page 28

98 10 0
                                    

Kano,

Ranar laraba.

12:30pm

Katoton gida ne na bene mai dauke da zagayayyen katangu dogaye , motoci ne kala kala a fake a harabar gidan masu tsada da masu rangwamen kyau, wasu daga cikin motocin na mai gidan ne Alhaji Ahmad, wasu kuma na baqi ne da suke ta zuwa barkar haihuwar da akayi agidan.
        Daga gefe ta bangaren da dakin generator yake famfo ne awajen da wani zagayyayen waje da ake wanke wanke da kuma wanki, UMMU RUMAN ce zaune akan wata karamar kujera tana ta dirzar kayan wankin dake cikin robobin nan kamar Allah ya aikota, kayan sunada yawa sosai tun daga kan na jaririn dakuma na uwar jaririn harda kuma daidaikun nata data jima bata samu damar wankin ba.
        Rana ake tsalawa duk da garin na damuna ne amma kai kace baa taba digon ruwa ba, rana ta take sosai kuma wajen famfon bashida rumfa ba kamar wajen parking motocin ba, saida ta gama wanke na jaririn Tas sannan ta dawo kan na mai jego, wasu daga cikin zannuwan akwai wanda jini ya bata , tana kyankyami tana komai ta sa hannunta ta wanke su suma sannan ta zubar da ruwan ta tara wani ta dan zazzaga omon ta fara cuda nata kayan cikin sauri sauri kafin wani yazo,
          Bakin cikin rayuwa, bacin rai gamida tausayin kanta su suka sa zubar hawayenta batare da ta shirya ba, tana daurayar kayan tana share hawayenta dake fita daya na bin daya. Yau satinta na biyu agidan Husna yar Kanwar mahaifinta mai suna Anty sailuba, tun da husnar ta shiga edd dinta akayiwa mahaifinta waya akan ta bar duk abunda take tazo gidan husnar data kasance kanwar kanwarta, dan akalla zata ba husna shekaru 5,babu shiri malam ya ce maza ta hada kayanta tawuce gidan husna dan shima yasan bai isa ya saba umarnin kanwarsa sailuba ba.
        Anty sailuba ita kadai ce wanda Allah ya nufa da arziki a kaf danginsu gaba daya kuma itace karamarsu, Allah ya taimaketa ya zabota acikin garken yan gidansu yasa ta auri wani alhajin birni Wanda tun a lokacin ma ya girme mata sosai amma ya kasance mai tarin dukiya, tayi aure ta haifi yayanta duk mata kuma husnar itace ta biyun auta. Anty sailuba da wuri take wa yayanta mata aure kuma mafi yawanci alhazawan birnin suma suke aure, wssu daga ciki ma abokanan mahaifinsu suka aura, ita husna itace ma ta auri saurayi dan abokin abbansu wanda ya kasance mai tarin dukiya kuma mai rawa da bazar ubansa.
         Kasancewar Anty sailuba itace mai kudin dangi yasa babu mai iya tsallake maganarta, ya zamana itace ta dawo ubansu, uwarsu da kuma babbar yarsu gaba daya, itace take dan taimakawa dangi da abinci , sutura harma da zakka idan mijinta zai fitar. Sailuba macece mara kirki  , izza da girman kan balai duk a sanadiyar ganin tafi kowa abun hannu acikin zuriarsu, bata da zumunci na tsakani da Allah sai in gani tayi zata mori yayanka, haka take dauko yayan yanuwanta suyi mata wahala ita da yayanta idan abun wahalar ya tashi kamar dai yanzu da ta dauko Rumanan tazo tayi bauta agidan kanwarta duk da tarin masu aikin da suke dashi agidan.
          Malam mahaifin Rumana ba yadda ya iya dole ya tura rumanan sabida yasan ita kadaice zata yarda taje dan ita kadai ke jin maganarsa, su Hafiza daman bai isa dasu ba dan suma ba shiri suke da Anty sailubar ba, uwaka ubanka suke da ita. Dalilinsa na kara tura rumana shine dama yana fata wannan karan ya samu gurbi acikin list din zakkar da zaa fitar agidan sailubar wanda shekara 3 kenan rabonsa daya Samu , yana fata taji dadin zuwan rumanan ta tuna dashi a rabon azumi dasauran yan abubuwan datake gutsurowa ta bashi.
          Bayan ta gama shanyar a bayan gidan ta tattaro bokitanta tana jin yanda kanta ke sarawa, ta gaji matukar gajiya ga yunwa dake kwakular yayan hanjin ta, Rabon ta da abinci tun jiya da dare da aka sauko da abinci daga dakin mai gidan suka samu suka kara ci itada daya daga cikin masu aikin gidan wanda tasu ta danzo daya, 

yunwa da Rowa! Tana daya daga cikin Babban kalubalen datake fuskanta agidan husnan, abinci gashi nan Iya abinci amma bazaa dafa mai yawa ba duk yawan masu aikin da masu gadi amma shinkafa baa dafa kwano, aciki zaa dibarwa uwar mijin husnan dasu kansu da ita mai jegon da mai gidanta harma da bakin da suke dan lekowa akai akai, tun kafin husnan ta haihu ita take saukowa kullu yaumin ta debi abincin a store sanann ta mayar da kofar ta datse da mukulli, idan an gama kuma ta sauko ta dibarwa flask din maigidan da nata sannan ragowar na tukunya Su sukasan yanda zasu kasa su ci a tsakaninsu. Dalilin dayasa barna tayi yawa a gidan tsakanin masu aikin mata da maza, rayuwar holewa ake ba tare da sanin masu gidan ba duk dan sabida rashin wadataccen abinci.
           Ranar da Rumana tazo gidan harga Allah tayi zaton matsayinta yafi na masu aikin data tarar, sabida acewar Anty sailuba shine zatazo tadan zauna da husna kar a barta ita kadai sannan ta dinga duba masu aikin, sai gashi reshe ya juye da mujiya tun a washe garin ranar data zo gidan ta fara karbar umarni daga husnan na aikace aikace, a hankali a hankali har aikin da take ma yafi na masu aikin, a cewar husnan wai tafi jin dadin aikin rumana sannann tafiyi tsakani da Allah.
          Ko idan ita Anty sailuba da yayyen husnan sunzo gidan tun kafin ayi haihuwar da bayan anyi haka suke nuna kamar basu san daga inda tazo ba, bakin ciki kala kala suke guma mata da nuna mata cewa ita fa baa bakin komai take ba sannan ita ba yar kowa bace face diyar talaka futuk.  zaa iya cewa bakin fentin da Umma zulai tabarwa diyar tata guda da ta haifa agidan malam din, zaman datayi da shi da danginsa mara dadi ita tasa suka kasa mancewa kuma suke ramashi akan rumanan yanzu da lokacin ramuwar tazo, dan umma zulai har dambe ya taba shiga tsakaninta da sailubar agidan biki kuma har hanci aka fasawa sailuba, wannan ba karamin Kara hura wutar gaba yayi ba a tsakaninsu , yanzu a hakan ma wai sailuba ta manta komai ne kuma tana jan rumanan ajikinta.
            Hayaniya ce agidan musamman saman inda mai jegon da yan uwanta ke zama su kadai suyi bidirinsu kuma suyi shirye shiryen sunan da zaayi jibi, tsakaninta da saman sai idan kwala kiranta akayi ko kuma taje gyran daki da safe da kuma tattaro kwanukan da akayi amfani dasu, a kasa dakin da uwar mijin husnan take anan rumana take kwana ita da Yar tsohuwar mai fama da lalurar gani, kamar yanzu data shigo dakin da sai ka rantse baa gidan yake ba sabida rashin kyan gani, kayan dakin sun tsufa ainun , labule da dirowoyi duk sun tsufa sun balle kada ma bayin yaji labari, ga wani wari mara dadi dake sirnanowa daga both dakin da bandakin sabida rashin kula da bawa dakin muhimmanci.
        Ayanzu ne da rumanan tazo yake dan samun shara da wanki ba laifi duk da ita rumanan a hakan bataga wani aibin dakin ba compared to nasu gidan da ta baro, aranta kawai dai tasan mahaifiyar alhajin ta cancanci fiye da wannan dakin ko da ba irin na husnar ba, amma batayi mamaki ba dan tun zuwanta gidan baifi sau 4 taga alhajin ya shigo duba mahaifiyarsa ba, saidai hana karya kullum dare hajiyar tana da nata kullin nama da yoghurt, sai kuma magungunan dayakan aiko ya akawo Mata amma fa bashida lokacin zuwa duba uwarsa ido da ido.
           Hajiyar na sallah akan kujera Rumana ta shigo dakin idanta yayi jaa sosai , burinta ta zuba ruwa ajikinta ko zata samu kasusuwanta su sake daga rikewar da sukayi, ta shiga ta bude durowar hajiyar ta janyo Mata yar rigar da ta ke sawa dakuma man shafawarsu ta ajiye agefen hajiyar , hajiyar tana sallah ta gyada mata kai alamun ta gode mata.
         Rumana ta cire kayanta ta daura wani tsohon zaninta na wanka kamar an fito dashi daga bakin kura ta shiga bandakin ta kunna famfo ta fara wankan da ruwan sanyin , ko neman ruwan zafi batayi dan ba sabawa tayi dashi ba kuma heater dakin ma batayi, ta gama wankan ta fito ta shirya cikin wani riga da zani sanann tayi sallar azahar, idan tazo yin sujjada tana jin kamar kanta zai guntile, tasani ya kamata ta nemi magani amma tasan yunwa ce. Ruwan bunun da guntun biredin da takesha da safe baya isarta sam, koda can agida duk talaucinsu amma suna samun dumame suci ya samu yadan rike musu ciki amma banda nan, abincin daren ma lasawa ake balle arage ayi dumame.
       Ta idar da sallar ta jingina da bangon tana lulawa tunanin da bata da aboki sama dashi ayanzu, tunanin da tana da tabbacin shi ke ramar da ita tun watanni da dama da suka wuce tun bayan dawowsrta daga wajen ummanta, ta dawo daga yobe cike da burika Kala kala da jin cewa rayuwa ta kusa chanja Mata tunda ta samu alkawarin mahaifiyarta na cewa wai Yaya Aliyu zai soma kaunarta harma ya nemata wai......wannan itace gagarumar karya da kuma yaudarar kai mafi girma datayiwa rayuwarta.
          Ta cuci kanta KO tace ummanta ta cuceta domin tabbas ta kaita ta baro, tasa mata abubuwan da babu su Kuma bazasu faru ba acikin kanta, a hankali itama ta fara mafarkin yaya aliyun kuma wasa wasa kaunarshi tayi mata mummunan kamu fiye da zato, dalilin hakan ne yasa tayita wulankanta buharinta da iye shege kala kala wanda ko kare bazai ci ba.
           Tabbas buhari ya karbi gashi a hannun rumana fiye da yanda yake karba ada can tunda dama bawai tana ganinsa da kima bane, ta yarda dashine kurum a rashin kowa sannan Kuma da ganin irin tallafin dayake bata a rayuwa, buri da kuma mafarki irin nata na ganin ai kamar ta shiga gidan yaya Aliyu tagama ne yasa tasaka kafa ta wancakalar da dan sauran mutincin dayarage tsakaninta da buharin, Buhari mutum ne mai zuciya da neman nakai duk da ya kasance talaka amma yasan mutuncin kansa, kaunar dayakewa rumana kauna ce sabida Allah amma sai da takai ya hakura ya kuma tura a karbo masa kudin aurensa dayakai sannan aka warware zancen baikonsu.
           Kamar yadda akazo aka karbi kudin auren da kuma warware maganar haka malam ya warware jikin rumana da duka a wannan Daren, haka ya sata a daki ya jibga ya kuma huce takaicinsa akanta dan da baikon nata yake samu ya rage radadin rashin auren sauran yan uwanta, ita yana jin tausayinta kuma yana farin cikin ganin zata auru amma gashi an fasa,  tika tikan yan matan gidansa dasu yake kwana yake tashi a Ransa, 
         Da fari rabuwarta da buhari ko ajikin ta tunda tuni zuciyarta ta kawatu da tunanin Yaya Aliyu, hakan yasa bata ji bata ganin komai sai shi sai dan ragowar memory dinsu daya bar mata, dik duniya babu namiji irin yaya Aliyu a idon rumana ,ta wulakanta samari kala kala akan soyayyar maso wani data dorawa kanta dan baace Allah ya Dora mata ba, tana ta kirga ranaku da satuttikan da xaizo har inda take ya sameta kamar yadda mahaifiyarta tace AI zaizo amma shiru kamar an shuka dusa, alamu dai na babu wan kuma babu kanin tayi ga bakin cikin auren da bihari yayi shida wata makociyarsu anan layinsu, sunyi aurensu kuma sun tafi Lagos abunsu inda yake ciranin sa.
         Wani dare da bazata taba mantawa dashi ba shine daren da ta akayi sallama da ita, mai pos dinann ne wanda Umma Zulai take mata aike ta hannunsa, ya zo ya kawo mata sakon naira 20k cif daga mahaifiyarta, taji dadin aiken da ba ta da ko sisi dama ko sabulun wanka saidai su hafiza su sayo mata, bata bari mai pos ya tafi ba saida ta bashi 10K akan cewa ya je shagonsa ya kawo mata karamar waya ta kudin, a take ma ya ciro karamar keypad ya bata yace dama sayarwa zaiyi, ta karba Kuwa tasa Sim dinta ta danna kiran mahaifiyar ta , ta danji hayaniya sama sama kamar alamar ana gidan biki, 
Tasan wata Kika ummanta tana gidan biki sabida bukukuwan da ake tayi da bayan sallah , harta ajiye wayar ummanta ta kirata, ta dauka cikin zakuwa dan sun jima basuyi magana ba tun farkon axumi kafin wayarta ta lalace kuma bbau damar gyara dama buhari ne mai wanann aikin.

AFIFAHWhere stories live. Discover now