Page 45

96 9 0
                                    

Thursday.

10:30Am.

Saaima ce tsugunne kusa da wani karamin akwatinta tana ta shirya kayanta aciki, idan tagama jerawa sai ta debo wasu daga drawerta ta zubasu cikin akwatin, gaba dayanta hankalinta baya jikinta sai sauri take zubawa kamar ana korarta, daga bakin kofa kuwa AFIFAH ce tsaye hannunta daya a kugu dayan kuma rike da hannun Kinan daya baza ido yanata kallon Saaimar tashi, daga jiya zuwa yau ya fuskanci cewa tafiya zatayi ta barshi kuma fushi yake sosai da ita. Afy ba yadda ta iya ne shiyasa kawai zata bar saaima ta tafi gida, jiya tana zaune a daki Saaima ta shigo kamar an jefota tana rokonta akan ta barta ta tafi gida gobe, ta tambayeta dalilinta na gaggawar saitace kawai ta jima tana mafarkin cewa mahaifinta bashida lafiya kuma inta Kira wanta dashi kadai ne mai waya agidan baya dauka.

" Anty dan girman Allah Ki barni naje, Allah kuwa zan dawo, dubosu kawai zanje nayi,hankalina duk ya tafi can...."

Fadin saaima ajiyan da taje rokar Afy ta barta taje gida. Bazata iya hanata ba dan gaba daya taga hankalinta ya tafi gidan, kuma dama ta jima rabonta da gida kusan shekara da yan watanni kenan, dama can Yakumbo ce karfin zumuncin dake tsakaninsu da mutanen jajeren.  Ajiya da daddare Afy ta kira Sergeant john ta ce yau da safe yayi wa Saaima shatar mota har gida dan akaita Yobe, daga can sai ta kuma hawa mota ta nufi jajeren, haka kuwa akayi da sassafe saiga john da mai mota ana jiran Saaima ta fito su tafi, dalilin tsayuwar su kenan a dakin dan suyi sallama.
              Saaima ta zuge akwatin ta dago shi sannan itama ta mike tana duban Antynta Afy da Kinan, murmushi take mai shikuma sai ya juya jikin mammansa ya rufe fuska alamun fushi, Saaima ta karasa gareshi ta ciroshi daga jikin Afy ta rungumeshi tsam ajikinta, kamar ta fashe da kuka takeji amma ta daure bata so Afy tayi zargin wani abu, ta saki kinan sannan ta janyo akwatin har zuwa bakin katuwar wooden door din falon, sanann ta tsaya ta jiyo tana duban Afy da wani irin nauyi akirjinta, wani abu takeji da bata da tabbacinsa amma tasan ba abu mai kyau tayi ba, Afy didnt deserve this from her amma bata da wani zabi! Kokari kawai take ta tserarta da rayuwar masoyinta da daga sharrin JOHN. Ta yarda ta bar Kinan na dan wani lokaci dan ta ceci IMRAN daga hannun john, tunda basason zamanta agidan da har barinta gidan ne kadai zai fanshi rayuwar masoyinta, a duniyarta babu wani abu mai maana dayafi Imrana, zuciyarta shi kadai take dokawa.

" Sati daya Saaima, kar ki manta fa...."

Fadin Afy lokacin da take sakawa saaimar wata envelope a yar karamar jakarta, Saaimar ta sa gefen hijabinta ta goge hawayen bakin ciki da guilt, idonta ya sauka akan Kinan dake zaune daga can kan Sofa yana dubanta, yana ganin sun hada ido sai ya kauda kansa. Ta girgizawa Afy kai alamun ta sani, sati guda kawai.

" Anty kicewa Hafsan ta dinga tayaki kwana mana kafin na dawo, basai ta tafi ba"

Saaima ta fada dan bata da tabbacin abunda zai faru idan bata nan, bata da tabbacin ainihin dalilin da akasa ta bar gidan, amma daga dukkan alamu ba lafiya bace, shiyasa ko yaya take son hafsan da zata dinga zuwa taya Afy aiki ta kwanan,amma Afy ta kiya, acewarta zata iya zama ita kadai har ta dawo.

" bakomai fa Saaima, wannan satin nake saran dawowar Sadauki ai, yanzu dai maza ku tafi Kada rana tayi.....Ki dinga sa wayarki a charge fa kada na kira naji shiru, Allah ya tsare!"

Afifah ta fada tana wa Saaima waving da hannunta, itama tana ta jin babu dadi dan Saaima bata taba tafiya tabarta ita kadai ba, ko inane tare suke zuwa. Saaima ta hadiye wani yawu dan wayarta bata hannunta tunda john ya tafi da ita,  hannu Kawai ta dago Mata tana fadin

" Ameen...Allah ya tsare!"

Ta fada ne kawai dan aranta takejin itama Afy tana bukatar wannan adduar, ta juya ta jaa akwatinta ta fita compound din har zuwa gate inda baba maigadi yake, dattijon ya taso ya bide mata yana fadi cikin tsokana

AFIFAHWhere stories live. Discover now