Page 44

71 9 0
                                    

Ranar Eid
Shehuri Palace
Maiduguri.

6:15Am.

Daga can kuryar kasaitaccen parlon Yarima Massa wani Treadmill ne babba kuma sabo dashi mai cike da kwari da inganci ko a ido, Bisa treadmill din YARIMA MASSA ne akai yana gudu akansa, a hankali kuma yana kara gudun abun, harta kai da yasashi phase din dake kusa dana karshe. Sanye yake da wani Sweatpants Ash color ,babu riga ajikinsa dan tunda ya dawo Sallar asubahi ya cireta ya ajiye akan nan kujera dake falon.
          Tun dawowarsa daga Masallacin Masarautar ya haye kan treadmill din kamar yadda ya saba tunda baya yin baccin safe yanzu, tun wasu shekaru 5 da suka wuce ya nemi kaso 70 na baccinsa ya rasa ciki harda baccin safe, saidai yaga anayi. Yau ce Ranar Sallar Eidi karama kuma a matsayinsa na Yarima Massa mai jiran gado hakan na nufin cewa yau babbar rana ce a gareshi, ranar da zaa wuni ana zaman fada bayan an sauko daga hawan Sallan, So much is expected from him musamman kasancewar mahaifinsa bashi da cikakkiyar lafiya dan tun jiya aka sanar da cewa bazai samu damar halartar Sallar eidin ba.
           Towel din dake rataye a wuyansa ya janyo ya goge Gumin dake tsilalowa yana bin sassalkar fatarsa mai tsantsi da sheki, Gudun dayake ya fara yin yawa , yanda kirjinsa yake bugu da karfi fat fat fat yasan cewa ba abune mai kyau yakeyi ba but he doesn't wanna stop. He actually doesn't mind his heart stopping right now aganinsa zaifi mai sauki akan uban nauyin dake jiransa, Nauyin dake shirin hawa kansa na mulkar kasa irin ta bornu, nauyin mulkar masauratarsu da dumbin mutanen dake cikinsa ko kuwa nauyin idanun Matarsa MUNIRA dayakejin fiye da shekaru 4 baya iya kallon cikin kwayar idanunta, duk a ture wannan ma, Shi a karan kansa har yanzun bayajin kansa, he doesn't feel him self to the extent da zai iya daukar nauyin mulki, nauyin dayakeji a kirjinsa tun wannann yammaci daya tsinci kansa durkushe agaban gawar Aneesah bai kuma dawowa daidai ba, Tashin hankali da balain daya tsinci kansa a prison din america tsawon watanni 4 has completely ruined him.....part of him died 5years ago, meyasa akeso sai ya tashi bayan abunda ya mutu baya tashi?
            Ya kashe abun exercise din ya sauko sannan ya fito harabar kasaitaccen falon nasa mai matukar girma da alfarma, kafafunsa suka nutse cikin lallausan Persian carpets dake shimfide a falon iya ganinka, Wani madaidaicin fridge dake gefe ya isa ya dauko ruwan roba na Nestlé mai matsakaicin sanyi ya murde bakin ya kafa a baki yana sha, da ruwan ya tafi Bedroom dinsa ya bude a hankali idonsa na kan ta tana baccin ta cikin kwanciyar hankali.
           Yasan tana fashin Sallah shiyasa bai tasheta ba tun dazu, yanzun ma baiyi niyyar ta tashi ba amma yau babbar rana ce ya kamata ta tashin, ya isa ga curtains din dakin ya janye hasken safiya ya ratso ta cikin dakin, duvet din data rufa dashi har kanta ya yaye mata aikuwa fatarta mai kyau ta bayyana. Yan yatsun kafarta ya dinga ja a hankali yana dan mata susar kafa kadan kadan duk dan cikin son ta tashi ta wartsake. Tana jin duk abunda yake mata amma baccin yayi mata dadi bata son ta tashi Sam, yasan yanda kafarta take very ticklish shiyasa yake tashinta ta wajen, akarshe dai ta bude idon sosai tare da mikewa zaune ta jingina da kan gadon mai girma da fadi tana fadin,

" Na tashi King...na tashi"

Murmushi kawai yayi Sannann ya shige bathroom din dan yashirya a gurguje ya fita, Sallar eidin a masallacin gidan sarki karfe 8 ne kuma yanzu har 7 ta gota,  saida Muneera tayi kamar mintuna 5 tana kara watssakewa daga baccin sannan ta mike ta nufi kan wata Sofa inda rigar baccinta take ta zura, dama babu komai ajikinta sai Period pant dinta kadai. Kamar yanda Massa ya koya musu rashin kwana da kaya, ta riga ta saba sosai dan indai ba period take ba ko pant bazata iya kwana dashi ba.
          Saida ta gyara gadon a gurguje ta dauko Vacuum cleaner karami ta dan share carpet din duk da bawani datti yayi ba, Sauri takeyi taje ta shirya dan taki jinin ace Miji ya rigata shiryawa, tana fita falon ta bi corridor dazai sadata da bedroom dinta, Dakuna 3 ne dauke a corridor din, daya nata, daya nasu Nina sannan dayan kuma spare kawai sai aka mayar wasu Nina study room. Dakinsu Ninan ta kalla  tanajin kewar su a ranta, kusan watanni 3 kenan da Yaa Gumsu tasa aka tattara komai nasu suka koma sashinta, acewarta ita Yagumsu wai Munirah ta koya musu rayuwa irinta yaku bayi alhalin they are royal blood, shiyasa tasa su koma can dan alada da dabiu irin na sarauta su shiga jikinsu yanda akeso, tsakaninta dasu saidai su shigo su yini idan sun dawo school ko kuma idan ita ta shiga bangaren yaagumsun, abubuwa tsakaninta da Mahaifiyar Massa sun kara rikirkicewa tun bayan dawowarsu Nigeria Shekaru 4 da suka wuce, Things aren't going on well tsakaninta da Yaagumsu da wasu daga cikin yayyen Massa mata....her only support is Him and he alone!
            Wardrobe dinta mai girma da tsayi kamar katanga ta zuge , kasancewarta mai matsakaicin tsawo yasa bata ma dora kayanta acan saman sai iya yanda tsawonta zai kai, duk da kuma akwai yawaitar kuyangu masu mata hidima amma ta kasa sabawa da sai an mata komai kamar yadda dik suke musu acan bangaren surukarta, abu daya da tasan bayi na yi mata shine bangaren kitchen, Abinci saidai kawai taga anshigo dasu an fitar dan ko hanyar royal kitchen din bata san inda yake ba.
             Sabuwar hadaddiyar laffayarta da aka kawo mata daga wajen kabbasa jiya ta janyo ta ajiye akan gadon, tuni dakin ya cika da kamshin Kabbasar da aka tsuma laffayar da shi tamkar an kunna turaren wuta a lokacin, kamar yadda aladar gidan take duk Sallah YaaGumsu ce zata aikowa surukanta mata da kyautar laffayar da matan zasu sanya a ranar Sallah su kuma halarci Sallar idin da ita,  Laffayar ta kasance ta alfarma mai matukar tsadar da tafi ta kowa kyau da Tsada saidai bazata kamo na YaaGumsu ba, tun dawowarta Nigeria shekaru 4 kenan ake aiko mata da laffayar duk Sallah, kuma har agama shagulgulan Sallah baza a taba ganin laffaya mai shigen irin tata ba, acewar wata kanwar Massa mai Suna Fandy wai laffayar a hadaddiyar daular larabawa ta kasar dubai ake dinka irinsu kuma ake musu ado da duwatsun diamonds, the clothes are strictly meant for Queens and princesses.
         A hankali ta cigaba da duk shaanin wankanta a bathroom sabida tasan ba zuwa filin eidin zatayi ba, duk da bazatayi sallar ba tana son zuwa amma gara ta hakura akan taje ta zauna kusa da Yagumsu har ta fahimci cewa ba sallah zatayi ba, tsakaninta da uwar mijinta akwai kunya sosai dan ko kadan Yagumsu bata sake Mata. Bayan ta fito ta gama shafe shafen manta da Body oils kala kala Sannan ta Saka Atamfarta Holland riga da zani, sai ta dauko wannan laffayar ta warwareta tanajin yanda takeda da dan nauyi sakamakon duwatsun dake jikinta, Laffayar fara ce tas sai bakin lace din Gold color, ta daura ta cikin kwarewa sannan ta janyo wata drawer dake zube da tarin gwalagwalan jewelries dinta. Mintuna kalilan ta fito a asalin babarbariya matar Yarima Massa mai jiran gado,  tana fita falo ta fara jiyo bushe bushe na algaita da sauran kidade irin na sarauta alamar cewa an sauko Sallar idin, her mind lit up with excitement na sallar, wani farin ciki da duk wani musulmi yake ciki a ranar Sallah, tana isa Dining Area ta iske masu mata hidimar kitchen na bangarenta suna ta jera Warmers na alfarma da jugs jugs masu dauke da kunu kala kala irin na aladarsu.
          Kisre ( Sinasir) guda biyu da miyar yakuwa mai aikin ta zuba mata tanaci a hankali, wayarta take dannawa ta kira Abbanta, ummanta da sauran yayyanta tayi musu barka da sallah, tayi niyyar kiran Ikram da Afy amma sai ta bari anjima idan ta dawo saita hada musu conference call. Da sauri sauri ta gama ci tasha ruwa dan tasan cewa ita mai laifi ce awajen Yagumsu tunda bata halarci sallar idin ba kuma bataje wajenta ta mata barka da Sallah ba. Sink din dake gefen dinning ta wanke hannunta da handwash mai kamshi sannan ta gyara zamar laffayarta, ta dauki purse dinta dake cike da kudade sabbi fil da Massa ya bata a daren jiya wanda zatayi hidimar barka da salla dasu.
           Tana fita a sashinsu tare da wata kuyangarta dake take mata baya ta Fara cin karo da mutane kala kala suna zuwa su Fadi suyi  mata barka da sallah, haka zata bude jakarta ta ciro kudi ta basu sanann ta karayin gaba, kusan kowani zaure da tsakar gida na masarautar sai da tayi barin Kudin da ita kanta batasan iyakarsu ba, da kyar da sidin goshi ta samu ta tsallake ta shiga bangaren Yaagumsu, saida ta wurwuce faluka kusan Uku kafin ta isa wawakeken Falon da Yaagumsun ke karbar gaisuwa, ta labule inda ta cire takalmanta tana hango Yagumsun da yayyen Massa Mata da suke garin su 4 sun zagayeta, wasu matan ne a zazzaune daga baya suna ta gaisuwa wasu sai su tashi su tafi yayin da wasu suja gefe su zauna,  tana shiga falon wasu mata daga gefe suka fara yin guda tare da mata kirari a matsayinta na matar Yarima daya kwallin jal duk fadar.
          Da tana da damar hana matan yi mata wanann kirarin da ya hana dan ta jima da sanin cewa abun baya yiwa Yaagumsu da yayyen Massa dadi, duk da bata kalli fuskokinsu ba amma tasan cewa tuni farin ciki da annushuwa ya bar fuskokinsu, bata kai ga zama ba taji muryar Neena da Fanna daga bayanta suna fadin

AFIFAHWhere stories live. Discover now