Page 48

84 9 1
                                    

And there is a city in my heart where you are its only population.
~AFIFAH

BLUCABANA
ABUJA, NIGERIA.

9:40PM.

" Farouq dagaske ruwa kawai zakasha?"

Colonel Aliyu jajere ya furta yana duban Abokinsa Faruk dake zaune opposite dashi, Waitress din ta ajiyewa Farouk ruwan a gabanshi sanann ta juyo kan Aliyu Shima ta ajiye masa Avocado milkshake tana wani rangwada tana jujjuya masa kirjinta da mazaunanta gari guda, ko kallonta Aliyu baiyi ba coz he didn't even notice at all, gone are the days da mata irin haka a abujan suke motsa shi, yanzu ko tsirara mace zatayi bata ita yake ba, abunda yake damunsa ma kadai ya isheshi.

" So, ina jinka....Kace da hannun UmmuRuman acikin wannan abun?"

Farouk ya tambaya looking straight into his friend's eye bayan yayi sipping cold lemon water da aka kawo mishi. Aliyu yana jinsa ya jinjina masa kai alamar eh, tafukan hannayensa na hade dana juna yana jijjiga su, yana sanye da wani kaftani Grey yard, kansa babu hula sai tarin lallausar gashinsa da wani saje daya ajiye....which totally unlike him coz of his profession.

" Rumaan is behind all this Faruk, I knew it since from day one, nayi bincike sosai, I interrogate wannan matar ta wajenta da john, naji komai kuma na fahimci komai......unfortunately"

Aliyu ya furta ahankali yana jin bakin cikin komai, Ruman tayi gangancin da har take tunanin yin wasa da karamar kwakwalwarta agidan security agent. Farouk ya kara gyara zamansa sannan yace

" kace ka gano komai, its lovely yanda still ta cigaba da zama agidan ka kamar komai bai faru ba.....you love her that much?"

Faruk ya tambaya,

" Her days are numbered in my house faruk, bata ita nake ba yanzu.....dalilin dayasa na kiraka kenan dan ka bani shawarar yanda zan bullowa Abba, This cannot go on like this , I can't anymore!"

Aliyu ya fada bayan ya sauke kafafunsa ya fuskanci Faruk sosai, shi kanshi yana danjin kunyar faruk din sabida yana sane da yanda gabadaya a shekarun baya ya dena wani hulda dashi sosai, he pushed his Friend away for years, sai yanzu da ya dawo hayyacinsa , guguwar rayuwa ta dawo dashi real world sannan ya gane cewa da gaske dai bashida aboki sama da Farouk din.

" You fucked up Colonel, you really fucked up! Sam baka bani tausayi ba Kuma ina bayan Afifah akan matakin data dauka akanka....She's worth more than you could ever think of, I'm proud of her da tasan kanta."

Faruk ya fadi yana duban agogon hannunsa, hankalinsa yana kan matarsa ikram da dansu, lokacin komawarshi gida har wuce.

" I know, I did fucked up and I'm more than ready to fix things, I want her back....even if it will cost my life faruk"

Aliyu ya fada cikin yanayi na tausayi, shi kanshi baisan yanda yake iya rayuwa ba kusan wata daya da Sati biyu ba tare da Afy da Kinan ba, ga mahaifinsa ya juya masa baya,wani irin fushi Abba yake dashi.

" Kace location din wayarta yana showing Eastern border?"

Faruk ya tambaya. Aliyu ya jinjina kai yace

" Sure, Niger kenan, probably Diffa.....hakan na nufin Abba took her to her Family as I least expect"

" you should calm down for now, ka nemi excuse a wajen aiki idan sun baka sai mushiga wajen Abba this weekend, zamu bashi hakuri mu rokeshi ya bamu address din su muje a dawo maka da iyalinka"

Faruk ya fadi yana mikewa tsaye, Aliyu shima ya mike yace cikin dan jin dadi kadan, irin wannann maganar yakeso yaji dama, yasan yanda Abba yakeson Faruk, yasan zaici albarkacin faruk din. Yace

AFIFAHWhere stories live. Discover now