page 17

63 8 0
                                    

Bayan fitar Aliyu daga parlon Abba ya wuce sashenshi ya cire kayan jikinsa yayi saurin watsa ruwa , yana zuba ruwan ajikinsa yana ganin yanda ruwan yazama gauraye da jinin daya fita a ciwunkansa da kuma jinin abokan aikinshi da suka faffalatsar masa, kamar yanda ruwan yake gudana haka yake son jinin duk Wanda ya sace Afifah ya kwaranya Till every drop of blood in the Animal's body dried up......koda jamaar da suke da hannu akai sunyi dari yayi alkawarin karar da su da hannunsa.
           Yayi maza ya fito ya soma jera sallolin dake kansa ,bayan ya idar ruwan roba kawai ya bude ya sa a cikinsa sannan ya shirya cikin wata farar Tshirt da wandansa na khaki, wannan bindigar da Abba ya bashi ita ya hada ya soka a aljihun wandan ,ya ziri wayarsa yasa a aljihun wandon ya fita.
       Karfe goma na dare a lokacin gidan yayi tsit sai hasken fitilu kala kala da suka haske ko Ina, he could feel how sad the buildings were too, he still cannot believe Afifah isn't home by this time, Kuma misalta irin yaqin da ake kirjinsa bata lokaci ne, a yanzu yayi niyyar durfafar abun gadan gadan amma bari ya soma ganin mahaifiyarshi , ya hangeta a falom Abba dazu kusa da yakumbo amma babu mai nutsuwar yin wani gaishe gaishe.
yayi hanyar part din Umma Gaji ya iske ikram da Munirah kwance akan carpet kamar masu bacci amma ba bacci suke b, ikram ta na jin shigowarshi ta mike ta nufi yaya Aliyu da rinannun idanuwanta alamun taci kuka ta koshi , zatayi  magana kuka ya maye gurbin maganar kamar yanda takeyi tun dazu, shima nauyin ne a zuciyarshi dan haka ya kasa furta komai a gareta sai rike hannunta da yayi acikin nasa, kwankwasa kofar dakin Umman yayi kuma ya bude a hankali, idanunsa da Hanan suka fara tozali kuma baiyi mamakin ganinta ba sabida incident din daya faru a gidan ya isa yasa tazo gida kwana, a gurguje ya gaisa da Ummansa yana niyyar fita coz he feel guilty of duk wani second dayake batawa anan gida ba tare
Da tafiya neman ta ba, Umma Gaji ta dubi dan nata da dukuma yankan dayake a goshinsa, tausayinsa ya mamaye kirjinta,  tashin hankalin dake idanunshi na Batan Afifah ya danso ya bata mamaki amma ta ture abun a ranta,

" ga Abinci Haidar,  duk ka rame "

Umma Gaji ta fada tana kokarin saukowa daga kan gadon duk da itama ba lafiyar ce ajikinta ba, karfin hali kawai takeyi da rashin yin korafi amma tanajin cewa gab take da kwanciya....she's tired of breathing!

Kallo daya yayi wa abincin ya girgiza kanshi alamun bazai ci ba, tun jiya da daddare a barracks rabonshi da abinci kuma In banda ruwa yanzu babu komai a cikinsa, bazai iya cin komai ba, baya ma jin yunwar. hannunsa rike da handle din kofar umman yace

" na koshi umma, inada abubuwan yi masu yawa yanzu"

" indai maganar Afifah ne yan sanda suna iya kar bakin kokarinsu.....kada kashiga Haidar"

Umma Gaji ta fada tsakaninta da Allah, tunda hukuma ta shiga toh Aliyunta ya fita a maganar, waya san wadansu mutane ne suka saceta, ita fa duk abunda zaisa yayanta a hatsari bata kaunarshi.
Aliyu daya jiyo yana dubanta na wadansu sakanni, maganar ma babu ruwansa aciki bata tasowa, har baisan lokacin da ya furta

" Allah ya wadaran Aiki na matukar bazansa hannu wajen neman Afifah ba Umma! Akwai ma maganar da nakeso muyi amma sai ta dawo gida sannan"

Da fadin haka ya fita abunshi, Umma Gaji da Hanan da tun dazu bata ce komai ba suka bishi da ido cikin son Fahimtar maganganunshi,

" Hanan, mai yayanku yake nufi?"

Umma Gaji ta tambaya dan so take taga ko wani ya lura da soyayyar Afifah da take ganowa muraran ajikinsa da maganganunsa. Hanan ta jinjina kai tace,

" umma ina ganin yaya fa kamar son ta yakeyi, itama kuma kwana biyu na lura kamar soyayya ta fara amma baa san ko waye ba"

" waye fa in banda Yarima Massa? Gashi yazo gida ma yau"

Ikram ta furta tana son musanta zargin ta, God! Could it be yaya Aliyu all these while? Duk lovey dovey da Afy take ciki dama son yaya Aliyu take? No way!!

AFIFAHWhere stories live. Discover now