page 33

75 9 0
                                    

3 weeks Later.

Friday Night.
Abuja.

1:Am

Cedarcrest Hospital.

Katoton Unit din dake dauke da jerin dakuna kala kala nan ne Bangaren da labour wards da kuma rest rooms harma da nurseries na babban Katafaren Asibitin wato cedarcrest,  duk wadanda ke shige da fice a ta nan bangaren daga jiya da safe zuwa yau toh tabbas zai shaida cewa duk yadda akayi akwai matar soja dake bangaren zata haihu ko kuma ta haihun sakamakon sojoji guda biyu dake Tsaye Kikam suna gadin kofar shiga Unit din. Su kansu ainihin securities da aka ajiye dan gadin kofar tuni suka bar wajen tunda ance dama gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta.
            Karfe daya na dare a lokacin kuma babu laifi kafa ta dauke sosai a asibitin amma still akwai yan jamaa kadan dake shige da fice kamar yadda akasan asibiti dai baa rabashi da alumma, Sadaukin Afifah ne ya fito daga madaidaicin masallacin dake kusa da gate , Fadin irin tashin hankalin dayake ciki baya misaltuwa shiyasa ya koma masallacin yayi nafilfilu ya rokarwa matarshi sauki da kuma rangwame a wajen ubangiji, ya saka takalmanshi sawu ciki ya durfafi Ward din cikin tafiyarshi dinnan mai daukar hankali mai cike da Isa da kasaita, a fuskarshi haka babu wani alama ta damuwa amma zuciyarshi da ruhinsa? Fire!
          Sojojin guda biyu sukayi saluting dinsa lokacin da ya shiga wajen, a waiting area din babu mutane dan baifi mata 4 bane a zaune wanda dukkansa fararen fata ne da alama suma sun kawo yan uwansu ne zasu haihu, Yakumbo ce kadai bakar fata acikinsu kuma tana zaune ta jingine da bango da alama bacci ne ya dauketa ba tare da ta shirya ba, Carbi ne a hannunta amma har ya sulale kasa ya fadi, Aliyu yana isowa wajen ya zauna kusa da yakumbo ya dauki wannan carbin daya fadi kasa ya rike a hannunsa gam yana dubanshi....pink dashi yanata walwali kamar da duwatsun luu luu aka yishi, hannu yasa kadan ya dafa kafadar Yakumbo tare da fadin

" Yakumbo"

Firgi git ta farka tana fadin itama da sauri

" yaya Aliyu? Ta sauka ne?"

Girgiza mata kai Aliyu yayi alamar Aa, yafi awa guda baiga motsin wucewar Dr prateek ko wasu daga cikin nurses din ba, tunda suka shige ciki da yayayen jamaa basu fito ba , hakurinsa yana karewa dan gab yake da kutsawa cikin labor rooms din ya ganewa kansa halin da matarsa ke ciki.

" oh Allah na ni bilki, Allah Allah ka gajarta wa yarinyarnan nakuda, Allah ka yanke ka rabasu lafiya"

Yakumbo ta fadi tana daga hannayenta sama cikin alamar rokon mai duka, abunda kadai zata iyayi ayanzu kenan tunda dik rubutun dake hannunta taba Afifan tasha tun jiya da aka kwantar da ita kafin nakudar ma tayi tsanani haka. Aliyu ya amsa ameen a zuciyarsa yana jin tayi mishi nauyi da yawa, kamar nauyin duk duniya yake dauke dashi a yanzu. Kwata kwata bai tsammanin abun zai zama haka ba duba da ajiyan ma da kanta ta kawo kanta Asibitin batare da yasani bama yana wajen aiki.

" Yakumbo bari na kira Imran yazo ya Maidaki gida inyaso gobe da safe sai ki dawo, kafin nan ma ta haihu inshaa Allah"

Aliyu ya fada cikin son lallaba yakumbon coz she's too exhausted also, tana bukatar hutu itama. Yakumbo ta kekeshe kasa tace babu inda zata motsa daga nan, babu yanda ya iya ya hakura ya kyaleta. Mikewa tsaye yayi yanata zagaye a waiting area din Yaje can ya dawo cikin tararrdadi. He wants to see his wife, he wants to be with her now.
       Ko minti 5 baa kara ba wata nurse itama Indian ta fito dauke da wasu trays zata wuce,  isa tayi ga wata dattijuwa dake zaune can kusa da yakumbo ta fada mata cikin yarensu cewa jikarta ta haihu, yanda tsohuwar ta hau murna harda hawaye shima yaji hawayen ya ciko mishi a ido. Bin nurse din yayi da sauri ya gaya Mata Cewa yana bukatar ganin Dr prateek da gaggawa, nurse din ta bude baki zata masa musun cewa Dr prateek is very busy now amma ganin irin hade rai da Aliyu yayi yasa ta hadiye maganganunta ta koma ciki da sauri. Baafi minti biyu ba saiga Dr Prateek ya fito sanye da Hospital robe blue color irin nasu na likitoci, dan gajeren baindiyen likitan ya fito ya dubi Aliyu yace

AFIFAHWhere stories live. Discover now