Page 46

158 12 1
                                    

            Makararren Goron Sallah....Nace bari na bawa masoyana barka da sallah tunda ku ba wanda ya tuna da Saadatu baiwar Allah. Eid Mabroor!

Ku bani Labari, kunyi kewar Afy?

~~~~~~~~~~~~~~~~
~~~~~~~~~~~~~~~~

Abuja, Nigeria.

10:50Pm.

Cikin kwarewa kyawawan yatsuntsa ke ta typing a kan System din, daukacin hankalinsa da idanuwansa na kan Laptop din yana ta shigar da wasu bayanai cikin kwarewa. Yana zaune akan madaidaiciyar Varendar din dake bangarensa daga Sama, iska ce mai dadi da sanyaya jiki da zuciya ke busawa , baa jima ba tun lokacin da Ruwan saman ya zuba kamar da bakin kwarya kuma yanzun ma wani hadarin ne.
               Farin siririn photochromic glasses din dake manne a idanuwansa ya cire ya ajiye agefe, Runtse idanunsa yayi yanajin yanda kansa ke wani sarawa, zai rantse yana jin harbawar jijiyoyin kansa, ahankali ya ajiye system din a gefe ya mike tsaye ya isa ga bakin balcony din inda yake iya ganin katafaren farfajiyar gidan nasa gaba daya, Hannayensa sanye cikin aljihun 3quarter pants dinsa na sojoji. Kokawa yake tayi da idanunsa akan kallon bangaren AFIFAH JAJERE, kwakwalwarsa na umurtar idanunsa da su kalli sashin koda sau daya ne shikuma yana yaqi da hakan.
                 Kwanaki 6 yau, Kwanaki 6 tun bayan faruwar alamura marasa dadi a wani dare dayake kira da "Bakin dare". Kwanaki shida tun da wani sabon shafi ya bude a rayuwarsa,tun bayan ya aikata wasu abubuwa dayasashi tunanin anya shi din ne, wani irin fushi da zuciyarsa ta dauka baya tunani akwai wani mai rai daya taba jin irin wannan bakin cikin da fushin, A wannan dare ya rasa zuciyarsa, wata tsoka mulmulalliya a kirjinsa da ada babu komai acikinta face AFIFAH da kuma kaunarta, shiyasa a ranar ya hada da ita kanta Afy din da zuciyar tasa ya barsu anan wajen, duk dan sabida me? Duk dan sabida kada ya cigaba da dakon soyayyarta!
                  Shin dama mutum yana iya sanin mace tsawon rayuwarsa, har ya aureta ya haifi zuriya da ita sannan kuma ya cigaba da jin sonta sabo fil kamar a ranar ya soma arba da ita? Hakan take gareshi shikam, Yaso Afy, ya mata son da ya tabbatar da duk wasu halittun Allah subahanahu wataala zasu bada shaidar wannan kauna rana gobe kiyama, ya mata son da har yanzun zuciyarsa na cigaba da doka Mata.....shikam Afy ce jarabawarsa a duniya.
             Mintsinin da zuciyarsa ta cigaba da mai ne yasashi kasa jurewa ya dan waiga kadan ya dubi sashin nata, babu hasken fitila ko daya dan yasa an sauke wutar bangaren nata gaba daya ta fuse, bayason ma yaga wata fitila ta haska ko guda daya. Kamar ya tsugunna a wajen yayita kurma ihu sabida jin haushin yanda har ya biyewa zuciyarsa yayi mata abunda ya saba da alkawarinsu tun tana mitsitsiya a hannun sa tana wasa.
           Idonsa ya hasko masa lokutan da yake rike hannayenta yana koya mata rubutu, ya koya mata homework, ya rike hannunta suje bayan layi su sayo chewing gum da alawa, ya share mata hawaye idan tana kuka ko ya zane su muneera idan suka fadar da ita suna wasa, ya tuna lokacin daya shiga NDA 1 ya dawo ya tarar da shatin dukan wani prefect a islamiyarsu, har islamiyar yaje ya tsintsinkawa prefect din mari ya Kuma sa shi ya bata hakuri a bainar jamaa kamar yadda ya zaneta a bainar jamaa. Lokuta barkatai da yasha kareta daga duk wasu abunki da abun cutarwa, he was and always been her protector....He showed her the best of love kuma yanzu ya tabbatar shi ya fara nuna Mata mafi munin pain.
            Zuciyarsa ta fara sassautowa ne tun bayan ya ziyarci asibitin sojojin dake wani barikinsu anan abuja, nan asibitin yasa Simon yakai imrana awannan Daren aka mai aiki, ya shiga dakin da Imranan ke kwance yana samun sauki, yayi baki sosai ya rame dan ko abinci baya iyaci sai kuka da nadama dayakeyi, sabida tsabar son ya tunano ko ya gano mugun daya hada wannan irin tuggu har kasa bacci yakeyi. Ya shiga ya cewa Imrana cewa ya fadawa Simon duk abunda zaa kawo masa dan daga nan ya tafi inda ya fito ya sallamesa kuma baya bukatar sake ganinsa, Aliyu ya ajiye masa albashinsa na wannan watan duk da watan ko rabi baiyi ba, fuskarsa a hade ya juya zai tafi yaji Imranan ya fadi abunda yasashi gane tabbas yayi kuskure.

AFIFAHWhere stories live. Discover now