara haddace lokutan fitansa da dawowarshi, I see that he has a strict time for everything, duk karfe 9pm na dare ka leqa zaka tarar ya dawo ya ajiye motan, da kanshi yake wanke motarshi da kanshi yake chanja spare tyres ko yasawa motar shi ruwa, wani sain da yamma zaka tarar dashi da few of his friend sunzo sun sa fararen kujeru sun zauna suna hira, zakayita jiyo muryar su amma baza ka taba jin ta yaya Aliyu ba. 
        Wata magana mai tsawo bata kara hadani dashi ba tun ranar da muka hadu bayan incident dina da Ruman, bai kuma ce min komai about it ba nima kuma ban san ya sukayi ba amma tabbas naga chanji daga gareta, bata shiga harkata bata min magana nima kuma haka, ko kitchen na shiga yin wani abun na tarar da ita suna hira sai naji tayi shiru kawai ko kuma ta fita gaba daya, I like it that way dan dama ni ba wani muamala yake hada ni da mahaifiyarta ba balle ita kanta. A bakin munira Nake jin labarin cewa har da ita Daddy Rufai ya biyawa Umra da zamu je, naji mata dadi dan ni mutum ce mai wishing kowa well, banida matsala da kowa kuma a zuciyata bana yiwa kowa fatan komai sai na alkhairi.
          Ana gobe zamu tafi maiduguri gidan Shehun Borno daya kasance  aminin Abbanmu dan Daga can zamu shiga jirgi zuwa birnin Riyadh, nida ikram muna dakin yakumbo Ina karasa shirya mana akwatin mu nida yakumbo, hijaban yakumbo nake linkewa ina jerawa acikin wata karamar jaka dana sa nawa hijaban jilbabs da aka kawo mana daga wajen dinki dazu,  ikram tana daga zaune akan gado  tayi shiru da alamun magana a bakinta, da haka nake gane iky in tana da maganar da zata fada min, sai tayi Shiru tayita bina da kallo bakinta yana motsi, zuge zip din jakar nakeyi kuma ba tare da duban ikram din ba nace,

" inajinki iky, what's popping?"

Rufe fuskarta tayi da tafin hannunta cikin jin kunya,ga wasu butterflies acikinta suna ta kaikawo, mamaki takeyi Dama ashe akwai wani abu dazai sata jin butterflies bayan butterflies din da takeji idan taga lukman wani classmate dinsu?

" Don't ask Afy, its crazyyy"

Iky ta fada tana gyara turban din kanta black color,

" please Ki fada min kinsan na tsani a lasa min zuma a baki ayi shiru"

Na fada ina hararar iky, dama ita haka take akwai jan magana,

" nima a lasa min zumar toh"

Muryar rais ta furta ta wajen window, rais shugaban yan laben duniya kenan, tsaki nayi na tashi na janyo curtains din dakin muna dariya, 

AFIFAHWhere stories live. Discover now